29

526 74 10
                                    


"Karka ce mani amana ta kaci akan aikin da na baka?"

Cewar mubarak da ke riƙe da waya a hannu ya saka hands free. Mummy na daga gefe tsaye ta na saurare. Daga cen cikin wayar ya ce

"Ta ya kuwa zan fara cin amanarka bayan kuɗin da ka biya ni? Kawai nayi abun yadda ya dace ne."

"Ban fahimta ba" mubarak ya faɗi.

"Kuskure ne in saka ma duka cake poising, yanzu da na saka duka yadda aka buƙaci inci mai kake tunanin zai faru? Kodai da yanzu ina barzahu ko kuma in kare rayuwata a prison. Kuma kasan ba zasu taɓa zama ba sai sun gano wanda ya shirya wannan aikin. Saboda haka ne na saka dai-dai inda na san zai yanka kawai, koda ya ci wasu ma sunci ba za a zargi komai ba dan wani abu ya sameshi."

"Dakyau, kayi aiki mai kyau. Zan turoma cikon kuɗin ka"

Ya datse kiran. Numfashi mummy ta sauke.

"Kasan banyi tunanin hakan ba? Shegiyar yarinyar nan ce duk ta ke son jagula mani lissafi. Yanzu ai sai ta ƙare rayuwarta da mahaukata har su bata rabonta. Hankali na ya kwanta a yanzu zan cigaba da plan ɗina a tsare"

"Sai munyi magana"

Mubarak ya ce ya na barin ɗakin. Part ɗin shi ya wuce cikin jin daɗin yadda plan ɗin shi ke tafiya dai-dai, yanzun ne Nudhar zata koma ƙarƙashin shi ya cigaba da jan ragamar wasan.
••• ••• •••

Juye-juye ya ke ta faman yi ya na sakin tsaki. Yarinyar tabi ta mashi kane-kane a rai, duk yadda ya so yakice duk wani abu da ya faru dan gane da ita ya kasa. Ya na sane sarai ba hauka ta ke ba, ya batta ne kawai a hukunta ta ga abinda ta yi wata ƙila ta bar duk abinda takeyin nan da ma wanda ta ke shirin yi a gaba.

A ƙasan ranshi kuma wani zafin wulaƙanta tan da akai ke taso mashi da ya rasa dalili. Gaba ɗaya kanshi ya ƙulle so yake yasan dalilin abunda take yin ya kasa. Idan ɓata mashi suna take son yi mai yasa zata ceci ɗanshi ta hanyar kasada da tata rayuwar? A ta wani ɓangaren ya na gano kyautatawarta a gareshi. Yanke shawarar kiran Sameer yayi wata ƙila ya fahimci miyasa hakan ke faruwa.

"Ina jinka" sameer ya faɗi bayan ɗaga kiran.

Zaid ya zayya na mashi abinda ya ke mashi yawo akai tare da hasashen shi na ko sunanshi ta ke son ɓatawa. Ya kara da faɗin

"Amma abin da ke bani mamakin, meyasa ta kyautata mani har ya kaiga kasada da ranta akan ɗa na?"

"Kai me yasa yanzu ka damu da halin da ta shiga?"

Ɗan shiru yayi ya na nazari. Ya ɗan ɗage kafaɗa

"Nima bansani ba, hadda shi na ke son ka faɗa mani"

Takaici ya kama sameer, shi a tunanin shi Zaid ɗin ya ɗan ɗago wani a bu a familun nasu ne dan gane da case ɗin Nudhar..maimakon haka sai shirmen da ya kira ya na faɗa mashi.

"Wata ƙila kana son ta ne"

Ya faɗi ya na kashe kiran. Fiddo idanuwa Zaid yayi ya na bin wayar da kallo, sai kuma ya jefar da ita saman gadon

"Nooo! Sameer baida hankali. Bai ta ɓa ganin ina son wata ba.."

Sai ya ɗan yi shiru kuma kamar mai nazari kafin ya tashi a hankali ya isa gaban madubi ya na kallon Kanshi.

"Ko dai ita ke sonka?"

Ya tambayi hoton shi na madubi.

"To ta yaya" ya watsa hannuwa ya na yamutse fuska.

"Zaid zata iya faruwa, ai ance mutane na sadaukar da kansu a kan soyayya kuma Nudhar ta maka haka"

Ɗaga kai yayi alamar tunani, ya nuna Zaid ɗin madubin

NOORUN NISAWhere stories live. Discover now