CIKAR BURI

1 0 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
       *CIKAR BURI..!*
    🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌸🌸🌸🌸
              🌸🌸
                🌸

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Bro Muhammad Karim*
*Bro Nazifi yarima*

_Bismillahir rahamanir rahim._

_Wannan littafi na kud'i ne mai buk'atar karantawa cikin aminci saiya turo katin MTN na 200 naira ta wannan number 08163650557,ko kuma ta wannan account number 6020308418 Keystone bank._

*PAGE 28*

Sanya hannu tayi ta jawo phone d'inta tana bud'e sak'on idanunta yayi tozali da daddad'an kalaman soyayya daga wajen Mujaheed, murmushi ne ya kasa gushewa afuskarta ta dinga maimaita karatun message d'in tanata sakin k'ayataccen murmushi wanda ke nuna alamar na jin dad'i ne,hak'ik'a sak'on ya wanke dukkan haushi da bak'in cikin dake cikin zuciyarta dangane da Mujaheed d'inta.
Tabbas ta yarda da cewar Babangida shine ragamar rayuwarta kuma ginshik'i wanda saida shi zata kasance wata aba arayuwa saboda shi so wani abu ne da baya tsufa baya k’arewa ciwo ne a
cikin zuciya wanda baya tab'a warkewa..!

Cikin salo na jan aji Subai'a ta yamutsar da fuska ahankali ta saki numfashi tace"bazan fara kulaka ba Mujaheed har sai ka k'ara sanin muhimmancin so arayuwa da darajata..".
"Da sannu zaka gane cewar komai aduniya sai an wahala ake mallakarsa..".
Ab'angaren Bello haka abin yake tun ranar da Umaiyah ta tako k'afarta tazo gidansu ta bashi hak'uri ya shareta,tun tana sa ran zai kirata awaya har ta cire tsammani domin ta sadak'ar mayuwacin abu ne ya manta da abinda ta aikata masa zama guda shiyasa Umaiyah ta fad'a cikin matsanancin hali walwala da farin ciki sukayi k'aura daga zuciyarta.
Bello shima ya yanke shawara aranshi bazai tab'a kulata ba har sai ya tabbatar da tuban gaskiya tayi bana mazuru ba.
Wata rana da kanshi yaje wurin Ibrahim ya feso masa labarin cewar Umaiyah tazo har gidansu ta nemi gafararsa,Ibrahim ya ji dad'in yadda ta nemi gafarar abokinsa batare data nuna girman kai ba yace"Bello agaskiya Umaiyah ta cancanci rangwame agunka ka manta komai ku daidaita kanku..".
"Don da wata ce zata nuna girman kai wurin neman afuwarka but dayake ta fahimci rashin k'yautawarta shiyasa ta nemi afuwa..".
Bello rausayar da kai k'asa yace"tayi k'ok'ari Ibee amma ka sani ina tunanin mutumen ya juya mata baya ne shiyasa ta nemi gabana har da cemin inyi hak'uri mu d'ora soyayyarmu daga inda muka tsaya ta maidani sakarai mara wayo..".
Ibrahim ya furta cewar"a'aa Bello karka ce haka na fad'a tun farko Umaiyah tana matuk'ar k'aunarka saboda itace ta jajirce tsayin daka wurin ganin ta inganta rayuwarka tareda saita tarbiyarka akan hanya,kaga ko anan ta tsaya ta cancanci lambar yabo da jinjina awurinka...".
Bello yace"tunda kana goyon bayanta zanyi tunani akanta in gani ko zan iya cigaba da soyayyata da ita..".
"Ka daure ka manta komai kar kayi mata butulci saboda Umaiyah mace ce wadda duk namijin daya mallaketa amatsayin mata zaiji dad'i da alfaharin kasancewarta uwar 'ya'yansa domin ta samu tarbiya ta k'warai ta fito daga gidan mutanen arzik'i..".

Bello ya safke numfashi yace"Ibrahim na karb'i shawararka zanyi tunani da dogon nazari akai..".

Ibrahim ya jijjiga kafad'a alamar shi ya sani ya mere baki yace"to ubangiji yasa kayi tunani mai k'yau..".

"Insha Allahu zanyi ai komai Umaiyah tayimin bai dace ace na juya mata baya ba saboda ubangiji ya k'addari itace silar shiryuwata...".

"Tabbas haka ne gaskiya...".

{[]}{[]}{[]}{[]}{[]}{[]}{[]}{[]}{[]}

Umaiyah ce tayi tagumi da hannu d'aya d'ayan hannunta rik'e yake da kafceciyar phone d'inta tanata trying nombar Bello tana shiga baya d'auka,ahaka A'isha tazo ta risketa cikin matsanancin hali kallo d'aya tayi mata taga kamar tanada damuwa kusa gareta tazo ta zauna ta sanya hannu ta jaye mata hannun da tayi tagumi dashi tace"Aunty Umaiyah ki daina tagumi ba k'yawo..".
Alokacin ne Umaiyah ta lura da akwai mutum kusa gareta ta saukar da gwauron numfashi tace"naji A'isha yaushe kika iso wurina ban sani ba..?".
A'isha ta musk'uta tace"taya za'ayi ki sani kina can kin fad'a duniyar tunani wai mi kika nema kika rasa arayuwarki Aunty da zaki d'orawa kanki damuwa da yawan tunani..!?".

CIKAR BURIWhere stories live. Discover now