Kwananta goma da dawowa gidansu amma har lokacin hankalinta na kan Abul, ko wani hali yake ciki da ya kwana biyu bai ganta ba, sai Allah.
Bacci wannan gagararta yake yi sai dai kwakwalwarta ta sakata na dole. Abinci kuwa dama ba'a maganarsa, domin tun mutuwar Aliyu ta k'aurace masa shima sai dai ta ta6a kad'an don Sabrin ta samu abunda itama zata ci.
Ta k'ara ramewa ta fige kamar ba ita ba, ga wani duhu da tayi. In ka ganta baza ka d'auka Laila bace tsabar canjawar da tayi, babu wannan jiki mai kyau d'in, babu kwalliyar sannan uwa uba, babu kwanciyar hankali sam.
Ummii tana yawan mata fad'a Idan ta ga tayi zugum tana tunani, amma da ta kwatanta halin da itama zata shiga idan makamancin hakan ya sameta sai ta daina yiwa Laila fad'a, ya dawo itace mai rarrashinta da bata baki. Son dake tsakanin uwa da d'anta ba abun wasa bane.
Baba ma dattaku ne yasa tun farko ya barwa Umma Abul ba don yaso hakan ya faru ba, saboda shi kanshi ya sani ko a musulunce Laila ce ke da hak'k'in rik'e 'yayanta ba mahaifiyar Aliyu ba.Yau tashi tayi cikin son ganin Abul, haka kawai taji hankalinta ba zai kwanta ba har sai ta ganshi, don haka tun kafin Baba ya fita ta fad'a masa zata je duboshi.
"Ki jira idan na tafi shago sai Madu ya zo ya kaiki."
Bata so haka ba domin har yau Madu in banda gaisuwanta da yake amsawa babu maganar dake shiga tsakaninsu.
"Baba da ka bari kawai mu hau abun hawa ni da Mas'ud."
"A'a baza ayi haka ba, ki shirya Madu zai zo ya d'aukeki da misalin k'arfe goma."K'arfe goma da wasu mintuna Madu ya ajiyesu ita da Mas'ud a gaban gidan Umma. Da sallamarta ta shiga gidan shiru kamar babu kowa a ciki, d'akin Umma ta nufa tana mai cewa Mas'ud ya tsaya a waje sai an masa iso.
Sallama ta k'ara yi sannan ta kutsa kai cikin d'akin. A kwance ta samu Umma tana bacci a kan gado yayin da kuma Abul ke gefenta yana numfashi da kyar. Yayi wata muguwar rama kanshi ya fito sosai yana bud'e ido a hankali yana rufewa.
Ganin mamansa yasa ya saki wata kuka wacce da kyar take fita tsabar ya galabaita. Sannan ya d'ago hannu d'aya yana mik'a mata.
Kuka ne ya kwacewa Laila tayi saurin sa hannu ta d'aukesa, sai a lokacin Umma ta farka taga Laila a kanta. Salati ta fara yi sannan ta tashi zaune tana duban Lailan dake sauk'e Abul k'asa ba tare da ta sakashi a jikinta ba.
"Ni Nafisatu me zan gani haka? Yarinya ki shigo har d'akina babu sallama sannan ki tsaya a kaina kina kuka kamar ce miki aka yi mutuwa nayi."
"Umma ki duba Abul bashi da lafiya jikinshi yayi zafi, ga kuma kashi da yayi a jikinshi. Umma me ya sameshi ya rame haka?" Laila ta tambaya tana zubar da kwalla domin ko ita ba uwarsa bace zata tausaya mishi a halin da ta ganshi a ciki.
"Kin tsaya kina tuhumata ne akan rashin lafiyar d'anki? Waye baya rashin lafiya? Kuma mak'on uwarsa da yake yi yasa ya rame har hakan ya jawo masa cuta. Kuma gashi har ya fara sabawa dani, yanzu ganinki da yayi kwana zai yi yana kuka kamar ranar da kika tafi."
Laila bata saurari Umma ba ta fita da Abul waje, Umma ta biyota da sauri tana tambayar ina zata kaishi. Sai dai ganin ta kaishi bakin band'aki yasa Umman ta tabbatar wanke masa kashin zata yi, hakan yasa ta koma cikin d'aki tana sababi ita d'aya.
Mas'ud da ya gaishe da Umma ta shareshi yaja tsaki bayan ta shige d'akinta, kana ya maida hankalinshi kan yayarsa dake kiciniyar cirewa Abul kayan jikinshi wanda ya ca6e da kashi.
Da sauri ya isa gurinta ya kunce mata goyan Sabrin sannan ya azata a bayanshi, yarinyar dake bacci ko farkawa bata yi ba taci gaba da baccinta.
"Kalti yaron nan ya rame wallahi, dubeshi sai kace bashi ke da k'iba daa ba." Mas'ud ya fad'a cikin tausayawa.
"Ba'a bashi abinci ne, kaji mini yaro da kinibibi." Suka jiyo muryar Umma daga d'aki wacce ke sauraron duk motsinsu sai dai babu wanda ya tanka mata.
"Mama tafi dani, jan biki Mama." Shine abunda Abul ke furtawa a hankali wanda Laila ce kad'ai ke jiyo sautin muryar tashi.
Kai kawai take d'aga mishi tana wanke masa kashin, ganin k'asusuwan jikinshi da tayi ne yasa ta fashe da kuka, tana gamawa ta ciro wani kayanshi dake kan igiyar shanya ta sanya mishi ta fita daga gidan da gudu rungume da d'anta.
Mas'ud da ke goye da Sabrin yayi saurin bin bayanta domin bai san hakan na cikin tsarinta na zuwa gidan ba.
Umma kuma takun sawunsu yasa ta fito da sauri har zaninta na fad'uwa ta ga babu su a tsakar gida.
Wani kuwwa ta saka wanda yasa Muna farkawa daga baccin safe da take yi ta fito a tsorice don ta d'auka gobara ne ya tashi a gidan.
Itama bin bayan Umma tayi zuwa zaure tana kwala nata kira, Umma kuma rik'e take da zani tana kiran sunan Laila tana tsine mata.
Sai dai ko hangensu bata yi ba sakamakon gudun da suka yi bana wasa bane.
Tuni mutane suka taru a k'ofar gidan suna tambayar ba'asi amma Umma sai kuka take yi tana cewa Laila tsinanniya ce.
Sai da aka kira Nazifi ya zo sannan ta fad'a masa yanda aka yi, har tana k'arin cewa Laila tunkud'eta ta yi ta fice da gudu.
Wasu laifin Laila suke gani yayinda wasu kuma ke Allah shi k'ara suna kuma goyan bayan Lailan. Saboda makwabtansu da suke amfani da katanga d'aya su suka san halin da Abul yake ciki, kullum cikin kuka yake, da dare haka zai hana kowa bacci da ihunsa yana kiran uwarsa 'Mama, Mama'. Kwana biyu ne da suka ji shiru suka shigo yiwa Umma barka wacce bata samun bacci, shine take fad'a musu ai bashi da lafiya ne sannan muryarshi ta dashe tsabar kukan da yayi.
Wani abu da basu sani ba shine Abul bai daina kukan dare ba, dashewar muryarsa yasa su basa iya jinshi amma kuma haka suke kwana a zaune shi da Umma yana kiran sunan mamanshi. Idan abun ya bata haushi sosai sai ta gaggaura masa maruka wai don yaji tsoronta ya daina kukan. Sai dai hakan baya hanashi sai ma yaci gaba, dalilin hakan yasa take baccin safe kamar matacciya wanda yasa har Laila ta shigo d'akinta bata jita ba.
أنت تقرأ
RUWAN ZUMA (completed)
عاطفيةShin wani irin kallo kake yiwa masoya biyu wad'anda akwai tazarar shekaru tsakaninsu, musamman ma in aka ce Macen ta fi Namijin yawan shekaru? Tayi wuff dashi, ko Tsoho yayi wuff da yarinya. To ga labarin wani matashin saurayi mai farin jinin 'yan...