Babi na biyu

1.7K 157 11
                                    

Aliyu ne zaune a cikin gidansu da yamma sakaliya yana cin abincin rana dalilin bai dawo gida da wuri ba sai lokacin. Hayaniya yaji a waje kamar ana kiran sunansa.
Ummansa dake masa fifita ta dakata daga abunda take yi ta rafka salati,
"Na shiga uku ni Nafisatu, me nake ji kamar mutanen Mai Tatsine ne suka dawo garin Kano. Aliyu tashi ka rufe mana k'ofa kar su shigo su yankamu." A gigice ta yi maganar tana cilli da mafificin hannunta.
Aliyu ya tashi ya nufi bakin k'ofa, a tunanin Ummanshi rufewa zai yi, amma ganin ya fita waje yasa ta yi kuwwa ta bishi babu ko mayafi a jikinta.
Dandazon samari ne suka gani kowannensu d'auke da gora suna ihu suna cewa zasu illata Aliyu, yayinda Haruna kuma ya tsaya a gabansu yana hanasu shiga gidan, kuma shi yake kiran Aliyu ya fito.
Abdul kuma da yanzu ya gane waye Aliyun da ya hurewa Laila kunne sai ya shiga tsananin mamaki da kid'ima kawai ya samu guri ya zauna yana dafe da kanshi.
"Alhamdulillah, ga Aliyun ma ya fito. Zo ka fad'a musu ba kai kake zuwa gurin budurwar Abdul ba." Cewar Haruna yana sauk'e numfashi dalilin wahalar dashi da samarin suka yi.
Aliyu ya gyara tsayuwarsa ya rik'e k'ugunsa abunda ya zame masa d'abi'a ya ce,
"Idan kuma nace nine fa?"
Umman Aliyu dake bayan d'anta tana zare idanu cikin kad'uwa ta ce,
"Aliyu me yake faruwa ne? Su waye wad'annan?" Me ka musu Aliyu?"
"Umma ki koma cikin gida kin ga ko mayafi baki dashi. Abokaina ne 'yan majalisarmu." Ya juya yana lalla6ata tamkar k'aramar yarinya.
"Kai Aliyu! Wannan ziyara tasu bata lafiya ba, dubi wancan yanda yake rik'e da mashi kamar mai shirin soke rak'umi. Me kuka zo yiwa d'ana?" Umma ta fito daga bayan Aliyu tana mai tambayarsu, a wannan karon babu tsoro a tare da ita sai tsantsar dakewa irin ta uwa mai son kare 'yayanta.
"Umma don Allah ki koma gida. Kin ga wancan sunanshi Abdul shine shugabansu, wannan Zailani, wancan kuma Sanusi...." Da haka ya kira sunan samarin kaf Umma na jinshi amma ko kad'an hakan bai kwantar mata da hankali ba. To waye bai san suna da kuma fuskar mak'iyinsa ba? Ita Aliyu zai yiwa wayo?
"Kar ka raina mini hankali mana Aliyu. Ka wuce mu koma gida ko kuma mu wuce Caji Ofis domin ban yarda da wad'annan yaran ba."
"Malama d'anki....." Wani mai suna Garzali ya fara magana, amma bai kai ga k'arisa magananshi ba Aliyu ya dakatar dashi ta hanyar daka masa tsawa, yace,
"Karka kuskura ka yiwa uwata rashin kunya. A kul d'inka."
Kana ya juyo ya dubi Yayansa Nazifi wanda shima yanzu ya fito tare da sabuwar Amaryarsa cikin tashin hankali suna tambayar ba'asi.
"Nazifi don Allah ka shigar da Umma gida, babu abunda zai faru. Magana kawai zamu yi."
Da haka Nazifi ya shigar da Umma gida bayan ya lalla6ata akan cewa zai dawo ya tsaya tare da Aliyu yaji me yake tafe dasu.
A bakin k'ofar gidan Umma ta dawo ta tsaya domin tace bata isa ta shiga gida ta bar Aliyu cikin azzalumai ba.
Sai a lokacin Aliyu ya samu nitsuwarshi ya dubi Abdul da ya samu guri ya zauna a kan wani dakali yana kallon diraman Aliyu da mahaifiyarsa.
"Abdul ya aka yi?" Kawai shine tambayar da Aliyu yayi masa, wacce tasa Abdul harzuk'owa dalilin jin laifin da Aliyu yayi masa ya dawo d'anye a zuciyarsa, ya taso yana nuna Aliyu da yatsa.
"Uban me kake zuwa yi gurin budurwar da zan aura Aliyu? Ashe dama kai munafuki ne mai fuska biyu? Abunda zaka saka mini dashi kenan? Wani shege ne a Samarin Libati bai san cewa Laila tawa bace ni kad'ai? Aliyu son Lailata kake yi?"
Umma da ke bakin k'ofa taji wani tuk'uk'in bak'in ciki ya mamayeta wato duk wannan gororin da mashin da aka zo kashe Aliyu dasu akan mace ce? Wai Laila? A take taji tsanar yarinyar a ranta tamkar taje gidansu ta tsinka mata maruka lafiyayyu.
"Wace kenan? Wai Laila kake nufi?"
"Ka fini sani Aliyu. Tukunna ma so nake inji ta bakinka cewa kai d'inne da gaske mai zuwa gurinta tace ta fasa aurena sai kai, ko dai wani ne?"
"Kafin in ce wani abu zan so ka tuna abunda ya faru a daren Mauludi sati uku da suka wuce." Cewar Aliyu yana mai fuskantarshi babu alamun tsoro a tattare dashi.
"Me ya faru?" Abdul ya tambaya cikin rashin gane in da maganarshi ta dosa.

Haruna dake gefe guda wanda tunda aka shigo unguwar shi da Hamisu abokin Abdul suka so gane abunda ke faruwa ya tuntsire da dariya har yana fad'uwa k'asa.
Abdul da har lokacin yana cikin duhu ya dubi Haruna cikin 6acin rai ya ce,
"Haruna wai me yake faruwa ne? Uwar me kake yiwa dariya? Menene ya faru sati ukun da suka wuce?"
"Kai da kanka kace babu shegen da ya isa ya je gurin Laila ya hure mata kunne, to ashe Aliyu ya je. Gashi kuma ya doke fadarka da alama kuwa sai ka sake gina wani." Ya k'ara tuntsirewa da dariya.
Abdul kama kanshi yayi da hannu biyu yana jin 6acin rai da bak'in cikinshi na fita daga zuciyarsa. Fuskarsa Idan ka kalla mamaki ne had'e da murna. Sauk'e hannayensa yayi shima yayi dariya yana nuna Aliyu da yatsa,
"Amma Aliyu ka shammaceni, yanzu kai da gaske zuwa gurin Laila ka yi don ka nuna mini iyakata? Baka kyauta mini ba, amma dai yanzu kam na gane kuskurena. Na ji, ka iya sace zuciyar 'yan mata."
Aliyu murmusawa kawai yayi yana kallon Abdul kallo mai wuyar fassara.
"Kai ku zo mu tafi, Ina da gurin zuwa." Cewar Abdul yana mai juyawa ba tare da ya k'ara sauraran komai daga bakin Aliyu ba.
Da haka samarin suka bar k'ofar gidansu Aliyu, su kuma suka koma cikin gida Ana kiraye-kirayen sallan magriba.
Umma da Nazifi dai basu zauna ba, suna tsaye kan Aliyu suna tambayarshi ainihin labarin abunda ya faru, duk da cewa sun gane duk fad'an wai akan mace ce.
"Aliyu wai bada kai ake magana ba kayi shiru ka kyalemu? Wai me ya faru ne? Wace 'yar iskar yarinyar ce take k'ok'arin sawa a kasheka a gaban idona?"
"Umma ki kwantar da hankalinki ba wani abu bane babba. Wasa ce kawai tsakaninmu." Da haka ya mik'e ya fita zuwa zauren gidan ya shiga d'akinsa ya kulle.
"Ni Nafisatu na ga ta kaina! Yau dubi yanda yarinya ta so a kashe mini d'a haka siddan bai kashe uban kowa ba. Nazifi kana ganin yaron nan ya k'i labarta mini komai ya tafi ko? Wai ya zan yi da Aliyu?"
"Umma, yanzu da zarar na yi magana anjima kad'an zan ji ba haka ba. Ke da Aliyu ai sai Allah."
A nan ya bar Umma a tsakar gidan tana bambami ita d'aya ya shige d'akin Amaryarsa.

RUWAN ZUMA (completed)Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang