"Tun yaushe?" Shine tambayar da Mas'ud ya yiwa Laila yana mik'a mata wayar.
Kar6a tayi tana harararsa ranta a 6ace ta koma ta zauna kan kujera tana maida numfashi a hankali.
Shima biyota yayi ya zauna kusa da ita ya zuba mata idanunshi masu kama dana Sabrin.
"Baki bani amsa ba."
D'ago ido tayi ta kalleshi kana ta d'aura k'afafunta a kan kujeran tace,
"Meyasa ka tambaya?"
"Answer me Kalti."
"Zai yi sati." Ta bashi amsa tana mai kawar da kanta gefe ganin irin kallon da yake wurgo mata na tuhuma.
"Meyasa kika fara 6oye mini sirrinki yanzu? A daa duk wani motsinki da kowanne abu daya shafi rayuwarki na sani Kalti kuma nima haka kin san nawa. Meyasa kike son 6oye mini abunda ke tsakaninki dashi? Why?" Ya tambayeta yana mai juyo da fuskarta ta kalleshi da kyau.
Had'e fuskarta tayi tamau kana tace,
"Mas'ud bani son irin haka, komai ne na rayuwata sai na fad'a maka?"
"Yes."
"Sake mini fuska kar ka 6ata mini kwalliya." Tace dashi tana harararsa kad'an.
Sake mata fuskar yayi kana ya rik'o hannunta duka biyu yanda baza ta juya mishi fuska ba yace,
"Ina jinki."
Ajiyar zuciya ta sauk'e tana dubanshi cikin ido tace,
"Baza kayi judging d'ina ba?"
"Na daina." Ya amsa mata yana murmushi kad'an.
Ganin hakan yasa itama ta sake fuskarta ta fara bashi labarin Haydar da take 6oye mishi. Ta k'arisa da cewa,
"I don't know meyasa na kasa korarsa kamar yanda nake yiwa sauran masu cewa suna son aurena. Ko don idan yayi wasu abubuwan yana tuna mini Aliyu ne? Ko dai haka kawai Allah ya had'a jininmu? Babu maganar wai ko ina sonshi Mas'ud, wallahi babu ita. Haydar ba sa'ana bane sannan ko da auren zanyi ina da zawarawa daidai shekaruna in aura. Ni dariya yake bani don shirmensa yayi yawa, shi da gaske wai aurena zai yi." Ta k'arishe maganan tana darawa.
Murmushi kawai Mas'ud yayi yana kallon yanda take walwala kamar bata da wata damuwa a rayuwarta wanda hiran Haydar kad'ai da tayi ya jawo hakan.
"Sai ki matsa masa ya fito da mata kafin lokacin yayi domin yanzu saura sati biyu biki."
"Zai yi wuya ayi auren nan dashi amma ko daga baya ne zan masa idan Allah ya nufa."
"Ko tare da naki za'ayi bikin nashi?" Fad'in Mas'ud yana karantar yanayinta.
Laila tayi d'an jimm kad'an tana tunani sannan tace,
"Idan kuma hakane bazan samu damar halartar auren nashi ba, ina dai jira ya fitar mata yayi aure kafin Alhaji Abdul ya gane halin da ake ciki ya koresa a aiki."
"Da wannan ma don wannan. Amma Kalti daga yau bana son kina 6oye mini wani abu na rayuwarki. Karki manta tun a daa tare muke sirrinmu, kuma har gobe ina son mu kasance haka."
"I promise bazan sake ba amma kaima you have to trust me cewa bana yiwa Haydar soyayya na aure, Allah ne ya had'a jininmu kuma nake taimakonsa babu gajiyawa."
"I trust you Kalti."Kwana biyu da haka Haydar ya iso gidan Laila kamar yanda ta umarcesa.
Ganin Mas'ud zaune kusa da ita yasa yaji kamar yaje ya bashi naushi, amma tunawa da yayi cewa k'aninta ne sai ya samu sauk'i a zuciyarsa.
Zama yayi a k'asa kamar kullum ya gaishesu tana tambayarshi jikin Ammi yace,
"Ta samu sauk'i sosai."
Sai dai Laila ta lura da wani kallon soyayya da yake mata idan Mas'ud baya gani wanda hakan yaso ya bata dariya amma ta tamke fuska tamkar bata gani ba.
"Ka fitar da mata?" Tambayar farko kenan da ta fara masa.
Gyad'a kai yayi ya had'a da cewa,
"Na samu."
"Wacece kuma a ina take?" Tayi masa tambayar tana rik'e numfashinta.
Kallon Mas'ud yayi yaga shima jiran amsarsa yake yi. Haydar ya had'iye yawu yace,
"Sunanta Minat a unguwarmu take amma iyayenta basu shirya aurenta nan da sati biyu ba."
Ajiyar zuciya Laila ta sauk'e wacce bata ma san ta rik'e ba, Mas'ud ya bita da ido yayi d'an murmushi ta gefen bakinsa.
"Sai yaushe kenan?"
"Zuwa wata biyar ko sama da haka, saboda basu shirya ba kuma basu da k'arfi." Ya amsa mata cikin sauri kamar wanda ya haddace maganan tun ba yau ba.
Kallon Mas'ud tayi suka yi magana ta ido kana ta juyo da dubanta ga Haydar tace,
"Shikenan, da zarar anyi auren Sabrin hankalina ya dawo jikina za'a fara naka sai ka yiwa dangin mahaifinka magana a je nemo maka aurenta."
Shiru yayi ya sadda kanshi k'asa fuskarsa ta canja zuwa bak'in ciki, kallon juna Mas'ud da Laila suka yi kana ta maida dubanta ga Haydar tace,
"Haydar lafiya dai ko?"
"Ban san su waye dangin mahaifina ba haka kuma ban san na mahaifiyata ba. Ammi kad'ai na tashi na gani a matsayin zuri'ata." Ya k'arishe maganan yana runtse idonshi kad'an domin hawayen da suka taru su koma.
Mas'ud ya mik'e tsaye yace,
"If you need me ina side d'ina." Kana ya fice ya bar musu falon.
Cikin tausayawa Laila ta dubi Haydar itama taji hawaye na taruwa a nata idon tace,
"Baka ta6a fad'a mini ba."
"Bana son yin maganar da kowa ne."
"Ka tambayi Ammi ita zata sani Haydar, duk tsawon wannan lokacin me ya hanaka tambayarta?"
"Tambayarta da nayi yasa ciwonta ya tashi har ta kwanta a asibiti. Idan kuma na k'ara matsa mata zan iya rasata alhali she is all a have."
"Ko ni zata iya fad'a mini idan naje mata da maganar aurenka?"
"Baza ta fad'a miki komai ba k'arshe ma hakan kan iya tayar mata da ciwonta. Idan ba ita taso yin maganar ba don Allah kar ki kawo mata shi."
Gyad'a kai Laila tayi tana jin zafi a k'irjinta, ashe shine dalilin da yasa bai ta6a kawo mata hiran 'yan uwanshi ba? Itama kuma sai tayi nauyin baki duk tsawon wannan lokacin bata ta6a tambayarshi ba.
Ganin har lokacin Haydar baya cikin walwala yasa Laila taji babu dad'i domin tafi sabawa da barkwancinsa ko da kuwa wani lokacin yana wuce gona da iri.
Sallamarshi tayi ya fita jiki babu kwari sannan ko d'an tsokananta da yake yi na maganar soyayyar yau bai mata ba. A nan ta gane hakan ba k'aramin cinsa yake yi a ciki ba. Waye ba zai so sanin tsatsonsa ba?
Bayan tafiyar Haydar ta kira Mas'ud ya dawo take fad'a masa wasu abubuwa da ta gani game dashi wanda a daa bata d'aukeshi a komai ba.
"Sai yanzu na gane dalilin da yasa har Ammi ta kwanta a asibiti amma babu wani d'an uwansu da yazo dubata."
"A yanda na samu labari basu da kowa sai junansu, and he was 23 suka zo wannan unguwar suka zauna. Mutanen unguwan sun ce basu san daga ina suke ba amma basu da wani mummunan hali ko wani abun kushewa."
Laila ta yiwa Mas'ud kallon tambaya ya kuma gane ya bata amsa da cewa,
"Kalti a yanda kike ji dashi I won't let him hurt you idan ya gama shiga jikinki ba, shiyasa nayi bincike a kanshi sosai. Sai dai Haydar bashi da wani mummunan hali illa rashin sanin daga ina suka fito. A nan garin yayi University har ya gama tare da abokinsa Nasir. Ina ga sauran tarihinsa na baya zai iya fad'a miki idan kika tambayeshi."
"Kana tunanin zai fad'a mini?"
"Zai fad'a miki tunda yace yana sonki."
"Mas'ud kenan. Yau kuma kaine kake fad'an hakan da bakinka?" Tayi 'yar murmushi da iyakarta fatar baki.
"Ya zan yi? Idan ma kince zaki aureshi ni bazan hanaki ba domin kuwa hakan ba haramun bane Kalti."
"You are joking right?" Ta tambayeshi cikin mamaki don bata tsammaci jin hakan daga gareshi ba.
"Komai kika yi a rayuwa zaki samu wani hakan bai mishi ba, komai da kika sani."
"Wannan ba amsa bace."
"Sannan zai yi wuya a bashi auren yarinya a garin nan matuk'ar ba'a san asalinsa ba. Kamar abun da wuya."
Da haka ya tashi ya shiga d'akinta ya d'auko mata hijabi yana cewa,
"Ki tashi mu tafi."
"Laffaya zan saka." Ta bashi amsa tana mai kar6an hijabin ta koma d'akinta dashi.
Minti biyar da haka ta fito sanye da laffaya green wanda yayi mata kyau bana wasa ba.
"Kyau kam sosai amma hijabin yafi rufe miki jiki Kalti."
"Kaima kasan nafi son laffaya akan hijabi."
Bai k'ara cewa komai ba yayi gaba ta bishi a baya suka bi Laila Beauty suka d'auki Sabrin. Daga nan kuma kasuwa suka tafi sayayyan kayan biki.
Bayan sun dawo da dare Laila ta shiga d'akin Abul ta sameshi kwance a kan gado ya rufe idonsa yana bacci.
Murmushi tayi tana ganin yanda kowacce rana yake k'ara kama da Babansa tamkar an tsaga kara. Har zata tafi ta jiyo muryarsa ya kira sunanta.
"Mama."
"Dama baka yi bacci bane?" Ta iso gaban gadonshi ta zauna tana k'ara godewa Allah da ya bata su.
"Yanzu nake shirin yi." Ya tashi zaune shima yana kallonta.
"Kwana biyu baka son cin abinci har ka rame, dubi yanda idonka ya fad'a fa. Ko dai baka da lafiya ne?" Ta ta6a goshinsa amma bata ji alamar zazza6i ba.
Cire hannun nata yayi daga goshinsa ya rik'e a nasa yace,
"Mama me ya dawo dashi gidan nan yau?"
"Ya Allah!" Ta runtse idonta kana ta bud'esu ta kalli Abul, cikin gajiyawa da maganar tace,
"Abul ba auren Haydar zan yi ba, zuwan da kaga yayi Mas'ud ne yasa in kirashi yaji ko ya tsayar da mata dalilin naso na had'a aurensa da Sabrin, amma hakan bai yiwu ba saboda iyayen yarinyar basu shirya ba. Haydar mutumin kirki ne Abul, sannan wancan abun da yayi ya bamu hak'uri ni da Mas'ud." Tayi masa wannan k'aryar don kawai hankalinsa ya kwanta.
Wani irin farin ciki ta gani kwance a fuskar Abul wanda ya sakata nishad'i har sai da hakwaranta duka bayyana.
"Mama da gaske?"
Tsaki taja cikin wasa tace,
"Ban sani ba."
Saisaita fuskarsa yayi ya zama babu wannan wasan yace,
"Ki mini alk'awarin cewa bazaki ta6a aurenshi ba."
"Abul..." Zata yi magana ya dakatar da ita da cewa,
"Just promise me Mama. Ina son hankalina ya kwanta yanda ko da gaba na ganshi a gidan nan bazan nemi karyashi ba."
"Baza ka iya fad'a da Haydar kaci nasara ba Abul." Tayi dariya kad'an cikin ganin wautarsa.
Shima d'aga kai yayi sama yana tuno siffar Haydar, yaga kuwa idan har aka bari suka yi fad'a ba k'aramin kashi zai sha ba, sai dai ko rundunar sojoji ne zai iya taransu in dai akan mamanshi ne.
"Sai yanzu nake mamakin ya aka yi ya bari Uncle Mas'ud yaja kwalar rigarsa har waje bai kwace ko yayi fighting d'inshi back ba."
Murmusawa kawai tayi bata ce kanzil ba, Abul yaci gaba da magana.
"Now promise me." Ya jefar da wancan maganan yana mik'a mata hannu don ayi sealing promise d'in.
Itama mik'a mishi nata hannun tayi tana cewa,
"I promise, amma kai har yanzu in mutum zai maka alk'awari sai yayi shaking hannunka?"
YOU ARE READING
RUWAN ZUMA (completed)
RomanceShin wani irin kallo kake yiwa masoya biyu wad'anda akwai tazarar shekaru tsakaninsu, musamman ma in aka ce Macen ta fi Namijin yawan shekaru? Tayi wuff dashi, ko Tsoho yayi wuff da yarinya. To ga labarin wani matashin saurayi mai farin jinin 'yan...