CIKAR BURI

1 0 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
       *CIKAR BURI..!*
    🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌸🌸🌸🌸
              🌸🌸
                🌸

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Bro Muhammad Karim*
*Bro Nazifi yarima*

_Bismillahir rahamanir rahim._

_Wannan littafi na kud'i ne mai buk'atar karantawa cikin aminci saiya turo katin MTN na 200 naira ta wannan number 08163650557,ko kuma ta wannan account number 6020308418 Keystone bank._

*PAGE 26*

Ta dad'e tana k'issima maganganu cikin k'ok'on zuciyarta tareda jinjinawa lamarin Babangida da soyayya tayi masa kamun kazar kuku ya rasa farin ciki arayuwarsa,ya zamo dole ta rarrashesa domin kada ya jefa rayuwarsa cikin k'unci da had'ari ta silar wadda yake so ya kamu da mugun ciwo.
Kauda tunaninta tayi gefe d'aya ta fuskancesa ido da ido cikin tausayawa tace"Babangida wa cece wannan da har tayi nasarar gigita k'wak'walwa da zuciyar k'anena..?".
"Wa ce mai sa'ar ce ta iya shiga cikin zuciyarka ta hana maka jin dad'i da walwala arayuwa..?".
Babangida ya kalli fuskar Aunty Sharifah da manyan idanuwanshi murya asanyaye cikin tattausan lafazi yace"hajiya zan fad'a miki ko wa cece amma kiyimin uzuri har mu daidaita atsakaninmu tareda warware matsalolin da suka kunno kai idan komai ya daidaita zan sanar miki ko wa cece..".
Jinjina kai Aunty Sharifah tayi tana sakin k'ayataccen murmushi tace"ok ubangiji yasa komai ya daidaita Bro but ka rage yawan damuwa kaji dukkanin abinda ubangiji mad'aukakin sarki ya tsaro zaka samu saika sameshi arayuwarka..".
"Saboda haka kabi komai ahankali cikin natsuwa..".
Babangida ya gyad'a kai cikin gamsuwa da ladabi yace"insha Allahu zan bi komai atsanake hajiya Aunty ubangiji yayi mana maganin abinda bamu iya yiwa kanmu..".

Aunty Sharifah ta musk'uta tace"Ameen kaje dinning table kaci abinci kowa yaci abinci agidan nan banda kai shiyasa akowane lokaci baka tab'a k'iba..".
Murmushi yayi kad'an yace"hajiya kenan karki damu idan na samu kwanciyar hankali zanyi k'iba harda k'aton tumbi..".Ya k'arasa maganarsa azolaye yana dariya ciki-ciki.

Aunty Sharifah ta bintsire baki cikin rashin yarda da zancensa tace"kaine zakayi k'iba da k'aton tumbi da ko anyi ruwa harda k'ank'ara..".
Mik'ewa tsaye yayi yace"lallai zaki kuwa gani nan gaba idan nayi aure zaki tabbatar zanyi k'iba mai k'yau ta natsuwa da kwanciyar hankali..".

"Naji je dai kaci abinci babu wani son zance salon ka shiririce don kada kaci abincin...".
Babangida ya k'arasa wurin dinning table yaja kujera ya zauna akai yace"ohhh ni Bangis na shiga uku tunda bana son yawan cin abinci dashi akeyimin gori akowane lokaci banida hutu..".
"Eh anyi maka idan baka son ayi maka magana kayi zuciya ka dinga cin abinci akodayaushe..".
Babangida ya wanke hannu yayi bisimillah ya fara cin abincin atsanake bai k'ara kulata ba ganin ya fara cin abinci yasa Aunty Sharifah taja baki ta tsuke maida hankalinta tayi kacokam akan Indian film d'in da take kallo.

[[∆]][[∆]][[∆]][[∆]][[∆]][[∆]]

Bello Muhammad da Ibrahim suna zazzaune akan cushion cikin gidansu Bello suna kallon wasan ball da akeyi tsakanin Manchester da Liverpool,sun maida hankalinsu kacokam akan TV.
Hannu Ibrahim ya zura ya d'auki remote control ya rage volume d'in TV ya dubi Bello yace"Bello kanada labarin mutuniyarka..?".

Bello hankalinsa na akan ball yace"wa ce mutuniyar tawa kake nufi..?".

"Kanada wata mutuniyar ne bayan Umaiyah sarauniyar zuciyarka..?".

Nisawa ahankali yayi Bello ya tab'e baki yace"hmm banida labarinta saboda har yanzun nan duniya batayi mata karatun ta natsu ba..".

Ibrahim ya tsiyaya lemun dake gabansu cikin kofi ya kurb'a kad'an sannan yace"a'a baka iya kasan cewar duniya bata koya mata hankali domin yanzu bakwa tare shawarar da zan baka itace duk lokacin da ta dawo wurinka don neman gafara da sulhu to ka yafe mata awuce wurin domin ko Babangida na fahimci cewar yayi laushi da yawa abinda ya aikata maka yayi nadamarsa..".

Shek'ek'e Bello ya kalli Ibrahim cikeda rashin yarda ranshi a b'ace yace"ta ya kasan cewar sunyi matuk'ar nadama Ibee ko ka fara chanzawa ne...?".
Ibrahim ya girgiza kai yace"ko d'aya ban chanza daga ainahin yadda ka sani ba abokina..".
"Hmm naji ubangiji yasa haka ne..".

CIKAR BURIWhere stories live. Discover now