Bismillahir rahmanir rahim.
February 1997...A cikin d'akin wata matashiyar budurwa ce mai kimanin shekara sha bakwai tsaye a kan sallaya tana sallah, can bakin k'ofa ta waje kuma wani saurayi ne da shekarunsa zasu kai sha hud'u yake kaiwa da komowa, da alama jira yake ta gama sallah ya mata magana.
Tana idarwa ko addu'a bata yi ba ta jiyo muryansa a tsakar kanta tamkar zai tada gidan.
"Kalti Laila ga can mutumin jiya a waje, wallahi yau ma ya dawo." Yace da ita yana mai shigowa cikin d'akin tun kafin ta masa iso.
Bata kulashi ba, haka kuma bata juyowa ba sai da ta gama addu'arta ta shafa sannan ta juyo da dara-daran idanunta ta zabga masa harara.
"Kai wani irin mutum ne Mas'ud? Ina jinka ka shigo gidan nan da gudu kamar wanda yayi gamo da aljanu." Ta mik'e tsaye tana ninke abun sallar dake hannunta.
Da haka ta kwa6e hijabinta ta zauna bakin katifa tana mai jawo robar kayan kwalliyarta kusa da ita, dama fitowanta daga wanka kenan zasu tafi islamiyya. Mai ta fara shafawa sannan ta bad'e fuskarta da hoda tana gyarashi da wani tsumman zani.
Mas'ud da bai ji dad'in yanda yayar tashi ta kar6i zancen ba sai ya zauna kusa da ita ya zuba mata idanu baya ko kiftawa.
Laila da har lokacin zuciyarta bai daina bugu ba tunda ta ji labarin mutumin jiya, tace,
"Da kazo ka tasani a gaba kwalliyar kake so na maka? Kuma kasan zamu yi lattin zuwa islamiyya, gashi daga jin yanda jikinka ke tashin tsamin nan ko wanka baka yi ba. Don Allah ka tashi ka shirya mu tafi." Ta k'arisa maganan tana shafa janbakin Majik a bakinta had'e da zizara kwalli a idonta.
Mas'ud har zai bud'e baki yayi magana sai kuma ya fasa, mik'ewa tsaye yayi yana karkad'e rigarsa yayi hanyar fita amma murmushi ne a fuskarsa sosai saboda yasan yanda mutumin ya tsaya mata a rai dole ta nemi k'arin bayani.
Har ya je bakin k'ofa ya tsinkayo muryar yayar tashi cikin kunya tana cewa,
"Umm... Mas'ud. Wai me mutumin ya fad'a?"
Ai da gudu ya dawo gefenta ya zauna bakinshi a washe yana cewa,
"Wai cewa yayi in yi kiranki. Har ya bani Naira d'aya, kin ganta nan." Ya zaro kwandalar daga aljihunshi ya nuna mata.
"Hmm, kud'in nan ya maka yawa Mas'ud. Ka kawo in ajiye maka ka dinga kashewa a hankali." Tace dashi tana mai kar6an kud'in ta sokeshi a k'asan katifarta.
Bai damu ba, haka ya tashi ya fita daga d'akin don yin wankan da ta ce yayi.
Yana fita ta sauk'e wata ajiyar zuciya wacce bata ma san ta rik'e ba, wai mutumin jiya ne a waje? Me kuma ya dawo dashi yau?
A gurguje ta gama shiryawa cikin 'yar atamfarta d'inkin riga da zani. D'aurin d'ankwali ta kafa sak irin ta Maryam Babangida sannan ta d'auki turarenta da ke cikin wata guntuwar kwalba ta d'iga a hannunta sannan ta shafa a rigarta, ta maimaita hakan har sau uku sannan ta rufe ta ajiye.
Mayafi ta yafa wanda ya rufe dukkan ilahirin jikinta, kana ta d'auki Al Qur'ani mai rubutun Warshi ta rik'e a hannunta, da haka ta fito k'ofar d'akin ta samu takalminta kobashu ta sak'alawa k'afafunta.
In ka ganta a wannan lokacin zaka d'auka koktel (cocktail) ta nufa ba makarantar allo ba, don tsabar kwalliya da had'uwar da ta yi.
A tsakar gida ta bakin madafi ta hango mahaifiyarta zaune a kan kujeran tsuguno tana tankad'en garin masara.
"Ummii zamu tafi makaranta." Ta ce da ita bayan ta iso gurinta.
"Sannu Dawisu uwar ado, wato ke duk fad'an da za'a miki akan saka jambaki in zaki tafi makaranta sam bakya ji ko? Jiya ba Marwa ce ke fad'amin malaminku ya sakaki goge bakinki da bayan takalmi ba?" Ummii ta tambayeta tana mai rik'e ha6a ganin nacewa da kuma taurin kai irin na Laila akan kwalliya har ya fara yawa.
"Ummii k'arya suke miki. Shatuwa kad'ai aka saka ta goge amma banda ni. Haba, da girmana da ajina a ce wai ni Laila Choge ce za'a saka ta goge bakinta da bayan takalmi? Ai ban ga wannan malamin ba kaf fad'in Kanon dabo." Ta k'arisa maganan cike ta jin kai.
"A dai juri zuwa rafi." Kad'ai Ummii ta fad'a kana ta cigaba da tankad'en ganin kishiyarta Tabawa ta fito daga d'akinta da buta a hannu.
Wani irin kallon sama da k'asa Tabawa ta bi Laila dashi kamar idanunta zasu juye. Ganin kallon yayi yawa yasa Laila yiwa Ummii sallama ta fita tana cewa Mas'ud da ya fito daga wanka,
"Ka sameni a hanya."Tana fita ta hango mutuminta na jiya yau ma tsaye a jikin besfanshi hannunsa bisa k'ugunshi, tsayuwa yayi irin ta gayu ajin k'arshe.
Zuciyarta ce ta k'ara bugawa a karo na biyu, ta rungume Al Qur'anin hannunta a k'irji sannan ta fara takowa ta zo zata wuce ta gabanshi ba tare da ta masa magana ba.
"Laila." Ta jiyo sautin muryanshi a kunnenta a karo na farko tun had'uwarsu jiya. Dama yana magana ne? Ashe haka sautin muryarshi take da dad'i?
Tsayawa ta yi cakk, sannan ta juyo tana kallonshi fuskarta a had'e kamar wacce ta ga bak'in sak'o.
"Don Allah bani minti biyu daga cikin lokacinki." Yace da ita yana mai cire hannunsa daga k'ugunsa.
Ta kai sakan biyar tsaye sannan ta tako ta iso gurinshi ta tsaya nesa tana kallonshi.
Gyara tsayuwarsa yayi ta hanyar mik'ewa da dukkan tsayinsa, hakan yasa dole sai Laila ta d'aga ido kafin ta ga kwayar idanunsa. Abunda yake k'ara burgeta dashi kenan, wato mutumin akwai tsayi bayan gayu da ya iya, shiyasa tun kafin ta san sunansa ta ji ya burgeta duk da cewa had'uwarsu ta farko ya 6ata mata rai.
Kawar da kanta ta yi bata son su had'a ido, zuciyarta na bugawa idan ta kalli tsabar kwayar idonsa.
"Assalamu alaikum." Yace da ita bayan ya fuskanceta.
"Wa'alaiku mussalam." Ta amsa masa har lokacin bata dubeshi ba.
"Sunana Aliyu. Na san jiya ranki bai yi dad'i ba da abunda na miki. Ina mai baki hak'uri kuma na d'auki laifina da ban sanar da ke dalilin da yasa na yi hakan ba."
"Ah to ya fi maka. Haka kawai ka aika a kirani a cikin gidanmu sannan in fito ka k'i mini magana har sai da na gaji na koma. A ina ake haka?" Tace dashi cikin k'uluwa don har lokacin abun na ci mata rai, sai dai duk abunda ya mata bai hana zuciyarta yaba tsarin halittarsa da kuma hana idanunta ganin gayunsa ba. Ai ita mutum mai tsafta da ado ko mak'iyinta ne yana burgeta.
"Naji nayi laifi. Amma dalilin da yasa kika ga nayi haka saboda rashin sallamar da kika mini ne bayan kin fito kin sameni. Shirun da nayi jira nayi ki mini sallama saboda nasan kin san muhimmancinta." Cewar Aliyu yana mai zuba mata ido yana nazarinta.
Zaro ido Laila ta yi kunya sosai ta rufeta har tana 6oye fuskarta da littafin hannunta. Wato duk wannan fushin da ta yi laifinta ne ba nashi ba? Ina ilimin zuwa islamiyyarta yake da ta kasa yi masa sallama bayan ta fito.
"Laa. Don Allah kayi hak'uri, mantawa na yi. Ina wuni." Ta samu kanta da fad'i bayan ta bud'e fuskar tata.
"Lafiya kalau. Ya mutan gidan duka?" Ya tambaya yana mai yaba halinta na saurin d'aukar laifinta. Ashe yarinyar tana da hankali.
"Kowa lafiya kalau." Ta bashi amsa tana kallon k'ofar gidan nasu ganin shiru har lokacin Mas'ud bai fito ba.
"Kar In tsayar da ke, naga kamar islamiyya zaki tafi ko?" Yace da ita yana mai tayar da besfanshi.
Ran Laila ya d'an sosu kad'an, daga fara magana har zai ce zai tafi? Lokaci d'aya kuma ta kwa6i kanta don tasan gaskiya ya fad'a. Wai me yake damunta ne? Ta tambayi kanta. Jiya suka had'u amma har bata son rabuwa dashi?
Mas'ud ne ya fito daga gidansu ya nufosu yana dariya, ganinsa yasa Laila tamke fuska tana masa ido amma ina bai gani ba.
"Kalti Laila ba kin ce baza ki k'ara tsayawa dashi ba?" Mas'ud yayi kato6ara.
Aliyu da ke kan abun hawansa yayi dariya ya ce,
"Ashe haka kika fad'a? Gashi kuma ni yanzu ma na fara zuwa, kuma zan dawo anjima da dare. A yi karatu lafiya." Da haka ya barsu tsaye kunya kamar ya kasheta.
Yana k'ulewa ta juyo gurin Mas'ud ta danna mishi rankwashi a tsakar ka.
"To waya tambayeka? Wallahi zan ci kaniyarka in baka daina wannan fad'i ba'a tambayekan ba. Yi gaba mu tafi Kafin mu yi latti."
Da haka suka kama hanyar islamiyyar Mas'ud na sosa gurin da aka rankwasheshi, sai dai ko kad'an bai nuna ranshi ya 6aci ba, hasalima dariya yake yi yana mata gwalo.
Sun ci rabin tafiyar a haka Mas'ud na tsokanarta har ya sakata dariya,
"Ka san meya faru Mas'ud? Ina fitowa kawai na ganshi a waje yayi irin wannan tsayuwar da yake burgenin nan. Har zan wuce sai ya kira sunana, ya mini sallama. Shine yake fad'a mini dalilin da yasa jiya har ya tafi bai mini magana ba wai don ban masa sallama bane. Ka san kunyar da naji kuwa? Ji nayi kamar in ruga cikin gida." Ta bashi labarin abunda ya faru tamkar tana magana da wata k'awarta.
"Kin yi fushin banza kenan? Ni dama na san dole ku shirya. Wallahi ko Kalti, gayen yana burgeni, Idan na ganshi sai naga babu wacce ta dace ta zama matarsa sai ke. Kin ga shi gayu, ke gayu 'ya'yanku ma duk su tashi cikin gayu muna kaisu gidan d'aukan hoto ana musu jumbo kati." Ya k'arishe maganan yana kallon sama alamar yana hasko hakan a idanunsa.
"To kai da kake ta surutunka ka ji yace yana sona ne? Ko nace maka Ina sonshi ne?" Ta fad'a tana d'an bugin kafad'arsa cikin wasa, yayin da fuskarta kuwa cike take da annushuwa.
"Ni nasan yana sonki ne, kuma wallahi shi zaki aura ba Abdul ba." Mas'ud ya 6ata rai.
Zuciyar Laila ce ta buga da k'arfi wannan karon na wani abu na daban. Lokaci d'aya kuma fara'ar fuskarta ya d'auke.
Da haka Mas'ud ya juyo da niyyan mata magana amma ganin halin da ta koma yasa ya rufe bakinsa. Hannunta kawai ya rik'o, itama ta damk'e nata cikin nasa suka cigaba da tafiya. Ba dole sai sun yi magana ba, dashi da ita duk sun san abunda ke zuk'atansu.
YOU ARE READING
RUWAN ZUMA (completed)
RomanceShin wani irin kallo kake yiwa masoya biyu wad'anda akwai tazarar shekaru tsakaninsu, musamman ma in aka ce Macen ta fi Namijin yawan shekaru? Tayi wuff dashi, ko Tsoho yayi wuff da yarinya. To ga labarin wani matashin saurayi mai farin jinin 'yan...