Babi na sha Bakwai

885 90 6
                                    


Bayan fitan Haydar da minti sha biyar Laila ma ta fito da rakiyar Ammi wacce ke cigaba da mata godiya da fata nagari.
"Ammi ki bar godiyan nan haka, ai Haydar kamar k'ani yake a gurina."
Kayan abincin da Laila ta kawo musu tasa yaran unguwa suka shigar dashi gidan, Ammi dai baki yak'i rufawa ta kasa daina godiyan da aka hanata.
  Bayan tafiyan Laila Haydar ya dawo gidan fuskarsa a had'e babu walwala.
"Ali kuka kayi ne?" Tambayar da Ammi ta fara masa kenan da taga idanunsa yayi ja.
Zuciyarsa ba dad'i ya kalleta yace,
"Seriously Ammi! Ni me zai sakani kuka? Ni mace ce?"
"To meya sameka?" Ta k'ara watsa masa wata tambayar tana nuna masa kujerar tsugunno dake kusa da ita.
Zama yayi akai babu musu kana kafad'unsa suka sauk'a alamar gajiya ya d'ago kai ya dubeta yace,
"Ammi Hajiya Laila nake so, ita kuma nake son aure ta zama matata uwar 'yayana. Na fad'a mata abunda yake cikin zuciyata amma ta shashantar da zancen kuma  tak'i saurarata wanda k'arshe ma ta d'auki maganata irin ta marasa hankali. Ammi ya zan yi?"
"Baka da hankali Aliyu Haydar."

A ranar da daddare Laila ce kwance a d'akinta gefenta kuma Sabrin ce akan kujerar dressing mirrow tana mata lissafin cinikin da aka yi a Laila Beauty, ita kuma tana danne-danne a wayarta kan wasu kaya da za'a kawo mata daga Maiduguri.
Tana tsaka da haka ta ji k'arar shigowar sak'o a cikin wayarta. Fita tayi daga whatsapp ta koma gurin text messages taga sak'o ne daga Haydar kamar haka.

   'Hey Beautiful, I just want to say I miss you and I love you.'

Numfashinta ne ya d'auke na sakanni kafin ta tuno yanda ake yi taja mai tsayi ta sauk'e da k'arfi, Sabrin dake gefenta ta dubeta a d'an tsorice tace,
"Mama lafiya?"
"No, no babu komai. Carry on."
  A haka Sabrin ta gama mata lissafin har suka shiga wata hirar daban Laila na maimaita text d'in Haydar a zuciyarta. Haydar ya rainata kuma zata yi maganinsa, raininsa yayi yawa!
"Mama zan je na kwanta, wallahi duk na gaji."
Ta mik'e tsaye tana hamma tare da mik'a.
"Kina k'ok'ari Sabrin Allah ya miki albarka. Ai nan gaba ke zan barwa shagon ni kuma in huta a gida abuna."
Dariya Sabrin tayi tace,
"To karatun da zan yi fa? Kinga fa next year zan fara Jami'a."
"Nima da nayi karatun banyi amfani da kwalin degree d'in ba, sai dai bazan miki dole ba, duk wanda kika za6a a cikin aikin gwamnati ko a Laila Beauty I'll respect your decision. Kiyi bacci and banda hirar tsakar dare da Salman."

Minti talatin da haka itama tayi shirin kwanciya ta lek'a d'akin Abul. Kamar kullum yau ma ta sameshi rik'e da laptop yana danne-danne cikin kwarewa da kuma sabo. Dama tun tashinsa ya iya computer ya kuma samu karatu a Jami'a ta fannin hakan, wanda tsabar kwarewarsa yasa 'yan department d'insu suke kiransa Computer Geek.
  Bai d'ago ido ya kalleta ba saboda har wannan lokacin basu daidaita ba bayan arangama da yayi da Haydar a asibiti.
"Yanda kake rik'e na'urar baturen nan ko Al qur'ani baka karantawa irin haka Abul."
  Shiru yayi kamar bai jita ba wanda hakan ya k'ona zuciyar Laila ta rufe Laptop d'in ta kalleshi cikin 6acin rai.
"Ina matsayin mahaifiyarka amma ina maka magana kana mini shiru? Kasan wa kake yiwa haka ko ka manta matsayina ne a gurinka? Kar kaga ina lalla6inka ka wuce goma da iri, bazan d'auki raini daga d'an dana haifa da cikina na kuma raineshi ba. Idan ka manta wacece ni a gurinka tun wuri ka tuna don bazan lamunci wannan iskancin daga gareka ba. Kana jina?" Ta daka mishi tsawa tana nunashi da yatsa.
Gyad'a kai yayi amma a zuciye har jikinshi na kyarma.
"Banji kayi magana ba."
"To."
"Sai kuma me?"
"I'm sorry."
"Good." Ta fice daga d'akinsa zuwa nata d'akin tana jin ranta babu dad'i.
Dawowa tayi d'akinsa ta samu yana hawaye yana cije le6e wanda tasan babu mamaki ya fasa bakinsa.
  Abunda take tsoro game da Abul kenan, shi idan ranshi ya 6aci bashi da kyau ko kad'an, kuma zai iya aikata komai sai dai daga baya yazo yayi dana sani. Tana kaffa-kaffa dashi amma tasani lokaci yayi da zata daina hakan domin ko babu tsufa akwai mutuwa.
  Abul yayi girman da nan gaba kad'an zai bar gabanta ya zama shine mai kula da rayuwarsa, ta yaya zai yi tarayya da dubbannin mutane da wannan saurin fushi nasa da bak'ar zuciya?
Ta sani a yanzu rayawa yake yi zuciyarsa cewa da Babansa yana raye da bazata mishi haka ba. Kullum maganarsa kenan wanda shi a tunaninsa idan Babansa yana nan duk wata jarabawa ta rayuwa bazai faru a akanshi ba.
  Ya zata yi ta nuna masa cewa a hakan, a yanda yake yafi wasu dubu kwanciyar hankali akan wanda suka rayu tare da uwarsu da ubansu?
  Zama tayi akan gadon kusa dashi ta fara magana a hankali.
"Abul fad'an dana yi maka yasa kake kuka da girmanka?"
Girgiza kai yayi wanda yasa Laila ta masa wani kallo kana ya bud'i baki yace,
"A'a."
"To meya sameka?"
"Babu"
"Haka kawai baza kayi kuka ba Abul. Ka fad'a mini damuwarka, duk duniya kana da wanda ya fini ne? Ko kuma akwai wanda zai soka fiye dani?"
"Mama na yarda kiyi aure amma banda yaron nan."
A bazata taji maganar wanda sai da hanjin cikinta ya kad'a, ido kawai ta zuba mishi shima yana kallonta amma nashi kallon na rok'o yake mata.
"Don Allah Mama." Ya k'ara fad'i yana kamo hannunta."
Murmushi tayi wacce iyakarta fatar baki tace,
"Me ka gani da har kayi tunanin zan iya auren Haydar?"
"Nasan irin mutanen da suke shiga ranki Mama, kuma shi yana d'aya daga cikinsu wanda kuma ya samu damar shiga rayuwarki har kika kasa rabuwa dashi. Wallahi Mama da akan wani aka miki wannan zargin da kin shafe babinsa a rayuwarki, amma shi kin kasa, k'arshenta ma yau har gidansu kika je."
"Are you spying on me Abul Khair?" Ta mik'e tsaye tana kallonshi cikin mamaki.
"Wannan bashi ne tambayar da zaki yi ba Mama, tambayar da zaki yi shine; ya akayi kika kasa rabuwa da yaron alhalin kin iya yanda zaki kori mutane wanda a daa kinyi kuma har yanzu kina kan yi? A daa bana son kiyi aure domin burina bai wuce ace kinje Aljanna kun had'u da Babana ba, amma a yanzu na yarda kiyi auren saboda zamanki haka bazai hana mutane yi miki k'azafi ba wanda har raina nake jin bak'in cikin hakan. Kuma yin auren shine rufin asirinki da namu Mama. Wallahi yanzu kam na amince."
"Dama ba yardarka nake nema ba, kuma daa ina son yin auren daa tun kafin ka mallaki hankalin kanka nayi Abul."
  Yaci gaba da maganarsa kamar bai ji me tace ba, yace.
"Ga Baffa Nazifi har yau idan naje gidan Umma sai yace mini 'Mamanka ta gujeni'. Sannan ga Alhaji Abdul wanda tun saurayi da budurwa aka ce yana sonki kuma wai a kanki yak'i yin aure har yanzu, he's almost 50 Mama amma har yau bai cire rai da aurenki ba. Da kuma sauran manyan mutanen da suke fatan ki auresu Mama, wanda ke kanki kinsan suna da yawa. Sannan ga Uncle Mas'ud wanda shima saboda kink'i yin auren yasa shima yace bazai yi ba. A kan rashin aurenki Uncle Madu yake miki duk wannan k'azafin wanda har yayi nasarar rabaki da mahaifiyarki, sannan karki manta Mama, a kan rashin aurenki Ummii ta had'u da hawan jini wanda kullum ta tuna ta barki kina yawo a gari babu miji sai ta kwanta rashin lafiya. Duk fa akan kink'i yin aure abubuwan nan suke faruwa Mama."
  Jawota yayi ta zauna a gefensa  ya kamo hannunta gam cikin nasa yaci gaba da magana,
"Bakya ganin kamar kin yi son kai? A kan wani ra'ayinki guda d'aya yayi affecting rayuwar mutane da yawa negetively Mama. Kuma duk sunyi k'ok'ari a kanki sun miki halacci tun baki da komai. Bakya tunanin cewa kema ya kamata ki d'auki wani mataki a rayuwarki da zai kawo zaman lafiya da kwanciyar hankalinsu matuk'ar hakan bai kaucewa shari'a ba? Think about it Mama. Komai da yake faruwa akan aurenki ne, da zarar kinyi kowa zai huta za'a samu peace of mind, dani, Sabrin, Uncle Mas'ud da Madu, Alhaji Abdul, Baffa Nazifi, Ummii, Umma da duk mutane masu sukanki akan abunda bakya aikatawa, sannan ke karan kanki zaki huta Mama. Kiyi aure komai ya zama tarihi don Allah. Please."
"Sakar mini hannu." Shine abunda tace dashi wanda ya aikata hakan babu musu.
  Mik'ewa tayi tsam ta fice daga d'akin amma kafin ta isa nata ta jiyo muryar Abul a bayanta.
"Alhaji Abdul is the right person for you Mama, bashi da mata ko 'yaya sannan yana sonki since day one har kawo yau bai fasa kawo miki tayin soyayyarsa ba. Ki gyara mana zuriya, do the right thing." Ya kulle k'ofarsa.
  Ta jima tsaye a gurin tana tunanin maganganun Abul, wanda bata ankara ba sai ji tayi kamar mutum a bayanta ta juyo a tsorice.
  Mas'ud ta gani tsaye rik'e da kofin shayi yayin da hannunsa d'aya ke cikin aljihun wandonsa.
"Stop doing that Mas'ud."
"Me kenan?" Ya tambayeta kamar bai san me take magana akai ba.
"Ka sani." Ta bashi amsa tana mai d'aura hannayenta saman k'irjinta cikin dakewa.
Murmushi yayi kad'an kana ya ajiye kofinsa a kan saman kujera ya ware hannayensa yace,
"Come here."
Ta kai sakan goma tana kallonshi idanunta na tara hawaye sannan tayi gudu ta isa jikinsa ya maida hannunsa ya rungumeta. A take ta fara kuka yana bubbuga bayanta alamar rarrashi sai dai bai ce da ita komai ba.
  Sai da tayi mai isarta sannan ta matsa daga jikinshi tana goge hawaye tana murmushi.
"Nasan Mas'ud d'ina yana nan bai daina sona ba."
"Kina jawo magana ne kwanan nan Kalti, but ki sani duk wuya duk rintsi zan bi bayan duk wani decision da zaki d'auka."
"Kaji abunda Abul ya fad'a mini?"
"Naji and he is right. It's time kiyi aure."
"Da gaske nina hanaka aure?"
"Ta wani gurin yes, amma bayan hakan akwai wani dalilina mai k'arfi."
"Me kenan?"
"Kije ki kwanta kiyi bacci." Da haka yaja hannunta zuwa d'akinta, sai da yaga ta kwanta ta lullu6u sannan ya kashe mata wutan d'akin yace,
"Good night." Ya rufe mata k'ofar.
"
Ta yaya zan fara tunanin aure ni da nayi alk'awarin har in mutu bazan yi ba? Tukunna ma da waye zan iya rayuwar aure ba uban 'yayana ba?
Tambayoyin da Laila take yiwa kanta kenan hawaye na sauk'a a gefen fuskarta.
  K'arar da wayarta ta fara yi yasa ta share hawayenta tana jin haushin yanda da girmanta take kuka kamar k'aramar yarinya.
  Screen d'in wayar ta duba taja tsaki ganin Haydar ne ke kiranta. Haushinsa taji ya turnuk'eta domin akanshi duk wannan magana ta taso har Abul ya iya cewa tayi aure wanda a daa in aka ce mata Abul zai yarda tayi aure zata k'aryata.
   Wai ma me suke tsoro ne game da Haydar da suke son ta rabu dashi? Menene aibunshi?
  K'arshe da ya dameta da kira tasa wayar a flight mode kana ta duba yawan kiran da ya mata. 36 missed calls and 4 text messages wanda ta karanta kamar haka.

RUWAN ZUMA (completed)Where stories live. Discover now