CIKAR BURI

1 0 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
       *CIKAR BURI..!*
    🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌸🌸🌸🌸
              🌸🌸
                🌸

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Bro Muhammad Karim*
*Bro Nazifi yarima*

_Bismillahir rahamanir rahim._

_Free page._

*PAGE 14*

Ranar Monday su Subai'a suka fara zuwa school suka fara d'aukar darasi a new level a compound d'in makarantar student's ne guda-guda suka dawo makarantar,domin a first week ba kowane d'alibai ne ke saurin dawowa school ba saboda iyayensu wasu masu kud'i ne wasu kuma masu k'arfin hali ne,shiyasa arayuwa ba dole sai anzamo d'aya ba idan kana fama da rashin lafiya wani lafiyarsa k'alau idan kanada fama da jarabtar talauci wani cikin daula yake,ubangiji mad'aukakin sarki bai tab'a rabawa dai-dai ba domin shine yake jarabtarmu ta hanyoyi iri-iri daban daban ya gani shin zamuyi hak'uri ko baza muyi ba,duk lokacin da kake cikin k'unci to ka sani dukkan k'alubalen da kake ciki bai ko taka rabin na wani ba.

Su Subai'a zaune cikin class d'insu bayan lecturer ya fita suka fara zancen zuwa cin abinci.

Subai'a ta dubi Umaiyah tace"Umy ki tashi muje restaurant mu ci abinci yunwa nakeji..".

Umaiyah tayi hamma da sauri ta saka tafin hannu ta toshe baki sannan tace"to Suby mi zai hana kije kiyo mana take away nifa akan tsabar yunwa ko gani bana yi da k'yau sosai..".

Da mamaki Subai'a ta bud'i baki tace"bakiyi breakfast bane da safe..?".

"Nayi but ban k'oshi ba na zo makaranta..".

Subai'a ta jijjiga kanta alamar gamsuwa tace"uhmm bari inje inyo mana take away kinji d'ora kanki akan desk kafin in dawo..".Tana rufe bakinta ta mik'e tsaye tareda ficewa daga cikin class d'in domin ta lura da cewar yunwa tana neman illartar da Umaiyah.

Tafiya takeyi da sassarfa anutse take yayinda dukkan gab'ob'in jikinta ke motsawa iska mai k'unshe da ni'ima sai kad'awa takeyi,tana ratsa sassan jikin bil'adama iskar ta shak'a cikeda annushuwa gab da zata shiga cikin restaurant sukayi kicib'is dasu Bello,turus taja k'afafunta ta tsaya ta fad'ad'a fuskarta da murmushi tace"ina wuninku yah Bello..?".
Atare suka k'araso wurinta suna mata kallon sani fuskokinsu ayalwace Ibrahim ya fara amsawa yace"lafiya k'alau muke Subai'a..".
"Ina k'awarki..?".Ya tambayeta a siyansance tamkar babu abinda ya faru akan abokinsa adalilinta..
Subai'a ta chanza fuska zuwa yanayin damuwa tace"tana class kwance batada lafiya..".
Bello yayi k'arfin halin cewa"ayyah Allah ubangiji ya bata lafiya..".
  "Ameen..".
Ibrahim ya saki numfashi yace"to yanzun nan mi zakiyi a restaurant k'anwata..?".

"Take away zanyi mana i think ciwon nata yanada nasaba da yunwa..".

Ibrahim ya jinjina kai murya atausashe yace"ok let's me escort you to enter in..".
"Bello wait for me here yanzun nan zan fito..".

Bello da hannayensa suke sanye cikin aljihu ya karkad'a kai yace"no problem dude you can go...".

Ibrahim da Subai'a suka rankaya cikin restaurant atare kai tsaye suka je wurin masu serving d'in food Subai'a ta fad'i irin abinda take so,aka saka abincin cikin take away aka sanya cikin leda bak'a Ibrahim shine ya biya kud'in gaba d'aya suka fito daga ciki godiya Subai'a tayiwasu Ibrahim sukace ta gaida Umaiyah kafin suzo ganin jikinta,bata kawo komai aranta ba saboda batasan abinda yake faruwa ba directly ta nufi hanyar zuwa wurin Umaiyah.
Bayan ficewarta ne Bello ya tsuke fuska yace"Ibee ya naga kana sakewa yarinyar nan fuska bayan k'awarta ta yaudareni ta nuna min halinsu na mata..!?".

CIKAR BURIWhere stories live. Discover now