2

1K 113 4
                                    








  Da sallama ta shiga parlour'n, babu wanda yai mata kallon arziki bale ta saka ran zasu amsa.

"Gani Mami"

"Gaki? Kizo kiman ƙerere haka kice gaki dan ga sa'ar ki ko?"

Tai sakato a tsaye tana kallon ta da mamaki. 'Ku dai bakuda alƙibla' ta faɗi cikin ranta.

Harara mami ta banka mata kafin tace.

"Aikin naki ma sai an kira ki za ki yi shi? Tun yaushe aka faɗaman kin dawo makarantar, koma ince galbaro. Idan zaman gidan ne ya isheki ƙofa a buɗe take ai, kinfi kowa sanin babu mai tsaidake tunda kin saba yin gaban kanki."

Har yanzu dai ci kanki Nudhar bata ce mata ba. Hakan ya ƙara kular da mami.

"Zaki ɓaceman da gani ki kama aikin ki ko sai na ci ƙaniyan ki"

Kafin ta rufe baki Nudhar ta yi hanyar kitchen.

"Mtsww! Aikin banza kawai"

Muryar Husnah tai mata rakiya.

Kace kace ta taradda kitchen ɗin, plates a barbaje duk an ɓata. Da gani kasan da gayya aka ɓata duk abinda ke wurin, hatta gas ɗin mai ne nashe nashe kwance a kai.

Ta rataye mayafinta a ƙofa ta cigaba da aikin gyara. Taɗau lokaci tana gyaran kasancewar ta mai sanyin jiki. Sannan ta leƙa parlour dan tambayar abinda zata girka na dare.

Ba kowa ɗakin sai Haseena kwance tana kallo, bata ko ɗaga ido ta dubeta ta ba duk da tanajin tambayar.
Tasan a rina ai, duk iskancin Husna ta fiye mata tunda ita zata tankata ko da dacin mutunci ne, amma haseena sai kai mata magana Goma bata maida maka ɗayaba tsabar miskilanci koma ace raini kai tsaye.

Ta na tsaye Mami tazo wucewa.

"Lafiya?" Ta ce mata.

"Daman ina tambayar me za'a girka ne"

"Daddyn su na gida yau. Ki mashi tuwon semo mu kuma sai kiyi mana shinkafa jalof, akwai Cow leg ki yi pepper soup"

Ta na faɗi tai wucewar ta.

'Shegen cin tsiya kamar da rana ba shinkafar sukaci da miya ba, mtsww!'  ta faɗi ƙasa-ƙasa ta koma kitchen ɗin.
••••       •••••

Sai da ya koma gida ya a je Aabid kafin ya shiga Sashen  Daddy. Zaune ya iske shi da manyan littafai  da System a gefen shi yana dubawa.

Kusa da shi ya zauna kafin ya ɗaura kanshi a cinyar Daddyn.

"Sannu da aiki Daddy"

"Yauwa ɗan Baffan shi, ya naka aikin?"

"Alhamdulillah, Daada tace kana nema na. Na tsaya kai Aabid park ne rigima yake"

"An faɗaman fitarku ai"

Ya ɗago kai yana kallon daddy.

"Waye ya faɗa maka?, wai gidan nan ba'a barin mutum yai rayuwar shi ne dole sai an saka mashi ido.."

"Haba kaikuwa" daddy ya dafa kafaɗar shi.

"Ba yadda kake tunani bane, duk wanda ke cikin nan a kwai bare?"

Ya girgiza kai.

"To ka dinga yiwa mutane tunani mai kyau, ka koyi kauda ido dan Allah Zaid, wannan zafin ni bansan inda ka gado shi ba"

Ya dai ɗaga kai ya tsuke fuska.  Daddy ya girgiza kai, ya rasa hali irin na Zaid.

"Daman ɗaurin aure nake son kaje mani gobe zai samu? Ina da meeting lokacin kuma yana da muhimmanci."

NOORUN NISAWhere stories live. Discover now