06

716 101 4
                                    


06

 

Danƙari! ta faɗa ta na raba idanuwan ta ga kaf illahirin wurin, gine gine ne gasu nan kashi-kashi duk iri ɗaya sai dai akan samu tazara tsakanin wani zuwa wani. Lokaci bayan lokaci mutane masu mabanbanta uniform da tag rataye a wuyan su, kan gitta ta su wuce ba tare da wani ya kalli inda take ba bare ta saka ran taimakon ɗayan su.

Tsaye ta yi ta na tunanin inda zata dosa kafin ta yanke shawarar cankar ɗaya tayi mashi tsinke,  ta na ɗaura hannu jikin ƙofar ta ji a rufe, bata ɓata lokacin ta ba wurin tsayawa ta juya ta nufi wata hanyar ta na fatan cin karo da wanda zata tambaya  ta huta.

"Ki na neman wani ne?"

Muryar ɗazu ta ƙara tambayar ta. Da sauri ta gyaɗa mashi kai.

"Wa ke nan?"

Tai shiru na ɗan lokaci tana tunanin yadda zata kira shi _Zaid_ kai tsaye a  kamfanin shi.

"Uhmm?" Ya furta ya na kallon ta.

"Mr. Zaid"

ta furta a hankali.

"Zaid?" Ya maimaita kamar ya na son tabbaci akan sunan.

Ta gyaɗa mashi kai.

Da hannu ya gwada mata wani ƙaton building da sam hankalinta bai karkata gare shi ba tun shigowar ta. Bai jira godiyar da ta ke mashi ba yai gaba.

Ta taka harta isa wurin ta murɗa ƙofar ta shige, ƙofar da ta ci karo ta na kallon ta ta nufa sai da ta danna ɗan maballi ta buɗe kafin ta ƙara cin karo da wata kofar ta glass da baka iya hango abin da ke ciki.

Sai wata mata da ɗan guntun sket brown da farar shirt ita ma da tag a wuyan ta zaune bisa kujera da tebur mai ɗauke da telephone da wasu zungura zunguran takaddu a  kai, hankalin ta gaba ɗaya ya na kan system ɗin da take daddanawa.

Ba ta bi takanta ba ta  matsa ta na tattaɓa kofar ko zata ga abin da zai taimaka mata ta buɗe.

"Excuse me" matar ta faɗa ta cikin son ƙarin bayani.

" Mr. Zaid na ciki?"

"Bazai haɗu da kowa ba a yau"

"Kira shi, yasan da zuwa na"

Ko kallon ta matar batai ba ta ci gaba da abinda ta keyi. Haushi ya kama ta ta ƙara danna mashi kira ya ƙi ɗagawa. Ta samu wuri ta tsaya ta na jiran taga ta inda zai ɓulo.

Tun ta na ƙilga mintuna har ta ga awa ɗaya ta cika ciff bashi ba alamar shi babu kuma alamar sheg*yar matar zata kula ta. A ranta ta ƙara fidda mintuna sha biyar da daga su bazata ƙara ko second ɗaya ba a nan.

Duk wani kiran da ke shigowa akan idon shi yake tsinkewa, bai shirya ɗaukan ba ne kawai so ya ke ya ƙure haƙurin ta ya kuma sha mamakin ganin batai zucciya ta tafi ba kusan awa ta biyu na shirin shiga.

A wani bangare na zuciyar shi kuma ya karkata ne ga son fahimtar wani abu da yake jin ya mashi banbanci a tattare da shi da ba zaice ga ta yadda ya fara ba sa'annan kuma ba zai ce ga ainahin abin da ya ke jin ba.  Abu ɗaya da yafi matuƙar ɗaure mashi kai a duk lokuttan da ya ganta sai ya ke jin kamar a kwai wani abu mai mahimmancin da ya ke son sani.

Ya ƙara kallon ta yadda cctv ke dallo mashi ita a tsayen ta ta na jijjiga ƙafa alamar gajiya.

'Mata ban haushi gare su' ya ayyana,kafin ya yanke iya adadin aikin kwana nawa zatai mashi ta tafi ta bashi wuri, a ran shi. Ya ɗauki wayar shi ya daddana.

"Zaki iya shiga"

Ta ji matar ta faɗa daga inda ta ke tsaye ta na shawatar tafiya.
Ta na ganin ƙofar ta buɗe ta dallawa matar harara ta shige.

NOORUN NISAWhere stories live. Discover now