CIKAR BURI

15 0 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
       *CIKAR BURI..!*
    🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌸🌸🌸🌸
              🌸🌸
                🌸

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Bro Muhammad Karim*
*Bro Nazifi yarima*

_Bismillahir rahamanir rahim._

_Free page._

*PAGE 1*

Kaduna State.
Malali area unguwa ce ta masu hannu da shuni domin had'ad'd'un gidajen dake cikinta kad'ai zasu iya gamsar da mutum hakan,wasu k'yak'k'yawan 'yan mata ne guda biyu na hango cikin shiga ta alfarma kowaccesu tasha ado mai ban sha'awa,suna tafiya cikin salo mai jan hankali suna fira daga ganinsu kasan daga babbar makaranta suke domin hand bags ne rataye a kafad'arsu,d'ayan kuma ta rik'o wani handout a hannunta duba d'aya zakayi musu ka gano su d'in mata ne ma'abota kwalliya da wayewa saboda fuskarsu tasha had'ad'd'iyar kwalliya mai tsari da burgewa.
  Dukansu kusan tsawonsu d'aya amma akwai banbamcin yanayin sura domin Subai'a chocolate colour ce,tanada dara-daran idanu masu haske tamkar milk yayinda siririn hanci da k'aramin bakinta sune jagorar fallasa sihirtaccen k'yawonta,ta kasance mace k'yakk'yawa mai k'yawon ban mamaki sannan gata shagwab'ab'b'iya ta bugawa amujalla,yayinda k'awarta Umaiyah ta kasance black beauty wadda ubangiji ya mallaka mata k'yawon diri mai gigita k'wak'walwa tanada zazzak'ar murya mai dad'in gaske wanda idan mutum bai fahimci yanayin maganarta ba zai iya k'issima hakan amatsayin yanga wannan kuwa yana daga cikin yanayin halittar mabuwayin sarki Allah.
Subai'a da Umaiyah k'awayen juna ne tun suna nursery school suke tare amakaranta d'aya,adalilin haka ne soyayya da tsananin shak'uwa ya wanzu atsakaninsu ta yadda d'aya bazata iya yin wani abu ba sai tare da d'ayan,,tun daga suturu, islamiya komai iri d'aya ake musu saboda ganin irin k'auna da soyayyar dake wakana atsakaninsu yasa iyayensu suka zamo abokan juna ta sanadiyyar 'ya'yansu, akowane lokaci sukan ziyarci juna duk dayake suna rayu a unguwa d'aya hakan baisa sukayi fatali da k'awancensu ba,idan ka zauna da k'yau sosai kaga yadda suka shak'u tareda nunawa juna tsananin k'auna da soyayyar gaskiya bana tantanma anan gaba akwai abinda zai iya rabasu ko ya rusa wannan soyayyar ta hak'ik'a.
Basa b'oyewa juna sirrinsu duk yake ba komai Subai'a ke fad'awa Umaiyah but ita Umaiyah ta aminta da ita hundred percent,domin ayanzu Umaiyah tanada wani saurayi wanda yake mutuwar sonta mai suna Bello itama gwargwadon hali tana nuna masa k'auna azahiri.

  Bayan sun k'araso adaidai kwanar da zasu rabu Subai'a ta d'ago dara-daran idanunta tace"Besty sai yaushe zamu k'ara had'uwa kuma..?".
Umaiyah ta saki murmushi tace"Suby wannan aiba magana ce kinsan akowane lokaci burinmu mu kasance tareda juna saboda haka gobe zan zo gidanku anan zanyi breakfast..".
Subai'a ta waro idanu cikeda mamaki tace"da gaske Umy momy zata barki kiyi sammako agidanmu..?".
Umaiyah ta d'aga kafad'a tace"mi zai hana..?Bakisan yadda momyna keji dake bane shiyasa kike tantanma akan haka amma zanyi k'ok'arin ganin na kammala ayyukan gida in zo saina barwa A'isha sauran ta k'arasa..".
Subai'a ta saki numfashi tace"to shikenan Besty sai kinzo idan Bello baizo zance wurinki ba ki k'i zuwa..".
"Rufamin asiri Suby kinsan yadda momy take idan ta ganni tsaye da Bello ai kashina ya bushe wallahi kema kinsan yadda iyayenmu sukeda burin akan karatunmu basa son ganin muna kula samari..". Umaiyah ta fad'a tana fuskantar Subai'a.
Subai'a ta jinjina kai tace"haka ne Umy zolayarki fa nakeyi ai nasan momy akwai tsattsauran ra'ayi..".
"K'ya dai fad'a Besty ai ke Maminki tana miki sauk'i tunda bata cika takura miki ba..".

Subai'a tace"gaskiya Mamina tanada sauk'in kai ba kamar momy ba kema kiyi hak'uri batason karatunki ya shiriri ce ne Umy..".
Umaiyah ta had'iye wani abu azuciyarta tace"haka ne Subai'a ai shiyasa kikaga ban faye saka lamarin momy azuciyata ba domin banason damuwa da tunani su haifarmin da babbar illah arayuwata,nasan komai lokaci ne zai zo ya wuce tamkar amafarki..".
Subai'a ta rik'o hannunta d'aya cikin k'auna tace"alal hak'ik'a maganarki gaskiya ce Umaiyah babu abinda yake dawwama aduniya..".
Umaiyah ta jaye hannunta tace"Besty ya kamata mu k'arasa gida kada mu jawowa kanmu matsala..".

CIKAR BURIWhere stories live. Discover now