CIKAR BURI

1 0 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
       *CIKAR BURI..!*
    🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌸🌸🌸🌸
              🌸🌸
                🌸

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Bro Muhammad Karim*
*Bro Nazifi yarima*

_Bismillahir rahamanir rahim._

_Free page._

*PAGE 11*

Sun dad'e sosai suna firarsu atsanake tamkar babu abinda yake damun Bello azuciyarsa ahalin a k'ok'on ranshi ji yakeyi yana tafarfasa da k'una!Domin ayadda Umaiyah ta tarbeshi ya lura da cewar wani yana k'ok'arin shiga atsakaninsu saboda bata nuna kad'uwa da farin ciki wurin ganinshi ba,duk da yayi mata 'yan tambayoyi amsa baisa ta fad'a masa gaskiyar abinda yake mak'ale cikin zuciyarta ba,tun anan zuciyarsa ta fara rawa akanta daurewa kawai yakeyi har suka kammala firarsu yayi mata sallama ransa adagule yayi gida ita kuma ta juya ta fad'a cikin gida.

Bello tafe yake kansa sunkuye a k'asa yana tunanin chanzawar yanayinta alokaci d'aya baisan miyasa ta kasa sakin jiki dashi ba kamar alokuttan baya ba,anyah Babangida baiyi nasarar wargaza soyayyar dake tsakaninsa da Umaiyah ba anyah bai shiga ya fita ba ya fatattaki soyayyarsa azuciyar Umaiyah ba..?Idan ko da gaske ne shine silar tarwatsewar farin cikinsa babu shakka Babangida ya zamo babban maci amana kuma k'aton munafuki!Tabbas zan nuna masa shi k'aramin k'waro ne wallahi tunda yake neman shigemin hanci bazai tab'a samun farin ciki aduniyarsa ba.
Haka Bello ya dinga tafiya yana zancen zuci har ya k'araso cikin d'akinsa directly room d'insa ya shiga ciki ya cire tufafinsa ya koma daga shi sai singlet da gajeren wando,pillow ya jawo ya d'ora kanshi akai fuskarsa tana kallon ceiling yana tunanin chanzawar Umaiyah da kuma cika bakin da yayi agabansu Jabir yana kod'a Umaiyah akan baza tab'a iya soyayya da wani ba,ganin yadda tunaninta ke neman yi masa lahani arayuwa cikeda matuk'ar dauriya Bello ya mik'e tsaye jalabiyarsa ya d'auko ya zura ya zari key d'in motarsa.
Wurin mai gyaran waya ya nufa domin ya duba masa lafiyar wayarsa bayan yaje mai gyaran yayi iyakar bincike akan matsalarta but ya gano batada wani matsala,bai b'oyewa Bello ba yace masa wayarsa lafiyarta k'alau ko zai sayar masa da ita ne nan take ya yarda ya sayar masa da wayar bayan ya cire sim cards da memorynsa mai gyaran ya chake masa kud'insa Bello yaje shagon sayarda wayoyi ya siyo waya sabuwa dal cikin kwalinta.

{{{}}}{{{}}}{{{}}}{{{}}}{{{}}}{{}}

*BAYAN KWANA SHIDA*
Rayuwarsu Subai'a agarin Gwandu tana tafiya yadda ya dace domin ayanzu sun riga sun saba da rayuwar garin yanayin yadda mutanen garin ke tafiyar da tsarin rayuwarsu abin yana matuƙar burgesu da basu sha'awa,saboda wata rana haka kawai suke fitowa suna yawo agari suna ziyarar gonaki,lambu,wurin wasannin gargajiya suna zuwa kallo suna jin nishad'i azuk'atansu.
Garin ya k'unshi hausawa,fulani,zabarmawa,kabawa da sauran yaruka na mutanen Kebbi.
Tafiya sukayi mai tsawo har suka k'araso k'ark'ashin iccen mangwaro suka ja suka tsaya domin sun ni'imantu da inuwar mangwaron,Subai'a tana rik'e da doguwar sanda a hannunta ta kalli yayanta Shamsudeen tace"yaya mangwaro nake son sha..".
Shamsudeen ya d'aga kai sama yana k'arewa iccen mangwaron kallo da nazari can ya maida hankalinsa gareta yace"bari mu huta sai muje kasuwa in siya miki...".

Yakune fuska tayi kamar zata fashe da kuka tace"banason na kasuwa na wannan iccen mangwaron nake so..".

Cikin lallami Shamsudeen yace"Subai'a mi zakiyi da wannan mangwaron d'anye...?".

Rau rau da idanu tayi cikeda shagwab'a tace"sha zan yi yayah..".

Shamsudeen ya jijjiga mata kai yace"is okay bari in tsinko miki guda kar kiyi kuka kinji mik'omin sandar dake hannunki..".
Subai'a ta mik'a masa doguwar sandar ya amsa da ita yayi amfani ya tsinko mangwaro d'anyu guda biyu ya mik'a mata ta dinga wasar baki tace"nagode yayanah..".
Shamsudeen ya shafi kanta yace"bakida damuwa k'anwata..".
Jan hannunta yayi suka tunkari hanyar zuwa kasuwa suna k'arasowa tsakiyar filin kasuwa suka dinga ganin cinciridon mutane suna zuwa sayen kayayyakin masarufi da ababen more rayuwa,tsarin kasuwar gwanin burgewa domin masu saida dabbobi b'angarensu daban masu sayarda atamfofi da shaddodi ga shagoginsu nan ajere,masu saida kayayyakin miya suma suna gefensu mahauta suna b'angarensu suna aikin gyarar nama atsanake da dai sauran 'yan kasuwa.

CIKAR BURIWhere stories live. Discover now