CIKAR BURI

2 0 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
       *CIKAR BURI..!*
    🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌸🌸🌸🌸
              🌸🌸
                🌸

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Bro Muhammad Karim*
*Bro Nazifi yarima*

_Bismillahir rahamanir rahim._

_Free page._

*PAGE 10*

Mamaki kwance k'arara afuskar Falmata take kallon fuskar Umaiyah tana jinjina soyayyar data kammala tafkawa ayanzun nan cikin k'arfin hali da son sanin sirrin zuciyarta Falmata ta gyara zama tace"Umaiyah keda wa kike waya haka tamkar zaku lashe junanku akan tsabar so da k'auna..?".
"Yanayin fuskarki ya nuna cewar kina tsananin k'aunar wanda kuke waya Umaiyah ko dai Bello ne kika chanzawa suna zuwa Babangida..?".
Umaiyah ta saki k'ayataccen murmushi tace"a'aa ba Bello bane sabon saurayi ne nayi k'awata..".
Falmata ta jijjiga kai cikeda matsanancin mamaki tace"ikon rabbi ke kuwa Umaiyah yaushe kuka had'u..?".
"Sannan ya zakiyi da Bello dayake mutuwar sonki...?".
Umaiyah ta d'aga kafad'a irin ko ajikinta tace"bamu dad'e da k'ulla alak'a mai k'arfi a tsakaninmu ba maganar Bello wannan ba damuwa bace duk wanda nake so dashi zanyi rayuwar aure..!".
Falmata ta d'ora yatsarta agadon bayanta tace"haka ne but bai dace kiyiwa Bello butulci ba saboda yana mutuwar sonki arayuwarsa..".
"Naji amma kinsan so d'aya ne kamar yadda zuciya guda ce ba'a tab'a rabata gida biyu balantana in so su alokaci d'aya kuma so tsuntsu ne Falmata..".
Jijjiga kanta tayi tace"ba shakka maganarki gaskiya ce Umaiyah amma kafin ki zartar da hukunci akan Bello ki samu lokaci kiyi tunani domin bai cancanci *RASHIN SO* awurinki ba..".
"Misali idan kikayi duba da k'yau sosai kafin ki fara soyayya dashi yana aikata wasu dab'i'u marasa k'yawo amma bayan kun k'ulla soyayya mai k'arfi atsakani kika fara chanza masa akalar halayyarsa,daga d'abi'u masu muni zuwa k'yak'k'yawa dukkanin abinda kika ce baya tab'a k'etare umurninki tamkar kece kika zuk'unna kika haifeshi wannan bai isa ya gamsar dake cewar soyayyar gaskiya yakeyi miki ba...!?".
Umaiyah ta natsu tana saurarenta har ta k'arasa maganganunta tsab sannan tayi gyashi cikin damuwa tace"zanyi nazari akan maganarki Falmata..".
"Allah yasa kiyi tunanin daya kamata..".
Kiran daya shigo ne yasa da azama Umaiyah ta mik'e tsaye bayan ta amsa kiran tace"ok gani nan fitowa yanzun nan..".
Katse wayar tayi ta juyo fuskarta tace"Falmata yah Babangida yazo d'aukata fa..".
Falmata ta tashi tsaye tareda yafa mayafi ajikinta tace"to muje kiyi sallama da hajiyata sai ki wuce..".
Haka abin ya kasance saida Umaiyah tayi sallama da mahaifiyar Falmata sannan suka rankaya har wajen get anan suka taras da mota parker,har bakin motar Falmata ta rakata suka gaisa da yah Babangida Umaiyah ta shige cikin mota yayinda Falmata ta juya ta koma cikin gida.

Suna zazzaune akan kujera sai jifan juna sukeyi da kallon k'auna kowanensu ji yakeyi tamkar ya had'iye d'an uwansa adalilin tsabar k'auna da soyayyar gaskiya,dak'yar Umaiyah tayi jarumtar kauda idanunta gefe tace"yaya barka da yau..?".
Babangida da hannayensa ke kan steering yayi murmushin dake bayyana sirrin k'yawonsa yace"yauwa gimbiyata an gama hidimomin bikin ko..?".
Cikeda kunyarsa Umaiyah ta bashi da"ehhh..".
"Yanzun nan ina zamu nufa gimbiyata...?".
"Gida mana ko akwai inda kakeson muje ne..?".
"Ehh to idan har kina ra'ayin zuwa ba...".
Umaiyah ta juya fuskarta b'angare daban tace"mi zai hana...".
Babangida bai sake magana ba ya tada motar suka d'auki hanyar zuwa wani irin katafaren super market.
Acan sukaje yayi mata uban sayayya masu tsada ya biya kud'i sannan ya kaita gidansu bayan ya fitar mata kayayyakin ta shige gida,shi kuma yaja motarsa ya d'auki hanyar zuwa cikin gari.

[[[[[]]]]][[[[]]]][[[]]]]][[[[]]]][[[]]]

*BAYAN SATI D'AYA*
Soyayyarsu Umaiyah ta k'ara habb'aka ta yadda bazasu tab'a iya rayuwa ba idan babu juna ba, dukkan abinda yah Babangida yasan tana so shi yake k'ok'arin aiwatarwa tuni ya sace mata zuciya wurin k'yautatawa uwa uba ga iya furta kalamai masu sanyaya zuciya da saka natsuwa aruhi, ayanzu Umaiyah ta rage kad'aici da damuwar rashin k'awarta Subai'a saboda Babangida ya maye mata gurbin kowa aranta bata tab'a damuwa idan Bello bai kirata saboda k'aunar da takeyi masa ta rage tasiri azuciyarta Babangida kawai ne cikar burin zuciyarta.

CIKAR BURIWhere stories live. Discover now