Bayan tafiyar Laila, Alhaji Abdul ya kira Jennifer ya had'ata da Haydar suka fita tare.
Haydar bai bar ma'aikatar ba sai bayan azahar. A gajiye ya koma gida ya zauna a rumfarsu Ammi ta kawo masa ruwa.
"Ali yaya dai?" Tace dashi ganin yanda ya shigo a jikkace kamar wanda ya wuni yana aiki.
"Wallahi Ammi na gaji ne, tunda naje ban zauna na huta na minti biyar ba." Ya bata amsa yana cire rigarsa ya ajiyeta a gefensa.
"A hankali zaka saba, bari na kawo maka abinci kaci sai ka kwanta ko zuwa la'asar ne."
Bayan yaci abinci ya dawo cikin hankalinshi ya fara bawa Ammi labarin yanayin aikinsa da kuma albashinsa.
"Zasu dinga bani dubu talatin da biyar duk wata, Idan kuma na kai wasu watanni biyar ko shida suka ga na iya aiki zasu k'ara mini matsayi da kuma albashi. Ammi kici gaba da mini addu'a domin inaga wannan aiki dana samu shine cikar burinki wanda kika tsaya kai da fata akai sai nayi karatu."
"In Allah ya yarda Haydar. Kai dai ka rik'e gaskiya da amana a duk inda ka tsinci kanka, hakan shi zaisa ka samu nasara akan abunda kasa a gaba." Ammi ta shafa kanshi tamkar k'aramin yaro tana kallonshi cike da so da k'auna.
"Ammi ki shirya gobe zamu je gidan Hajiya Laila ki mata godiya domin hakan ya faru ne duk ta sanadinta."Washegari kamar suka dira a gidan Laila. Ammi dai tunda suka shiga take kalle-kalle tana yiwa Aliyu magana kan gidan.
Suna shiga falon Laila Ammi ta shak'i k'amshin turaren wutan dake ciki tace,
"Amma uward'akin naka Shuwa ce ko?"
"Ammi don Allah kiyi shiru." Shine abunda ya fad'a yana mai zama a k'asa, shiru Ammi tayi amma sai da ta harareshi tukun.
Itama a k'asan ta zauna tana shafa lallausar carpet d'in dake malale a falon.
Suna zama Laila ta fito daga kitchen hannunta d'auke da tray mai d'auke da ruwa, juice da kuma glass cup biyu.
"Sannunku da zuwa. Sannunku." Shine abunda take fad'a tana ajiye tray d'in a k'asa.
"Maman Haydar don Allah ki tashi ki zauna a kujera." Ta fad'a tana zama a kujera fuskarta d'auke da fara'a.
"Karki damu Hajiya, k'asan ma yayi."
"Maman Haydar baza ayi haka ba, ai bazan ji dad'in zama a sama ke kuma kina k'asa ba." Da haka Laila ta zamo daga kan kujeranta ta zauna a k'asa wanda hakan ba k'aramin mamaki ya bawa Haydar da Amminsa ba.
"Ina wuni?" Laila ta gaisheta tun kafin su bud'i baki su fad'i wani abu.
"To Hajiya za'ayi haka? Keda gidanki zaki zauna a k'asa?"
"Babu komai Ammi, haka kake kiranta ko Haydar?"
Haydar da har lokacin yana cikin mamaki ya d'aga kai alamar 'eh' kana ya gaisheta.
"Ina wuni Hajiya, mun sameku lafiya?" Ammi ma ta gaisheta tana mai d'an sunkuyawa kad'an.
"Lafiya kalau Hamdallah, kun zo lafiya? Ya hidima?"
"Lafiya Hajiya, ya kuma d'awainiya da Ali? Da fatan baya miki rashin hankali?"
"Ammi!" Haydar ya kwa6i mamarsa yana mata ido.
"K'arya nayi? Kana da hankalin ne?" Ammi ta danna masa harara kana ta maida dubanta ga Laila wacce ke dariya sosai.
Hakan ba k'aramin burgeta yayi ba, wai uwa da d'anta ne haka? Inama itama zata yi haka da Ummii! Ai da tafi kowa jindad'i a duk duniyar nan.
"Ke Shuwa ce ko?" Ammi ta sake yin tambayarta ta d'azu wacce Haydar yak'i amsa mata.
"Ammi!" Haydar ya sake kwa6arta yana ta6a k'afarta.
Buge hannunsa Ammi tayi kana ta juya gurin Laila tana murmushi.
"Ni Shuwa ce kuma Kanuri." Ta amsa mata tambayarta, a ranta kuma tana jin Ammin ta burgeta.
"Ai ina shigowa gidan naji k'amshin turarenmu, dana ganki kuma sai na tabbatar da hakan. Gade tahaawili bilhen fok waladi, inti kula Allah ikaffi leki hawa'ijki hinel-khair. Shukran."
"Ohh, kema Shuwa ce?" Laila ta zaro ido tana k'are mata kallo.
Shigar hausawa Ammi tayi ta atamfa riga da zani da kuma hijabi wanda wannan ba shigarsu bace ta Shuwa. Sai a lokacin Laila taga d'an kamanninsu a fuskar Ammi wanda dashi suke gane junansu a cikin mutane dubbanni.
Ammi bata amsa maganar kai tsaye ba illa kad'a kai da tayi amma kuma murmushi dake fuskarta ya d'auke d'iff na wasu sakanni lokaci d'aya kuma ta dawo da fara'arta tamkar ba ita ba.
Haydar dake gefe ya kafe idanunsa a kan Ammi zuciyarsa na tafarfasa tamkar zata faso k'irjinsa.
Lokaci d'aya yaga Ammi da Laila sun 6arke da hira ta harshen Shuwa, yanda suke karya harshe cikin kwarewa zai baka sha'awa amma banda Haydar wanda yake jin kanshi ya fara ciwo nan take.
Ganin duk hankalinsu baya kanshi yasa ya tashi ya fita daga falon yana jin duniyar na juyawa kamar zai fad'i a k'asa.
Kujerar roba ya samu ya zauna a kai kana ya dafe kanshi da hannayensa biyu, yayinda tambayoyi bila-adadin suka fara zarya a kwakwalwarsa.
Bai san lokacin daya d'auka zaune a gurin ba sai gani yayi Laila da Ammi sun fito suna dariya tamkar wad'anda suka jima da sanin juna.
Mik'ewa yayi tsaye yana k'ak'alo murmushi wacce iyakarta fatar baki ya dubi Laila yace,
"Hajiya muna k'ara godiya, Allah ya saka."
"Gaskiya sai dai Allah ya biyaki, nima gashi daga zuwana ta bani turaren wuta da kuma laffaya guda biyu da turmin zani biyu. Ka tayani godiya Haydar."
Kafin ya bud'i baki yayi magana Laila ta rigashi tana cewa,
"Ma fe mushkila Ammi. Nice da godiya domin naji dad'in zuwanki."
Sai da suka k'ara tsayuwa na minti goma suna yare sannan suka mata sallama suka tafi.
Haydar yak'e kawai yake yi a gaban Laila gudun kar ta gane halin da yake ciki, amma suna fita fuskarsa tayi daidai da yanayin da zuciyarsa take ciki. Sai daya tabbatar sunyi nisa da gidan sannan ya dakata daga tafiya ya tsaya.
Ammi da take bin bayanshi tazo ta wucesa tamkar bata ganshi ba, sai dai bata yi taku uku ba taji muryar Haydar a dodon kunnenta cikin murya mai d'auke da bak'in ciki, takaici, da kuma wani abu da za'a iya kira 'hope' a muryarsa yana cewa,
"Ammi mu Shuwa ne?"
Tsayawa tayi na sakanni goma zuciyarta na bugawa sannan tace,
"Mun gama wannan maganar Haydar. Kazo mu tafi gida." Taci gaba da tafiya ta barshi a gurin har ta 6ace masa daga gani.
Hawaye ne masu zafi suka sauk'a akan kumatunsa kana wasu suka cigaba da biyosu babu k'ak'k'autawa.
YOU ARE READING
RUWAN ZUMA (completed)
RomanceShin wani irin kallo kake yiwa masoya biyu wad'anda akwai tazarar shekaru tsakaninsu, musamman ma in aka ce Macen ta fi Namijin yawan shekaru? Tayi wuff dashi, ko Tsoho yayi wuff da yarinya. To ga labarin wani matashin saurayi mai farin jinin 'yan...