CIKAR BURI

1 0 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
       *CIKAR BURI..!*
    🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌸🌸🌸🌸
              🌸🌸
                🌸

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Bro Muhammad Karim*
*Bro Nazifi yarima*

_Bismillahir rahamanir rahim._

_Wannan littafin na kud'i ne mai buk'atar karantawa cikin aminci saiya turo katin MTN na 200 naira ta wannan number 08163650557,ko kuma ta wannan account number 6020308418 Keystone bank._

*PAGE 17*

Koda Mai keke napep ya ajiye Subai'a abakin get d'in gidansu duk ta jik'a fuskarta sharkaf da ruwan hawaye da majina, shasshekar kuka kawai takeyi ranta sai zafi yakeyi mata.!
Mai keke napep d'in da yaga yanayin da take ciki bayan ta biyashi kud'insa ya kalleta cikin tausayawa murya araunane yace"hajiya kiyi hak'uri ki daina kuka komai yayi zafi maganinsa Allah..!".
Subai'a bata tanka masa ba taja k'afafunta ta shige cikin gida Mai keke napep ya rausayar da wuya cikin alhini da tsantsar damuwa yace"ubangiji ya yaye miki damuwarki hajiya..".Rufe bakisa keda wuya yaja napep d'in ya k'ara gaba.
Directly Subai'a ta shigo tsakiyar parlour ahargitse cikeda tsananin b'acin rai da tururin bak'in ciki dak'yar take ganin abinda yake gabanta,domin yanar dubu-duhu take gani cikin k'wayar idanunta adalilin tsabar takaici da tsantsar k'unci babu kowa aparlour kai tsaye tahau upstairs dazai sadata da k'ofar d'akinta,tana iza k'ofar d'aki ta isa da gudu saman gado ta kwanta rigiggine rusar kukanta kawai takeyi tamkar numfashinta zai cire daga cikin gangar jikinta.
Ta dad'e sosai tana shan kukanta idanuwanta duk sun chanza launi kuma sun kumbura sosai muryarta ta dashe,tabbas idan abinda idanuwanta sukayi tozali dashi gaskiya ne to Mujaheed ya ci amanar soyayya ya kuma tarwatsa zuciya da duk wani farin ciki nata,duniyar taji ta fice mata arai gaba d'aya gwamma mutuwa da irin wannan k'alubalen rayuwar daya kunno kai a yanzu..!
Bayan tayi kukanta har ta gaji sannan ta lalibo phone d'inta ta fara neman nombar Abdulhakeem babban abokin Mujaheed idanu rufe zuciyarta sai suya takeyi mata,wayar tana fara ringing Abdulhakeem dake zaune akan gado yana danna laptop yaji wayarsa ta fara tsuwa, akasalance ya zura hannu ya d'auko wayar ganin sunan Subai'a b'aro-b'aro akan screen baisa ya kawo komai aransa ba yayi receiving call d'inta cikin sigar zolaya yace"Assalamu Alaiki ya sahibar Mujaheed..".
Maimaikon wannan maganar ya sanyaya zuciyar Subai'a sai ma ya k'ara hassasa wutar bak'in ciki azuciyarta ji tayi kamar ta shak'o wuyan Abdulhakeem idan yana agabanta saboda zarginta yafi karkata akan cewar yanada masaniyar komai.
Cikin dasasshiyar murya tace"kada ka k'ara kirana da sahibar Mujaheed Abdulhakeem..!".
Cikin mad'aukakin mamaki Abdulhakeem ya jaye wayar akan kunne sannan daga baya ya maidata a kunne yace"subahanillah..! Subai'a wai mi yake faruwa ne ko kunyi fad'a ne da Mujaheed ban sani ba..!?".
Atsawace Subai'a ta d'aga murya sosai tace"dakata Abdulhakeem..!Kada ka nemi ka rainamin da hankali ai duk wani munafurci da k'ulle-k'ullen da Mujaheed yakeyi kanada masaniyar komai saboda haka kaje can ka nemi wadda zaku dinga yiwa wasa da zuciya..!".
Abdulhakeem yaji hankalinsa ya tashi cikin wani irin yanayi yace"Subai'a maganar cin mutunci ta wuce ya kamata kafin ki furta kalma kisan irin maganganun daya dace ki gayamin domin ni bansan munafurcin da mukayi miki nida Mujaheed ba..!".
"Eh mana dole ka fad'i haka saboda bakinka d'aya dashi..".
"Ki natsu ki daina sakin kalamai masu zafi azuciya ki fad'amin laifin da mukayi miki..?".
Alokacin ne Subai'a ta sassauta murya cikeda haushin ganin Mujaheed da Umaiyah a d'azu tace"Abdulhakeem yau da mukaje walimar Fatima bayan an tashi daga walima akan idanuwana yazo ya d'auki k'awata Umaiyah da motarsa,nayi matuk'ar mamakin wannan rikitaccen al'amarin daya kasance arayuwata shin Mujaheed baisan cewar Umaiyah babbar aminiyata bace tun muna yara k'anana atare muka ta so..?".
Jin takai k'arshen maganarta nan da nan fuskar Abdulhakeem ta bayyanar da tsantsar tashin hankali gabansa ya buga da k'arfi..! Dak'yar ya iya had'a kalmomin dazai kare abokinsa yace"kiyi hak'uri Subai'a ina ganin Mujaheed ya taimaketa ne adalilin ta kasance k'awarki kuma unguwarku d'aya but miyasa bakiyi masa magana ba da kika ganshi tareda ita...?".
  Subai'a ta mere baki tana harararshi kamar tana gabanshi cikin hargowa tace"ai nasan bazaka tab'a ganin laifin abokinka ba saboda sai hali yaxo d'aya akeyin abota kuma ka sani abokinka ya cuceni ya cuci yarda da amincewar da nayi masa saboda haka ka gaya mashi nagode sosai da nashi irin salon soyayyar daya nunamin tabbas ya zalunci zuciyar data amince masa tareda bashi babban matsayi agurbinta saboda haka ka fad'a masa ban yafe ba sai ubangiji yayimin sakayyar cutar da zuciyata da yayi..!".
Abdulhakeem ya kad'u da sauraren irin kalamai masu muni dake fitowa daga cikin bakin Subai'a bakinsa yana rawa yace"subahanillah..! Subai'a abin har yakai kiyiwa Mujaheed Allah ya isa..!?".
Hawaye masu zafi suna zirarowa afuskarta cikin k'unar rai tace"abin yama wuce yadda kake tsammani Abdulhakeem..".
Abdulhakeem ya marairaice kamar zaiyi kuka yace"kiyi hak'uri zanyi masa magana inji dalilin dayasa ya d'auko Umaiyah..".
Subai'a ta girgiza kai alamar a'a tace"bana buk'atar kayi masa magana domin neman maslaha atsakaninmu saboda yanzu zuciyata cike take taff da takaicin yaudarar da Mujaheed yayimin bana sa ran akwai wata kalmar da zai fad'amin wadda zatasa in k'ara yarda dashi..!".
"A'a karki yanke hukunci cikin fushi Subai'a tana iya yiyuwa babu komai atsakaninsu..".
"Wannan kuma ya rage naku maciya amanar so masu wasa da zuciyar 'yan mata..!".
"Naji dai ki kwantar da hankalinki insha Allahu komai zai zamo daidai..".
Saboda haushin maganganun da Abdulhakeem ya cikata dasu yasa ta katse wayar k'it yayinda shi kuma ya cigaba da bata hak'uri sai daga baya ne ya ankara da cewar ta katse wayarta.
Hannunsa ya d'ora akai cikeda matsanancin fargaba da tsinkewar zuciya ya dinga jijjiga kai yana cewa"ina lillahi wa inna ilaihirraji'una..!Ta faru ta k'are anyiwa mai dame d'aya sata yanzu bari in shirya inje gidansu Mujaheed domin in sanar masa abinda yake faruwa..". K'arasa maganarsa keda wuya ya chanza tufafi daga shadda zuwa k'ananan kaya phone d'insa kawai ya d'auka ya fice daga cikin d'akin.

CIKAR BURIWhere stories live. Discover now