CIKAR BURI

1 0 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
       *CIKAR BURI..!*
    🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌸🌸🌸🌸
              🌸🌸
                🌸

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Bro Muhammad Karim*
*Bro Nazifi yarima*

_Bismillahir rahamanir rahim._

_Free page._

*PAGE 6*

Aranar Bello jiki asab'ule cikin yanayin damuwa da fargaba ya koma gida yana dawowa gidansu kai tsaye ya fad'a cikin bathroom ya sakarwa kansa shower,ko tashin hankali da damuwar dayake ciki zata ragu bayan ya fito daga ciki ya zura kayan shan iska ajikinsa ya kwanta akan yalwataccen gadonsa,zuciyarsa sai k'una da rad'ad'i takeyi masa domin tun yanzu ya fara jin shakku akan lamarin soyayyar Babangida da Umaiyah,sai yanzu yake ganin wautarsa akan saurin amincewar da yayi da sharad'in daya gindaya masa sai yanzu yake ganin laifinsa miyasa yayi sub'utar baki yace duk wanda zai iya sace zuciyar Umaiyah ya yarje masa yaje yayi soyayya da ita,miyasa tun farko bai hango cewar Babangida zai iya yin nasara akansa ba miyasa alokacin dayake fad'ar maganar baiji fargaba da tsinkewar zuciya ba sai yanzu..?.
Kayyyyy miyasa nayi haka anyah na k'yautawa zuciyata kuwa,yanzu idan yayi nasara akaina zan iya rayuwa babu Umaiyah anyah zan iya juriyar ganin tana soyayya da wani bani ba..? Ire-iren wad'annan tambayoyi ne sukayita d'awainiyar yawo acikin k'wak'walwarsa da ruhi ya rasa wace hanya zai b'ullowa al'amarin gashi ya riga ya amince agaban abokaninsa shin ko yaje yace musu ya fasa kuma idan ya aikata hakan kima da girmanshi zai iya zubewa a idanunsu zasu dauk'eshi mai magana mai biyu.
Bello ya rasa wace irin mafita ya dace ya nemo sai juye-juye yakeyi akan gado bedsheet d'in duk ya yamutse adalilin tsabar rashin walwala irin nashi,duk da sanyin A.C dake cikin d'akinsa hakan bai hanashi yin sharkaf da gumi ba nan da nan tunaninsa ya hargitse yanayinsa ya sauya idanunsa suka chanza launi ubangiji kad'ai yasa irin azababben d'acin daya keji a k'ark'ashin ransa,yana huci ya tashi zaune tareda sanya yatsun hannu yana hargitsa sumar kansa cikin tururin ciwo azuciya yace"miyasa na yarda da sharad'in Babangida ni Bello...!?".
"Yanzu idan yayi nasarar sace zuciyar Umaiyah ya zanyi da rayuwata idan babu ita,hmmm gaskiyar zance nayi matuk'ar wautar amincewa da sharad'insa...!?".

Tagumi yayi da hannu ya rasa ina zai tsoma zuciyarsa yaji sanyi ya rasa yadda zaiyi ya rusa komai batare da sun gano yanada sa hannu acikin al'amarin ba,to ko zaije ya fad'awa Umaiyah cewar wani abokinsa zai zo wurinta da niyar soyayya kada ta amshi soyayyarsa kuma ai batasan Babangida abokinsa bane bata tab'a ganinsu tare ba balantana idan yaje tayi tunanin akwai wata mak'ark'ashiya atsakaninsu.
Ko ya tunkari Ibrahim da wannan maganar yaji wace irin shawara zai bashi wata k'ila ya samu mafitar dayake fatar samu,da wannan shawarar yaji 'yar natsuwa azuciyarsa tareda k'ara jaddadawa akan cewar bazai tab'a barin Babangida yayi nasara akanshi ba.
Hajiyarsa da taji shirun yayi yawa Bello bai fito yayi lunching ba wannan dalilin yasa taji ta kasa natsuwa hankalinta yana kan d'anta,da sassarfa ta fito daga cikin room d'inta wurin dinning table taje ta had'o lunch akan tire komai da komai ta d'auko tiren ta tunkari hanyar zuwa room d'in Bello.
Izo k'ofar da Hajiyarsa tayi ne ya dawo dashi daga duniyar tunani nan take ya dinga saukar da numfashi ahankali tamkar wanda yayi tseren gudu,wurinsa ta iso ta dire tiren agabansa tana masa kallon k'walelecewa da son gano abinda yake damunsa ganin yadda ta kafeshi da kallo yasa Bello ya wayance ya saki murmushin yak'e yace"Umma lunching d'ina kika kawomin..?".
Umma ta samu wuri nesa dashi kad'an ta zauna tace"eh Bello naga tun d'azu ka dawo amma baka nemi kaci abinci ba ko awaje kaci ne..?".

Bello ya gyad'a kai yace"a'a ai kinsan ban faye cin abincin sayarwa ba gajiya ce tasa ban nemi inci ba..".

Umma tayi murmushi irin nasu na manya tace"naji Bello yarda bata zama dole ba mi yake damunka..?".
Jin ta sako mashi tambaya yasa yaji fad'uwar gaba ya ziyarcesa cikin dakewa tamkar babu abinda yake damunsa yace"Umma babu abinda yake damuna kawai gajiya ce ta sakoni agaba..".

CIKAR BURIWhere stories live. Discover now