Babi na takwas

1K 114 4
                                    


"Mas'ud bazan yi aure ba kuma bana buk'atar yi kwata-kwata. Ya zanyi Baba ya amince da wannan niyya tawa?"
  Tsayawa yayi da cin abincinsa yana kallonta cikin tausayawa, dawowanshi kenan daga University in da yake aji biyu dalilin bai samu shiga da wuri ba.
Shiru yayi domin bai san wace shawara zai bata ba a wannan karon, duk wata hanya ta zillewa Baba ya tosheta domin ya nuna cewa kawai aure yake son Laila tayi. Me zasu yi?
"Kawai ki koresu kamar yanda kike koran samarinki a daa, idan yaga babu masu zuwa ai ba zai ce ki fitar da miji ba. Tun shekarun baya nace miki mu gudu amma kika k'i, Wallahi a yau kika ce kin yarda zan zubar da karatuna in kaiki in da zaki yi rayuwar da babu takura ke da yaranki cikin kwanciyar hankali."
Shiru ta yi itama tana jin hayaniyar Abul da Sabrin a tsakar gida, dawowarsu daga makaranta kenan inda Abul mai kusan shekara takwas yake Primary 3, Sabrin mai shekara biyar ke Nursery 2.
  Sabrin ce ta fara shigowa d'akin a guje kamar yanda ta saba, Laila ta fara mata fad'a kan ta hanata shigowa babu sallama.
A nan Abul shima ya shigo bakinsa d'auke da sallama wacce Laila ta amsa bakinta d'auke da murmushi.
"Baban Babanshi, har kun dawo?" Tace dashi tana mai k'ara ganin tsantsar kamannin da yake yi da mahaifinsa.
"Mun dawo kuma yunwa nake ji sosai. Bari in je d'akin Ummii in d'auko mana abincinmu." Ya fita ba tare da ya jira me uwar zata ce ba.
Ajiyar zuciya Laila ta sauk'e ta fara taya Sabrin cire kayan makarantarta sannan ta saka mata na gida, tana gamawa yarinyar ta k'ara fita da gudu tamkar ba yanzu aka mata magana akan hakan ba.
"Yanzu Idan nayi aure wa zai rik'e yaran nan? Irin zuciya da kuma miskilancin Abul har tsoro yake bani, ga Sabrin da sam bata da nitsuwa irinta d'iya mata, Ina zan kai su? Gidan Umma zan mayar dasu ko kuma a nan gidan zan barsu alhali nasan Umma baza ta ta6a yarda da hakan ba? Tukunna ma wa zan aura cikin manemana? Duk cikinsu babu wanda zan ji dad'in zaman aurensa. Ina tsoron tashin hankali Mas'ud, bana buk'atar k'arin hakan a rayuwata, wanda nake ciki ma ya isheni."

  Bayan rasuwan Marigayi Aliyu maza suka fara kawo tayin soyayyarsu ga Laila wacce take ganinsu a matsayin mak'iyanta na ajin farko.  
   Yaushe mijinta ya rasu da har zasu zo suna neman aurenta? Shin zata ma iya soyayya bayan wacce suka yi da Aliyu uban 'yayanta? Sannan Ina zata kai 'yayanta wanda halinsu in ba ita uwarsu ba babu wanda zai iya zama dasu ba tare da anji kansu ba?
  Ana haka sai ga Nazifi ya zo wanda a tunaninta ya zo ganin yara ne kamar yanda ya saba, amma bayan ya gaisa da yaran ya aikesu su kira mamansu.
Bayan ta zo yake fad'a mata sirrin zuciyarsa na cewa yana sonta kuma zai rik'e su Abul tamkar 'yayan cikinsa da yake har lokacin Muna bata haihu ba.
  Abun haushi ya bata matuk'a, lokaci d'aya kuma taji wata muguwar tsanarsa a ranta, wai yayan Aliyu ne yake cewa zai aureta? Yayan Aliyu?
Bata furta masa a baki ba amma daga ganin fuskarta ya gane cewa bai samu kar6uwa a gunta ba.
"Nasan da wuya Iyayenki su barki zaune a haka babu aure. Ki k'arawa kanki shekara biyu zuwa uku nan gaba, nasan a nan kam ko auren dole za'a iya miki don a kawar dake daga zaman zawarci. Sai dai ki sani, kamar yanda Umma ta fad'a miki 'yayan Aliyu baza suyi agolanci ba haka nima zan k'ara jaddada miki, wallahi bazan bari kije gidan wani da yaran nan ba. Kinga kenan nine dai wanda zai cika miki burinki wato na rayuwa tare da 'yayanki ba tare da kin kai ruwa rana ba. Ina nan ina jiranki Laila har zuwa lokacin da zaki gane gaskiyar al'amari."
  Da haka ya barta tsaye tana jin wani tuk'uk'i a zuciyarta tamkar zata fashe tsabar bakin ciki.
Wato zai yi amfani da son da take yiwa su Abul domin ta yarda ta aureshi? Saboda sun ga tana son 'yayanta? Ina zata k'ara rayuwa da Umma a matsayin suruka da kuma Muna a matsayin kishiya bayan duk abunda ya faru tsakaninsu a baya? Sannan uwa uba, bata jin ko d'igon sonshi a zuciyarta sai ma tsanarshi da take yi daya iya zuwa mata da kalmar soyayya bayan mijinta ya rasu.
  Ana haka sai ga Dr Zubair wanda har yau gurinshi take kai 'yayanta idan basu da lafiya.
Kai tsaye ta fad'a masa cewa babu aure a gabanta, amma ya nuna shi yaji ya gani zai jira har lokacin da taji tana son auren. Da yake ta sayi waya, ta nan yake kiranta lokaci-lokaci suna gaisawa ba tare da ya k'ara mata maganar soyayyar ba, amma dashi da ita sun san kiran na tuni ne a akan maganarsa.
Abdul ma yana dirowa Nigeria kai tsaye ya sauk'a a gidansu Laila. Ko da ta fito tsoro ne ya kamata har ta juya da niyyar gudu amma ta tsaya da yace mata ta'aziyya yazo yi mata.
  Jiki ba kwari ta dawo suka gaisa sannan ya mata ta'aziyya tare da mik'a mata tsaraba yace a bawa 'yayansa, kuma da zarar ya huta zai dawo ya gansu.
  Tun a lokacin zuciyarta ta bata cewa shima zuwa yayi kamar sauran masu zawarcinta, don haka ta k'ulla aniyar rabuwa dashi cikin sauk'i ba tare da an samu matsala kamar na wancan lokacin ba.
  Sai dai duk magana da magiyar da Laila ta mishi Abdul bai daina zuwa gurinta ba, wani irin bak'in naci yake dashi kamar na hauka. Akwai ranar da yake fad'a mata cewa,
  "Saboda ke har yanzu nak'i yin aure Laila, Ina ji a jikina komin daren dad'ewa zaki zama matata, kiyi hak'uri ki k'ar6i tayin soyayyta a karo na biyu."
  Maimakon hakan yasa Laila taji sonshi ko kuma ta fara kulashi, sai ya kasance haushinsa taji sosai kenan ya saka a ranshi akwai ranar da Aliyu zai saketa ko kuma ya mutu domin shi ya dawo ya aureta? Wannan soyayya ce ko k'iyayya?
  Daga ranar ta daina fita gabad'aya ko da Dr Zubair ne ya zo, dalilin bata son ta yaudareshi tunda ba auren ne a gabanta ba.
Sannan yawan tsayawa dasu hiran ma zai wargaza mata tsarinta na kaucewa duk wata k'ofa na aure.

RUWAN ZUMA (completed)Where stories live. Discover now