"Abul baka iya gaisuwa bane?" Laila ta kwa6i d'anta tana mai masa ido kar ya kunyatata.
Juyawa yayi ya kalli Haydar sama da k'asa sannan yace,
"Sannu."
"Kana lafiya? Ina yawan jin labarinka a gurin Hajiya." Fad'in Haydar yana mik'awa Abul hannu.
"Mama waye shi? Wannan karon da 6acin rai yayi tambayar domin yaga saurayin na shige masa da yawa, kuma bai mik'a mishi hannu suka gaisa ba.
"Abul behave, baka ganin yana mik'a maka hannu ne?" Ta k'ara kwa6arshi kamar k'aramin yaro.
Bai k'ara magana ba ya juya a zuciye ya shige cikin gidan har yana buga k'ofar da k'arfi kamar zai cireta.
Haydar da abun ya bashi mamaki ya kalli gefe kamar hakan bai faru ba.
Laila kuma kunya ce ta kamata domin tana bawa Haydar labarin su Abul tana kuma yabon halinsu da kuma tarbiyyarsu, to gashi a had'uwarsu ta farko ya nuna ba hakan ba.
"I'm sorry, Abul baya sabawa da mutum farat d'aya. Kuma wai don shirme baya son ya ganni tsaye da kowanne namiji balle in ce zanyi aure."
"To ai yin auren ma ba laifi bane." Fad'in Haydar yana murmusawa.
"Well....da wannan ma don wannan."
Haydar ya lura har lokacin abunda Abul yayi na damun Laila, domin hatta murmushin da take yi d'azu babu shi a fuskarta. Me zai yi ya sakata dariya domin ganinta cikin farinciki shine burinsa? Yaushe hakan ya zama burinsa? Ya tambayi kanshi.
"Amma yanzu wannan babban saurayin d'anki ne?" Ya d'an nuna mamaki a fuskarsa.
"D'ana ne, shekararshi ashirin da uku."
"Amma Hajiya in an ganku tare wallahi baza'a ce d'anki bane, sai dai ace k'aninki ne." Ya fad'a tsantsar gaskiyarsa.
Wata dariya Laila tayi mai dad'in sauti wacce tasa Haydar shagala da kallonta ba tare da ya gane abunda yake yi ba.
"Hmm Haydar kenan. Wai haka kowa ke fad'i idan an ganmu tare."
Bai bar gurinta ba sai da ya k'ara sakata dariya kana suka yi sallama ya tafi mayar da motar kantinsu."To ka aikomin da rabona mana." Fad'in Nasir bayan Haydar ya shigo cikin kantin.
"Kai kaga kud'in nan wallahi kayan abinci zan sayawa Ammi sauran kuma in bata na cefene. Ga dubu d'aya ka rik'e ko tsire ka sayawa Halima."
Ya mik'a mishi dubun wanda Nasir ya k'arba ba godiya sai ma ashar da ya narka masa.
"Idan ta daina baka zamu zama d'aya ai."
"A rage hassada dai mutumina." Cewar Aliyu yana dariya.
Daga nan kasuwa ya nufa ya auno shinkafar tuwo, ta dafawa mai, manja da sauransu ya koma gida."Allah abun godiya, sannu d'an nan. Allah ya k'ara bud'i ya k'ara maka arzik'i da zuciyar yi." Haka Ammi tayita addu'a tana bud'e kayan abincin da Haydar ya kawo mata.
Shi kuma yana zaune a gefe sai murmushi yake yi yana amsawa da Amin.
"Ha'a, har da kayan shayi? Wai ina ka samu kud'i ne? Naga wata bai yi k'arshe ba."
"Wannan uward'akin nawa dai da nake baki labari, yau ma na kai mata kaya shine ta bani har dubu goma." Ya bata amsa yana ciro kud'i a aljihunsa.
"Ki rik'e dubu na cefene nima zan rik'e dubu na zuwa gurin aiki." Ya fad'a yana mik'a mata kud'in.
Da haka ya ciro wata leda a aljihunsa ya bud'e yana kallon Ammi wacce ke kallon ledar.
"Kai Ali har da tsire? Wannan uward'aki taka Allah ya mata albarka ya k'ara bud'a mata k'ofofin arziki. Ni da zaka yadda ai da sai muje gidanta in mata godiya." Ammi ta tura tsokar nama d'aya cikin bakinta.
"Ai baki ma san babban abun farinciki ba, tace ranar litinin jibi kenan in je gidanta daga nan kuma zamu je wani ma'aikata da za'a d'aukeni a aiki."
Shakewa Ammi tayi da tsokar dake bakinta, ai kuwa ta hau tari ba kakkautawa. Da sauri Haydar ya d'auki ruwan zo6on daya saya mata ya bata ta kur6a yana mata sannu.
Gyaran murya tayi tana sosa wuyanta tace,
"Ali irin wannan labarin ai baza ka fad'awa mutum da tsokar nama a bakinshi ba. Yau naga farin rana jumma'a haji babbar rana. Allah mun gode maka."
Haka Ammi tayita godewa Allah cikin farinciki tana k'ara yiwa Laila addu'a.
"Ammi kici naman kar yayi sanyi." Ya fad'a yana had'iye yawu domin ita kad'ai ya sayawa saboda k'arancin kud'in hannunsa.
"To sa hannu muci mana, naga kamar kaima baka ci ba."
"A'a Ammi, ai naman babu yawa ke kici kawai."
"Kaji mini maganar banza, ai bazan iya cin abu in hanaka ba Ali, maza d'auka." Ta fad'a tana mai tura masa ledar gabansa.
Dariya yayi kana yasa hannu ya fara ci yana bata labarin kalar kirkin uward'akinsa Laila.
Bayan sun cinye Ammi ta had'a musu shayi suka sha da biredi, sai a lokacin da tuno da d'anwaken da Minat ta kawo masa.
"Ali ga d'anwaken nan na ajiye maka." Ta jawo kwanon a k'ark'ashin gadonta tana bud'ewa, duk yayi sanyi ya k'andare.
"Nifa bazan ci ba, ji nayi na tsani d'anwake ma wallahi. In banda shirmenta ina naga kud'in yin soyayya ko aure? Yanda ubanta yake da tsananin nan ina fara kulata zai ce in turo! To me zan tura Ammi? Kema ki daina kar6an abunda ta kawo don wallahi ba biya zan yi ba."
YOU ARE READING
RUWAN ZUMA (completed)
RomanceShin wani irin kallo kake yiwa masoya biyu wad'anda akwai tazarar shekaru tsakaninsu, musamman ma in aka ce Macen ta fi Namijin yawan shekaru? Tayi wuff dashi, ko Tsoho yayi wuff da yarinya. To ga labarin wani matashin saurayi mai farin jinin 'yan...