"A'a barshi kawai." Laila ta samu kanta da fad'i bayan saurayin ya mata tayin d'aukan kayan hannunta.
"Ba komai Hajiya, aikinmu ne." Ya bata amsa yana k'ara mik'a hannunsa don kar6a.
Sai a lokacin Laila ta lura da kayan da ke jikinsa wato red and black, wanda duk ma'aikatan kantin shi suke sakawa.
Bata k'ara musu ba ta mik'a mishi ya kar6a.
"Ka saka a bayan motar kawai." Ta bashi umarni tana mai bud'e motar.
A baya ya saka mata ledojin kamar yanda tace kana ya rufe marfin yana cewa,
"Muna godiya Hajiya, we look forward to seeing you again. Have a great day." Kana ya bud'e mata mazaunin direba ya matsa baya.
Hakan ba k'aramin burge Laila yayi ba, ba don komai ba sai don mutanen gurin sun san makamar aikinsu. A nan tayi tunanin saka wannan tsarin a katafaren shagonsu na magani wanda Mas'ud ke kula dashi.
Sai da ta shiga kana ta zaro kud'i a cikin jakarta ta mik'a mishi amma ya girgiza kai,
"A'a Hajiya nagode."
"Ka kar6a, I insist." Tace dashi ba tare da ta mayar ba.
Bai k'ara musu ba ya kar6a yana mata godiya ta tayar da motar har ta 6ace masa da gani.
Wani tsalle yayi bayan tafiyarta kana ya fara k'irga kud'in. Dubu biyar cass ne a hannunsa ba tare da yayi aikin wahala ba.
"Kai mutumina me ka samu naga bakinka yak'i rufuwa haka?" Abokinsa Nasir ya tambayeshi yana mai gyara zaman belt d'inshi.
"Shiganka band'aki ya mini rana wallahi, kawai wata mata na d'aukarwa leda na saka mata a mota ta bani dubu biyar, dubu biyar mutumina. Wallahi ji nake yi kamar tsintarsu nayi." Ya fad'a yana mai k'ara k'irga kud'in kamar shi kanshi bai yarda ba.
"Kutma!! Sai nima ka bani rabona domin sai da nayita rok'anka sannan ka yarda ka jirani, kai amma tayi maka arziki, dama gashi wata yayi nisa." Nasir ya fad'a yana kaiwa kud'in cafka, amma saurayin ya soka kud'in a aljihunsa yana dariya.
"Zan baka amma ka nitsu, hingo ga d'ari biyar." Ya mik'a mishi wata kod'addiya da tun satin baya yake tsumulmularta.
"Wallahi Haydar baka da mutunci ko kad'an, don ubanka ka rasa abunda zaka bani sai d'ari biyar? Kai rawa kayi ka samu ko kuma kasan da zaka samu? Wallahi in baza ka bani dubu biyu ba ka rik'e kayanka."
K'arshe dai wata d'ari biyar d'in Haydar ya k'arawa Nasir sannan suka daidaita suka kama hanyar gida yana lissafin me zai yi da kud'in yana kuma bawa abokin nashi labari,
"Kaga matar kuwa? Ga kyau, ga kwalliya yanda kasan matan larabawa. Ina ga ma balarabiya ce domin tun data fito nake jin k'amshin turarenta har yanzu."
"Dole ka fad'i haka mana tunda ta baka dubu har biyar." Nasir ya gwatsaleshi don haushin bai bashi dubu biyun ba.
Dama tashinsu daga aiki kenan Nasir ya nemi ya zagaya band'aki har ya tsinci dami a kala.
Laila bata koma gida ba kamar yanda ta tsara tun farko, gidan Madu ta isa domin bawa Ummii abunda ta sayo mata.
Tana ganin motar Madu a farfajiyar gidan taji kamar ta koma, amma da ta tuna cewa ba tsayawa zata yi ba yasa ta d'auki ledan ta shiga.
Ko sashen matansa bata shiga ba kawai ta wuce gurin Ummii.
Sai dai tana shiga ta ganshi zaune a k'asa yana yankewa Ummii farcen k'afarta yayinda ita kuma ke saman kujera tana masa magana.
Ganinta yasa duk suka yi shiru daga hiran da suke yi. Sallama ta sake yi wanda Ummii ta amsa rai babu dad'i.
Ganin hakan yasa jikinta yayi sanyi domin tasan tabbas wata k'aryar Madu ya mata.
"Ummii ina wuni."
"Lafiya." Ta bata amsa a tak'aice tana kallon gefe.
"Ya Madu ina wuni."
Bai amsa ba, sai ma wani harara da yake watsa mata tamkar zai mareta.
"Ummii dama turaren wutan Duggat Al Oud Cambodi na kawo miki. Yau naje wani sabon super market na gani na tuna kina so." Ta fad'a cikin fara'a tana mai mik'awa Ummii ledar.
"Sai aka ce miki bana providing duk abunda take buk'ata sai kin sayo da kud'in da ba'a san a ina kike samu ba?" Wannan fad'in Madu kenan wanda ke tashi tsaye yana nunata da yatsa.
"Madu, ka daina sukar k'anwarka da abunda baka tabbatar ba." Ummii ta tsawatar masa tana dubanshi rai babu dad'i.
Laila da ba yau ta ta6a jin hakan daga bakin Madu ba ta kalli Ummii cikin karaya tace,
"Ummii kema kin fara yarda da cewa yawon banza nake yi ko?" Lokaci d'aya idanunta suka tara hawaye domin rad'ad'in da take ji a zuciyarta.
"Idan Yaya Madu zai mini wannan k'azafin ke Ummii baza ki yarda ba. Kinfi kowa sanina da kuma sanin halina Ummii. Ban ta6a harkar banza wajen tara dukiyata ba, wallahi ban ta6a ba." Ta fad'a yayinda hawaye ke zuba a fuskarta.
Sunkuyar da kai Ummii tayi yayinda itama hawayen ya fara taruwa a idanunta, ganin haka yasa Madu ya nuna Laila da yatsa.
"Kin gani ko? Daga zuwanki har kin sakata cikin bak'in ciki saboda tsabar taurin kanki da nuna isa. Ki tashi ki fita mini a gida kafin kisa jininta ya hau, dama kin saba."
Laila ta tashi a zuciye tana kallonshi ido cikin ido,
"Kayi nasarar shiga tsakanina da mahaifiyata amma ka sani; har duniya ta nad'e baza ka ta6a goge son da take mini don k'aryar da kake zuwa kana fad'a mata a kaina ba. Kuma na barka da Allah akan k'azafin zina da kake mini Ya Madu, wallahi Allah yana gani kuma shi zai mini sakayya." Tana fad'in hakan ta juya zata fita.
Kwal taji abu ya daki k'afarta wanda sai da taji zafi har tsakar kanta, da mamaki ta juyo tana ganin me ya daketa haka.
Ashe ledan da ta kawowa Ummii ce Madu ya jefo mata yana cewa,
"Ki d'auki tarkacenki bata buk'ata domin ni kad'ai zan iya mata komai. In banda k'aryar banza, mace kina zaune tsawon shekara ashirin babu miji kuma har kike iya bud'e baki ki kare kanki? Wani shiga da ficenki ne ban sani ba? Wallahi idan baki daina wannan rayuwar ba Laila kiyi kuka da kanki tun kafin had'uwarki da ubangijinki."
"Madu ka mini shiru nace ko?" Fad'in Ummii itama tana tashi tsaye.
"Naji ina yin zina, kai kuma da ka rik'e dukiyar marayu na ubangidanka kake tauye musu hak'k'insu fa? Me marabanka dani mai zina in ma da gaske ne ina yi?" Ta mayar masa da martani tana sakawa a ranta ta daina yin shiru idan ya cigaba da sukarta da aikata zina.
"Ni kike fad'awa haka? Ummii kina jin yarinyar nan ni take kira mai cin dukiyar marayu?" Fad'in Madu yana mai nuna kanshi da yatsa yana kallon tsakanin Laila da Ummii wacce ke kuka.
"Ku kasheni ku huta dama ni d'aya na rage muku. Yau idan Allah ya kar6i raina zan fi kowa murna domin masifarku da kuma halin da kuke jefani ciki ya isheni."
Zuciyar Laila ce ta karye domin hakan na d'aya daga cikin dalilin da yake hanata tankawa Madu, amma yau ta rasa hak'urinta har tayi sa'insa dashi a gaban Ummii.
"Ummii kiyi hak'uri ki gafarceni, amma kina jin abunda yake fad'a a kaina...."
Kafin ta k'arasa magana Ummii ta dafe kanta idanunta na juyawa.
Da sauri Madu ya kamota yana mai ajiyeta a kan kujera yana kiran sunanta cikin kid'ima.
Laila ma da gudu tayo kanta tana kiran sunanta, ruwan da ke ajiye a gefenta ta d'auko kana ta fara bawa Ummii tana kiran sunan Allah.
"Ummii, Ummii." Madu ya cigaba da kiran sunanta yana jijjigata.
"Kin ga abunda kika jawo ko? Yanzu kam hankalinki ya kwanta? Ki tashi ki fita kafin raina ya 6aci in fitar dake da kaina."
"Bazan fita ba, idan kana gadarar gidanka ne ni kuma gurin uwata na zo."
Ummii ta bud'e idonta ta kyar ta kalli Laila tace,
"Yalla Laila, ki tafi."
"Ummii..." Bata k'arisa ba Ummii ta d'aga mata hannu wanda hakan yasa Laila ta mik'e tsaye hawaye na zuba a idanunta ta fita daga falon.
Ina zata saka ranta? Me ta yiwa Madu da Ummii? Ya zata yi? Wad'annan sune tambayoyin da take ta yiwa kanta wanda silarsu duk akan ta k'i yin aure ne. A kan namiji ake mata wannan k'azafin, wai don bata da aure? Wa yace aure dolene? Ko sun manta cewa sunnah ce ta Annabin Rahama ba wai wajibi ba? Meyasa suka kasa gaskata cewa bata zina kuma bata ta6a kusantarta ba? Wai meyasa?
Tafi minti biyar zaune a cikin motarta tana kuka kafin ta kunnata ta fita daga gidan Madu, wanda yawanci in dai tazo sai wani abun ya faru muddin ta had'u dashi.
Shiyasa data lura da hakan ta daina zuwa sai da safe ko rana idan ya fita aiki. Yau ma ta danganta zuwanta da tsautsayi tunda tasan yamma tayi ya dawo gida.
Unguwar Jakara ta wuce inda gidanta yake wanda ta ginashi da kud'inta.
YOU ARE READING
RUWAN ZUMA (completed)
RomanceShin wani irin kallo kake yiwa masoya biyu wad'anda akwai tazarar shekaru tsakaninsu, musamman ma in aka ce Macen ta fi Namijin yawan shekaru? Tayi wuff dashi, ko Tsoho yayi wuff da yarinya. To ga labarin wani matashin saurayi mai farin jinin 'yan...