11

688 88 2
                                    

MAFARI


Bata taɓa tunanin rayuwa zata juyamata a lokaci ɗaya da ƙarancin shekaru haka ba, tasan iyayen ta basu raye,amma maraici bai kamace ta ba,in akai duba da tarin danginta. Sai dai dukda kasancewar su bai sa ta zamo wata abu mai muhummanci a cikin su ba. Asalima kowannen su bai fatan a ce ta raɓe shi. Son zuciya lulluɓe ya ke azukatan su da suka runtse ido sukai fatali da duk wata damuwarta tare da buƙatun ta.

Hawaye suka gangaromata, tasa hannuwa ta share, ta gyara kwanciya a yamutsattsiyar katifar da take kai, haƙarkarinta duk sun yi tsami. Murɗawar da cikin ta ya yi, ya nuna irin baƙar yunwar da take ji. Tasa hannuwa ta dafe cikin ta na jin yadda hanjinta ke yamutsawa suna curewa guri ɗaya. Takai idon ta inda kallabin ta ke yashe a ƙasa,tasa hannu ta jawo shi ta ɗaure cikin ta dashi duk a tunanin yai mata maganin yunwa.

A galabaice ta koma ta kwanta tana jin babu abin da ya ragu ga yunwar da take ji.

"Ina son binka Abbana, ina son rufe idanuwana..rufewa ta har abada!"

Ta faɗi da muryarta da bata fita sosai saboda gajiya da yunwa.

••••••• •••••••

Sa'eed Ahmad ɗan asalin ringim ne a jihar jigawa. Ƴan biyu ne shida ƴar uwar shi Salma a gurin mamansu. sai ƙanen su Salisu da suke ƴan uba. Shekara ɗaya suka bashi.
Dan haka ne suka tashi a tare, tun yarintarsu har girmansu basu taɓa ganin rigima ko wani abu mai kama da kishi a tsakanin matan biyu ba.

Mamarsu sa'eed itace uwar gida Saudatu suna kiranta da Baaba, maman salisu amarya habiba suna kiranta inna.

Sun taso cikin zuminci da son junansu har lokacin da Allah yai ma ml Ahmad da Baaba rasuwa sakamakon cutar amai da gudawa da akai fama da ita a garin na ɗan lokaci. A lokacin su duka suna jarabawar ƙarshe ta babbar makaranta dan haka inna ita ta cigaba da kulawa da ƴan biyun da ɗanta ɗaya tai masu ruƙo na gaskiya.

Lokacin da suka gama jarabawa su,sai suka cigaba da yan buge bugen su na nema da kasuwar da Babansu yabar masu kafin fitowar jarabawa su wuce makaranta ta gaba. Ita kuma salma tana gida tare da inna suna ƴan sana'oin su na cikin gida.
Basu taɓa fuskantar matsala ba ta fannin buƙatunsu, dan ba laifi shagonsu na kasuwa ba ƙarami bane.

Alhaji Badaru,maƙwabci ne ga Marigayi Ahmad a kasuwa. A yanzu kuma makwabci ga Sa'eed da Salisu. Mutum ne shi mai wayo da tsananin son kuɗin shi,ko kaɗan bai yadda ƙaddara ba ta fannin kasuwancin shi. Tun marigayi Ahmad na raye ya keson su ƙulla huɗɗa ta kasuwanci,amma sai Ahmad yaƙi bashi haɗin kai. Dan shi mutum ne da baison hayaniya ko kaɗan bare da ya kwana da sanin hali irin na Badaru.

A yanzu da babu Alhmad, Alh badaru yake ganin zai iya samun dama akan yaran shi, bawai so yake su amfana duka ba. A'a yana son yi ne dan amfanuwar kanshi kawai, kasuwar shi ta ɗaga sosai, ba kuma mutumen dake kulla a laƙa dashi saboda kowa ya sanshi sarai da ƙwarewa a butulci da son kai.
••
"Barka da safiya,Alhaji"

Ya faɗi yana ƙoƙarin buɗe shagon su. Alhaji dake kakkaɓe kaya ya juyo da murmushi kwanve a fuskar shi.

"Barka dai Sa'eed, an fito ne"

"Eh" kawai yace ya na sa kai cikin shagon nasu.

"Ina ɗan uwan naka ne? Nagan ka kai ɗaya"

Ya tsinkayo muryar shi.

"Yana tafe, uzuri ya tsaida shi"

"To, to ai shikenan"

Ya shige shagon, ba tare da ya ƙara tankawa ba.

Bayan sallar Azahar, ya sawo abincin shi yana ci. Dan har lokacin salisu bai zo kasuwa ba. Alhali yai sallama ya shigo.

"Abinci ake ci?" Ya tambaya,duk da ya gani.

NOORUN NISAWhere stories live. Discover now