Babi na sha tara

821 87 1
                                    


"Ali!!" Ammi ta kwa6eshi tana bugin k'afarshi ranta a 6ace.
"Ki fad'a mata Hajiya Laila." Ya zuba mata ido yayinda ita kuma take kallon gefe fuskarta babu wannan fara'ar.
"Ali ka tashi ka fice mini a gida tunda ba zaka iya yin shiru ba. Ita Hajiyar sa'arka ce da zaka dinga mata irin wannan wasan? Ban ce kar in saka jin ka tayar da zancen nan ba? Menene bata maka? Sannan don rashin kunya da rashin sanin girman mutum sai ka tunkareta da shirmen nan? Ali zan 6ata maka rai yanda baka tsammani, wallahi ka shiga hankalinka kasan da wa kake magana." Wannan fad'in Ammi ce cikin 6acin rai tana nuna Haydar da yatsa shi kuma yana kallon Laila.
Laila ta dubi yanda Ammi ke huci sai taji tausayin Haydar ba kad'an ba ya k'ara shiganta, tace,
"Shiyasa naso na masa aure tun kwanaki saboda a tunanina rashin aurensa ne ya kawo wannan zancen. Haydar kaji da kunnenka abunda Ammi tace ko?"
Girgiza kai yayi kana yayi d'an murmushi kamar bashi aka yiwa rufdugu ana yiwa fad'a ba. Yace.
"Ina son miki wata tambaya d'aya kuma ina son ki fad'i tsakaninki da Allah."
Ammi zata yi magana Laila ta katseta da cewa,
"Ammi zan amsa masa tambayarsa, saboda ina son a yau a kawo k'arshen wannan maganan."
"Kinyi alkawarin zaki fad'i tsakaninki da Allah?"
Murmushi Laila tayi don tasan zata iya fad'a mishi koma menene don bata shakkarshi ko wani abu.
"Nayi." Ta furta tana masa kallon yaro mai tarin yarinta.
"Idan daa za'a ce Ammi zata yarda ki aureni sannan mutanen duniya baza suyi zund'enki ba, shin zaki aureni Hajiya Laila? Karki manta kince zaki fad'i gaskiya!"
Wannan karon sunkuyar da kanta k'asa tayi na sakanni biyar kana ta d'ago tana ganin yanda dashi da mahaifiyarshi suka zuba mata ido suna jiran amsarta.
"I don't know Haydar." Shine kad'ai amsar data bashi kana ta mik'e tsaye tana gyara laffayanta tana cewa.
"Ammi zan tafi."
"Baki bani amsa ba." Ya furta shima yana mik'ewa tsaye.
Ajiyar zuciya Laila ta sauk'e kana ta dubeshi cikin ido tace,
"Kamar yanda kwanaki na fad'a maka cewa tarayya tsakanina da kai ba zai ta6a yiwuwa ba yau ma zan k'ara maimaita maka, domin kuwa na girmeka wanda nasan ban haifeka ba amma nayi k'ani da kai Haydar. Me amfanin auren da za'ayi jama'a na jiki da kuma na gefe na kushewa suna Allah wadai? Ai ana barin halal don kunya. Ka cire wannan magana a ranka ka nemi daidai kai ka aura, domin nan da sati biyu zan d'aura aure." Ta fad'i hakan wai duk don ya gane cewa baza ta iya aurenshi ba.
Wannan magana tata ta k'arshe ba k'aramin k'ona zuciyar Haydar tayi ba. Laila ta auri wani bashi ba? A zuciye ya maida dubanshi kan Ammi yana cewa,
"Ammi kinji amsarki ko? Ba wai nine bata so ba, a'a maganan da mutane zasu yi take tsoro. Sannan ki sani wallahi idan kinga kin auri wani bani ba ki tabbatar ni Haydar ba so nake miki na gaskiya ba." Yana fad'in hakan ya fice daga gidan tamkar zai tashi sama.
Idanu cike da kwalla Laila tabi bayansa da kallo tana jin d'aci a zuciyarta. Ajiyar zuciya ta sauk'e kana ta koma ta zauna kan kujeran tsugunnon tana jin jikinta babu kuzari ko kad'an.
"Ammi kiyi hak'uri amma ban san ya aka yi har Haydar ya fara tunanin aurena ba. Zan yi aure domin nima a gida an matsa mini inyi saboda zamana babu miji yasa ake mini zargin fasik'anci."
"Meyasa kika k'i yin aure har na tsawon shekaru ashirin kamar yanda Ali ya bani labari?"
Kallon Ammi Laila tayi sai taga ta yarda da ita kuma zata iya fad'a mata wani abu na daga rayuwarta.
"Ina yiwa mijina so na hak'ik'a wanda har ta kai nake tayashi kishin kaina wanda hakan shine ya hanani aure da kuma tarayya da kowanne d'a namiji. Ammi koda zanyi auren bazan auri Haydar ba domin bazan ci zamanina sannan inci nashi ba, a daa Allah yasa na cika burina na auri wanda nake so, a yanzu kuma bazan iya hakan ba domin aurena da Haydar zai jawo mini magana a cikin zuri'ata da kuma mutanen duniya. Ki bashi hak'uri ya nemi budurwa ya aura."
"Kenan da gaske ne ba Alin ne bakya so ba, maganar mutane kike gudu." Fad'in Ammi tana murmushi kad'an.
Laila bata tsammaci hakan ba, kuma a tunaninta bata yi furucin da zai nunawa Ammi cewa tana son Haydar ba.
"Ammi wannan ba gaskiya bane. Ina son Haydar amma ba soyayya ta aure ba, sannan ina shanye duk abunda yake mini ne saboda Allah ya had'a jinina da nashi."
"Kafin ki tafi bari na fad'a miki wata magana ko zaki yi amfani dashi." Fad'in Ammi ganin Laila ta tashi zata tafi a karo na biyu.
"Ina jinki Ammi." Ta furta tana mai d'aukan jakarta don ganin har magriba ya kunno kai.
"A rayuwa karki takura kanki akan maganan mutane domin duk yanda kika kai da taka tsan-tsan wani sai ya tofa albarkacin bakinsa. Idan har kina son auren Ali ni bazan hana ba kuma zan baku goyon baya d'ari bisa d'ari domin kuwa nasan zafin rabuwa da masoyi, wanda nake tunanin hakan ya faru ne da Allah ya kamani akan wasu laifuka dana aikata a baya. Sannan Alina ba shege bane idan ma kina tsoron auren wanda bashi da uba ne."
"Ammi ki bar zancen nan haka domin kuwa babu aure tsakanina da Haydar, ni abun kunya ma yake bani. Mu kwana lafiya."
"Shikenan, Allah ya had'aku da abokan zama nagari."
"Amin."
Da haka suka yi sallama Laila ta fitar da sayayyar data mata yaran unguwa suka shiga dashi cikin gidan.

RUWAN ZUMA (completed)حيث تعيش القصص. اكتشف الآن