Washegari asabar da safe Laila ce tare da Mas'ud a kan dinning table zasu yi breakfast bayan ya matsa mata ta fito.
"Mas'ud wani labari nake ji wai za'a je tambaya maka mata?"
"Kalti Ajidde ce ta fad'a miki ko? Yanzu dai kiyi breakfast sai in baki labarin komai." Ya tura mata abincin da ya zuba mata a plate yana ajiye mata fork a ciki.
Kallonshi tayi a marairaice fuskarta a kumbure dalilin rashin baccin da bata samu ba jiya.
"Ka k'ara kiran Abul ne?" Ta fad'i hakan tana d'aukan fork ta caki chips dashi.
Sai dai ta kasa kaiwa baki da Mas'ud yak'i amsa mata. Ko da ya lura da hakan sai yayi d'an murmushi kad'an yana cewa,
"Na san yana can gidan wani abokinsa, da zarar ya dawo hankalinshi zai nemi hanyar gida."
Kwalla ne ya ciko idanunta tana tunanin ina Abul ya shiga bai kwana a gida ba. Ana kiran wayarshi yak'i d'auka, daga baya ma kashe wayar yayi ya zama ba'a ma samunshi. Duk wasu abokansa da suke tunanin zai je gurinsu sun kirasu sunce basa tare. To ina ya shiga?
K'arshenta kasa cin abincin tayi in banda loma uku wanda ta had'iye da kyar. Komawa cikin falon tayi ta d'auki wayarta tana cigaba da kiran Abul sai dai har lokacin wayar a kashe take.
Mas'ud ya k'ar6e wayar daga hannunta ya ajiye a gefe yana cewa,
"Ki daina saka damuwa a ranki Kalti, duk inda Abul ya shiga shi ba yaro bane zai kula da kanshi."
"Mas'ud na yiwa Aliyu adalci kuwa dana bari d'ansa ya ta6ar6are?"
"Kina nufin shiriya da rashinta a hannunki take kenan?" Ya tambayeta yana jiran amsarta.
Karkad'a kai tayi ya k'ara da cewa,
"Kenan kinga baki da ikon shirya bawa ko ki 6ata shi, sannan kinyi iya k'ok'arinki wajen basu tarbiyya nagari, abunda zaki yi a yanzu shine addu'an Allah ya shirya miki shi, kuma zai shiryu da yardarsa."
"Hakane, amma anya kuwa yaron nan ba shaye-shaye ya fara ba? Ka duba yanda yake mini magana ni uwarsa kamar wata 'yar iska a titi. Wannan abu ya bani tsoro Mas'ud, wallahi ban ta6a tsammanin d'ana na cikina zai iya mini haka ba. A daa idan naga yaro ya lalace sai ince sakacin iyayensa ne, to ni ina na gaza a tarbiyyar yaran nan? Har Sabrin tayi aure ban ta6a ganin wani abu makamancin raini ko gur6acewar hali a tattare da ita ba, kuma duk tare na rainesu na basu tarbiyya iri d'aya. Meyasa Abul ya zama haka?"
"Saboda haka Allah ya k'addara, kuma baza ki fidda rai da shiriyarsa ba saboda ke uwace addu'arki baza ta fad'i k'asa banza ba."
"Hakane, Allah ya shirya mini shi."
"Ameen Kalti." Ya amsa addu'an yana danna wayarsa kana ya mik'a mata yana cewa,
"Ga matar da zan aura."
"Masha Allah kyakkyawa da ita. Amma meyasa ban san da zamanta ba sai kawai naji zaka yi aure cikin kwana biyu?"
"Saboda nasan zaki tursasani in aureta alhali ke baki yi ba, sannan zamanki ke kad'ai a gidan nan matsala ce babba da mutane zasu yi amfani da hakan wajen aibataki a idon duniya."
Laila kasa magana tayi ta bud'e baki tana kallon Mas'ud cikin mamaki. Kenan wannan shine dalilinshi na k'in yin aure? Wani irin so yake mata da har zai iya wannan sacrifice d'in?
"You are very stupid Mas'ud."
"I know."
Yana fad'in hakan ya tashi ya fita daga gidan zuwa gidan abokin babansu wanda zasu je nema masa aure. Ko awa d'aya cikekke bai yi a gidan ba ya shiga motarsa zuwa gidan Alhaji Abdul domin ya sanar dashi sak'on Gimbiyarsa Laila.
Duk da cewa bai ta6a zuwa gidan ba amma maigadin yana jin sunansa ya bud'e mishi k'aton gate d'in ya shiga yana cewa,
"Alhaji yace duk d'an uwan Hajiya Laila a bud'e masa ya shigo."
Mas'ud da mamaki ya kamashi yace a ransa ba k'aramin so Alhaji Abdul yake yiwa Laila ba da har ya bawa maigadinsa izinin barin danginta shigowa gidan babu wani dogon bincike.
Gida ne tangameme wanda ya ninka gidansu sau uku, shi kanshi da yake ba bak'on wannan rayuwar ba yasan cewa gidan Alhaji Abdul ba k'aramin kud'i yaci ba.
Tun kafin ya isa mashigar gidan wani mutum ya bud'e masa k'ofar falon ya kutsa kai ciki yana amsa gaisuwar mutumin.
"Ka biyoni zuwa falon Oga." Mutumin yayi gaba ba tare daya jira me Mas'ud zai ce ba.
Gyad'a kai yayi yabi bayanshi yana kallon tsarin gidan wanda ya burgeshi har yana ayyana ga Kaltinshi a ciki.
A falo na biyu mutumin ya tsaya ya nunawa Mas'ud kan kujera yace ya zauna. Shi kuwa ba musu ya zauna yana zaro wayarsa daga cikin aljihunsa don ta d'ebe masa kewa saboda yasan zai yi wuya Alhaji Abdul ya fito da wuri.
Sai dai kafin ma ya danna inda zai shigan ya jiyo takun sawaye ana sauk'owa daga matakala.
D'ago idon da zai yi ya hango Alhaji Abdul tare da Abul wanda yayi kofin-kicin da fuska tamkar bai so fitowa ba.
Tsananin mamakin ganin Abul a gidan Alhaji Abdul yasa Mas'ud tashi tsaye yana cewa,
"Abul dama nan kazo?"
"Eh." Kawai ya bashi amsa kana shima ya samu guri ya zauna amma yak'i su had'a ido, Mas'ud kuwa hankalinshi na kan ciwon da ya gani a fuskar Abul.
Alhaji Abdul ne ya dubeshi tamkar uban da yake son yiwa d'ansa gyara yace,
"Baka ga kawunka bane?"
Abul ya d'ago kai ya dubi Alhaji Abdul sannan ya maida dubanshi ga Mas'ud yace,
"Ina kwana?"
Mas'ud bai amsa ba illa ma tattara hankalinsa da yayi ya mayar kan Alhaji Abdul yana masa kallon tuhuma.
"Alhaji Abdul me yaron nan yake yi a nan? Kuma meyasa baka sanar da mahaifiyarshi cewa yana gurinka ba alhali kasan hankalinta a tashe yake?"
Alhaji Abdul ya gyara zamanshi yana cewa,
"Kar kaga laifina don ban sanar daku cewa yana gurina ba, domin kuwa da zarar na fad'a muku tun a jiyan zaku zo ku d'aukeshi wanda hakan ba komai zai gyara ba sai ma ya k'ara haiho wani abun daban. Kai Abul a ina na sameka?"
Abul yayi kicin-kicin da fuska yace,
"A club."
Duk'ar da kai Mas'ud yayi k'asa na wasu sakanni yana jin rad'ad'i a zuciyarsa lokaci d'aya kuma ya fara nanata lahaula wala kuwwwata a ransa. Me Abul yake son zama?
D'ago fuskarsa yayi ya dubi Abul yace,
"Abul me kake yi a Club da hankalinka da iliminka?"
Bai amsa ba hakan yasa Alhaji Abdul ya girgiza kanshi cikin rashin jin dad'in abunda zai fad'a yace,
"Ina cikin meeting a office wajen k'arfe tara Secretary na ta fad'a mini cewa ana nemana cikin gaggawa. K'arshe na k'ar6i wayar da aka kirani dashi aka fad'a mini cewa d'ana yaje club yasha wiwi wanda har ta kai suka yi caca, k'arshe da yayi losing sai ya nemesu da fad'a suka masa duka, ko da naje na samu sun kumbura mishi ido na kaishi asibiti aka wanke mishi inda yaji ciwo. Gudun halin da Laila zata shiga yasa na kawoshi gidana na kuma yi mishi fad'a sosai kan mugun halin da yake son saka kanshi. Yanzu daka ganmu haka gidanku zamu je ya bawa mahaifiyarshi hak'uri kan abunda yayi mata domin ya bani labarin halin da ake ciki. Idan zata auri Haydar laifi ne ko kuma haramun ne? This is unacceptable Abul, mahaifiyarka tafi gaban komai a gurinka, kaine ya kamata kayi supporting d'inta akan lamuranta ba wai ka koma gefe kana sulking kana shaye-shaye ba." Ya k'arisa maganan cikin fad'a sosai tamkar zai ari baki.
Jikin Mas'ud yayi sanyi domin a farko bai yarda da Alhaji Abdul ba, amma bayan furucin da yayi sai yaga a yanda yake son Laila ba zai ta6a barin gudan jininta ya gur6ace ba.
"Mun gode Alhaji Abdul Allah ya bar zumunci yasa kuma hakan ya zama sanadin shiriyar Abul. Dalilin zuwana gidanka dama Laila ce ta aikoni da sak'o mai girma." Ya dakata yana kallon Alhaji Abdul wanda ya matso bakin kujeran tunda yaji an kira sunan Laila.
Mas'ud ya dubi Abul yaga shima ya zuba ido da kunne yana sauraronsa, suna had'a ido Abul ya kawar da kanshi gefe.
"Tace in sanar da kai idan ka shirya a d'aura aurenku ranar Jumma'a mai zuwa."
Wani irin mik'ewa Abul yayi cikin sauri yana kallon kawun nashi kamar bai gaskata abunda yaji daga bakinsa yace,
"Uncle Mas'ud da gaske Mama zata auri Alhaji Abdul?"
Hararansa Mas'ud yayi irin (har yanzu ban manta abunda kayi ba) kana ya maida dubansa kan Alhaji Abdul wanda ke muntsinin hannunsa.
Abun ya bawa Mas'ud dariya amma ya murmusa kawai yace,
"Baka yarda ba ko?"
Alhaji Abdul da bakinshi ya kasa rufuwa tsabar farinciki yace,
"Wallahi ban tsammaci wannan ranar zata zo ba, na d'auka har in mutu bazan yi aure ba saboda Laila ta k'ini. Alhamdulillah ya Allah. Alhamdulillah."
"I did not expect that." Fad'in Abul yana komawa gurin zamanshi fuska ba yabo ba fallasa.
Sai da Alhaji Abdul ya dawo cikin hayyacinsa sannan Mas'ud ya mik'e tsaye kana ya dubi Abul yace,
"Ka tashi mu koma gida."
"Mas'ud saurin me kake yi? Ka d'an dakata in canja kaya sai mu tafi gaba d'aya. Wannan bushara da kazo mini da ita zata hanani zama ba tare da na kalli matar tawa ba."
Wannan magana da Alhaji Abdul yayi bai yiwa Abul dad'i ba, burinsa na daa ne ya dawo wato; kar mamanshi ta auri kowa ta cigaba da zamanta haka. Yanzu idan tayi aure wani zai maye gurbin mahaifinshi shikenan sai a manta dashi a shafe babinsa?
A can cikin ranshi kuma yaji kamar mamanshi ta za6i Alhaji Abdul ne saboda shi. Ya kyauta mata kuwa duk da cewa itama bata san halin da yake ciki ba?
K'arshe Alhaji Abdul ya koma sama ya canja kaya wai duk don ya burge Laila. Mas'ud kuma a ranshi yace daa kayanshi na farko ya bari.
"Mas'ud kaci tukuici mai tsoka, don Allah ka fad'a mini menene zan maka matuk'ar bai fi k'arfina ba wallahi zan mallaka maka." Fad'in Alhaji Abdul suna fitowa daga falonsa zuwa gurin ajiye motoci.
Murmushi Mas'ud yayi yace,
"Ka kula mini da Kaltina shine abunda nafi so a duniya, bayanshi bana buk'atar komai naka."
"Wannan maganar bamu k'arisashi ba saboda ko baka so sai an baka wani abun. Sannan ko baka fad'a ba ni zan kula da Laila tamkar ruhina, kaima shaida ne akan yanda nake sonta. Wallahil Azeem Laila zata zama tamkar sarauniya ce a gidana."
"Allah yasa." Mas'ud ya shige motarshi Abul ma ya shiga suka bar Alhaji Abdul a waje yana cigaba da murna.
"Ka shiga motan kawunka kenan? Shikenan bari in shiga nawa mu tafi."Minti sha biyar da haka suka iso gidan Laila. Tana zaune a falo suka yi sallama suka shigo ta amsa tana kallonsu, ganin Abul fuska a kumbure ba k'aramin firgici ya sakata ba. Cikin sauri ta tashi ta iso gurinshi tana tambayarshi wa yayi masa haka tana ta6a gurin.
"Wash Mama da zafi." Ya fad'a yana kawar da kanshi daga hannunta.
"Wa ya maka wannan d'anyen aikin Abul?"
Mas'ud ya tari numfashinta yana cewa,
"Ga Alhaji Abdul a waje yazo gurinki."
Zata yi magana sai kuma ta fasa ta jawo hannun Abul ta zaunar dashi akan kujera tana kallon Mas'ud.
"Babu inda zai je." Ya bata amsa kana ya fita waje ya kira Alhaji Abdul suka shigo tare.
Suna zama itama ta fito sanye da hijabi ta samu guri ta zauna tana yiwa Alhaji Abdul sannu da zuwa.
Shi kuwa gogan ganinta kad'ai da yayi sai ya susuce yana washe hakwara cikin tsananin farin ciki.
A maimakon hakan ya burgeta sai taji haushinsa ya turnuk'eta wanda ta kasa gane dalili.
Abul da yake gefe ya lura da kallon da Alhaji Abdul yake yiwa mahaifiyarshi sai kawai ya kawar da kansa gefe yana jin bak'in ciki a ransa. A daa yayi zaton in dai ta auri wani ba Haydar ba ba zai ji haushi da wannan takaicin ba, ashe k'iyayyar da ya yiwa Haydar ne yasa yaji wannan abun. Yanzu a kanshi zata auri wanda ya za6a mata amma sai gashi yana cikin bak'in ciki mara misaltuwa.
"Gimbiya Laila sai naji sak'o mai d'umbin alkhairi daga Mas'ud, naga cewa wannan magana ba zai barni na zauna ba har sai nazo da kaina."
Laila dake fatan ya tafi don ta zauna da yaronta tace,
"Haka ne."
Alhajia Abdul ya dubi Mas'ud wanda ke danna wayarsa kana ya tashi ya fita daga falon yana kara wayar a kunne. Yana fita Abul ma ya shige d'akinsa ba tare da ya kallesu ba. Hakan ya basu damar kasancewa su kad'ai a falon.
Laila dai fuska ba yabo ba fallasa tayi magana da Alhaji Abdul na minti goma kana ya mata sallama ya tafi da ya lura hankalinta na kan yaronta ne. Sai dai yace mata zai dawo da dare domin su fara shirye-shiryen biki tunda tace cikin kwana 6 take so a d'aura.
Yana fita kamar wata walkiya ta tashi ta shiga d'akin Abul ta sameshi a kan gadonshi yayi zugum kamar mara lafiya.
"Waye ya maka haka Abul? Sannan ina kaje ka kwana?" Tambayar da ta fara mishi kenan tana zama kusa dashi.
Ajiyar zuciya ya sauk'e kana ya fara magana kamar mai karantawa a littafi,
"Bayan na fita daga gidan nan kafin in haura titi wasu samari biyu suka tareni wai in basu wayata, su suka mini duka suna lalu6ar jikina zasu d'auke, muna wannan kokawar ne sai ga Alhaji Abdul ya shigo layin da motarsa, da suka ga hasken sai suka gudu suka barni. Shine yace in shigo ya mayar dani gida ni kuma nace masa bazan koma ba. Daga baya na fad'a masa me yake faruwa yace in shiga muje gidansa in kwana a can. To muna shirin zuwan ne sai Uncle Mas'ud yazo." Ya fad'i abunda Mas'ud yace ya fad'a gudun kar hankalinta ya tashi idan taji cewa yaje club yasha wiwi kuma har yayi caca.
Ita kuma wannan labarin nashi bai zauna mata ba, don haka ta dubeshi tace,
"Anya hakan ne ya faru? Alhaji Abdul baya zuwa gidana sai gaisuwar sallah k'arama ko babba kad'ai yake kawoshi, nan ma bada dare ba. Abul ka fad'a mini gaskiya domin ina ji a jikina k'arya kake mini."
"Wallahi haka ne ya faru Mama ki yarda dani. Kuma kiyi hak'uri ki yafe mini abunda na miki jiya don Allah"
"Ya wuce, Allah ya shiryeka Abul domin shine kad'ai burina a duniya."
"Mama bakya sonshi ko?" Yayi mata tambayar da bata yi zato ba.
Mik'ewa tayi tsaye ta isa bakin k'ofa kana ta juyo da kanta kad'an tace,
"Zan iya yin komai saboda 'yayana saboda ku nake gani nake farinciki, kuma bazan ta6a barin jinin Aliyu ya gur6ace saboda wani jindad'i nawa ba. Ka kwanta ka huta."
Da haka ta fice daga d'akin ta bar Abul na tsiyayar hawaye.Mum Fateey 👌
YOU ARE READING
RUWAN ZUMA (completed)
RomanceShin wani irin kallo kake yiwa masoya biyu wad'anda akwai tazarar shekaru tsakaninsu, musamman ma in aka ce Macen ta fi Namijin yawan shekaru? Tayi wuff dashi, ko Tsoho yayi wuff da yarinya. To ga labarin wani matashin saurayi mai farin jinin 'yan...