20

640 73 3
                                    


Subscribe my youTube channel please.👇🏻

https://youtu.be/ABjHKTccoss




Wani irin kuka ta ke mai taɓa zucciya, hawayen ne kawai ke zuba ta zubawa wuri ɗaya ido tunaninta duka ya gushe. Ko ɗan da ta haifa ba a bata damar gani ba, mace ce? Nami ji ne oho, su dai kawai sun barta da raɗaɗin ciwo. Bayan haka da farfaɗowarta ko gyagijewa batai ba mummy ta sameta da baƙaƙen maganganun nan tamkar taga maƙiyiyarta.

Bata san ya akai ba sai jin ta yi an ruƙo hannuwanta duka biyun an ɗago ta, ba yadda ta iya da ya wuce ta miƙen kamar yadda a ka buƙata. Ta bayan kuwa aka fita da ita ana ƙurmusata mota, gabanta wata irin faɗuwa ya ke tamkar zai ruguzo ga ƙirjinta da yai wani irin nauyi ya na zugi. Kwata-kwata ba ta da wani ƙarfin jayayya a jikinta, dole ta shiga ta na zubarda hawaye.

Maƙoshinta ya cika da wani kalar ɗaci tunda motar ta fara tafiya, sunan Allah kawai ta ke ambata tare da fatan mutuwarta a kan wannan baƙar kaddarai mai cike da son kai da zalunci.

Sai da su ka samu inda ba yawaitar mutane sosai su ka ajeta a inda zai sada ta ringim, ko cikin garin bata samu alfarmai kaita ba. Tana ji tana gani suka koma motarsu suka batta ita da jikkar kayanta yashe bisa dakali sanyi na kaɗa ta.
•••• ••••

Ayyiririii!! Daada ta rangaɗa guɗa ta na kallon jaririn hannunta sak babanshi da alamar farin da zai fishi.

Addu'a tai mashi kafin ta ɗau waya ta kira Baffa dasu dady ta shaida madu ɗa ya iso. Kafin kace meye a sibitin ya ƙara cika da ahalinsu kowa baki buɗe a nawa Zaid da ya kasa ɓoye farincikinshi barka, musamman da Daada ta ce mashi haka yake sak da aka haifeshi shima.

Bakin mummy kamar gonar auduga har zuwa lokacin da Aunty sumayya ta dakushe farincikin da faɗin.

"Bayan kamannin babanshi har na uwarshi ya ɗebo, muhamman farin ma bayan idanun"

Wani dumm! Mummy ta ji cike da firgici ta ke kallon Aunty sumayya jikinta na ɗaukar ɗumi.

"Kai ni dai ko ɗugo banga kamarsu da aunty Sabeena ba"

Cewar Zuhra da ta ke ƙara leƙa babyn. Azima tai saurin caɓewa

"Eh wallahi, tunda ita ba fara bace"

"Surutun ya isa haka Akku"

Aunty nafeesa ta faɗi.

"Hajjaju hajjaju"

aunty sumayya ta kuma faɗi ta na ƴar dariya. A lokacin da baffa ya fito daga ɗakin da Sabeena ta ke ya na mai tausaya mata ganin yadda tai wujiga wujiga a dole tasha wuya.

"Zaid ka miƙa masu shi mu koma gida hakanan ka samu ka ci abinci.

Kuma duk mu tafi a barsu su huta, wa zai tsaya ne..Saratu dai muje gida kinsha wahala ai"

"Ni zan tsaya"

Aunty Nafeesa ta faɗi da yasa aunty sumayya harararta ta gefen ido, ita taso tsayawa dan ganin kwaf. Mummy kuwa bataso tafiya ba, sauƙin da taji ma aunty nafeesa ce zata tsaya a wuce da sumayya da ta boni ai. Kuma ta dai samu Nudhar ta tafi, ga Dr. Hindu nan ma dan haka bata da matsala, sai dai halayen aunty sumayya haryanzu hankalinta bai kwanta da su ba, dole ta san gaskiyar abinda ta ke tunani.

Baffa dai ya tarkata su suka wuce, sai da kowa ya shige mota a na zuro kai da leƙen zaid ya taho kafin ya haƙura da kallon ɗan ya miƙawa aunty nafeesa ya tafi.
••••

Da wani irin tashin hankalin da bata zata ba ta ke kallon Aunty sumayya, laɓɓanta na rawa ta furta.

"Mai ki ke nufi?"

NOORUN NISADove le storie prendono vita. Scoprilo ora