CIKAR BURI

4 0 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
       *CIKAR BURI..!*
    🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌸🌸🌸🌸
              🌸🌸
                🌸

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Bro Muhammad Karim*
*Bro Nazifi yarima*

_Bismillahir rahamanir rahim._

_Free page._

*PAGE 3*

Ibrahim ya saki wani irin murmushi mai bayyanar da hak'ora yace"bayin Allah bakwa maida martanin magana ne..?".
"Ko azumin magana kuke yi..?".
Sai alokacin ne Subai'a ta saisaita kanta tace"muna yi bawan Allah saidai bamu tab'a cin karo da fuskokinku ba sai yau..".
Ibee yaja numfashi yace"ta iya yiyuwa haka ne k'anwata..".
Subai'a ta bintsire baki tace"haka ne yaya..".
"Kafin maganarmu tayi nisa ya dace ku bamu damar zama sister..".Inji Ibee yana kallon fuskar Subai'a.
Batare data kawo komai aranta tace"I'm so sorry ga wurin nan ku zauna..".
Benchin dake kusa dasu Ibee ya jawo sukayi masauki akai shida Bello dayake satar kallon fuskar Umaiyah dake faman dannar phone d'inta tamkar bata lura dasu ba.
Musk'utawa Ibee yayi yace"bari in fara gabatar miki da kaina sunana Ibrahim Khamis wannan abokina ne Bello Muhammad muna karanta physics ahalin yanzu muna three hundred level 300L..".
Subai'a ta jijjiga kanta alamar gamsuwa tace"ok i understand..".
"To tunda na gabatar miki da kanmu yanzu ke muke sauraro ki fad'a mana sunanki dana k'awarki..".
Saida Subai'a ta kalli fuskar Umaiyah taga ta tamk'e fuska alamar batason yawan surutu kauda kai tayi tamkar bata gane nufinta ba ta fuskanci Ibrahim tace"sunana Subai'a Hussaini wannan (ta nuna Umaiyah)sunanta Umaiyah Nuhu muna karanta Accounting ayanzu muna 100Level...".
Jin sunan sahibarsa yasa Bello ya lumshe idanu cikeda tsananin farin ciki da tsantsar nishad'i alokacin ne ya k'ara kafeta da tsumammun idanunsa yana kallonta babu ko k'iftawa.
"Wow!Sunaye masu dad'i..".
"Mun gode..".
Ibee ya saki numfashi yace"k'anwata akwai wata magana mai muhimmanci da zanyi dake zan so ki bani aron hankalinki..".
Subai'a ta jinjina kai tace"ba damuwa yaya ina saurarenka..".
"Da farko dai ina son k'anwarki itama ta saurari abinda zai fito daga bakina domin maganar ta shafeta..".
Subai'a ta dubi fuskar Umaiyah data k'ara tsuke fuska tace"Umy kinji abinda yace ki bamu aron hankalinki please..".
Batare data d'ago fuskarta ba tace"ina jinsa..".
"Umaiyah wannan sak'o ne daga zuciyar abokina Bello zuwa ga zuciyarki tun kwanakin baya daya fara ganinki ubangiji ya d'ora masa k'aunarki azuciyarsa shiyasa muka zo nan domin ya fayyace miki sirrin zuciyarsa wata k'ila idan da rabo kin karb'i soyayyarsa hannu bibbiyu...".
Umaiyah ta d'ago idanunta tana lece baki tace"ina abokin naka yake..?".
Ibee ya nuna Bello yace"gashi agabanki..".
Sau d'aya ta kalli gefen da Bello yake ta kauda kai saboda bazata iya jimirin kallonsa ba tace"shi bayada bakin magana ne da bazai iya furta kalmar so agareni ba..?".
"To kaji abinda gimbiyarka tace sai ka fad'a mata da bakinka Bello..".
Sai alokacin ne Bello ya samu sararin magana duk yake yana fargabar kada tak'i amsar soyayyarsa gyara muryarsa yayi yace"Umaiyahhh..".
Umaiyah ta nisa tace"na'am..".Saboda yadda ya kiran sunanta abakinsa tamkar shine ya rad'a mata sunan domin ya iya kiran sunan yadda ya dace.
"Da farko kamar yadda abokina ya fad'a miki gaskiya ne tun lokacin da idanuwana sukayi tozali da k'yakk'yawar fuskarki barci ya k'auracemin natsuwa ta gushe azuciyata,na rasa mi yakeyimin dad'i aduniya domin soyayyarki ba k'aramin kamu tayimin ba..".
"Saboda haka kada ki d'auka wasa nakeyi miki har azuciya ina k'aunarki ina fatar ki zamo abokiyar rayuwata da fatar zaki amince dani amatsayin masoyi wanda nan gaba kad'an zai zamo uban 'ya'yanki..".
Umaiyah da Subai'a shiru sukayi suna sauraron kalamansa kowaccesu da abinda take sak'awa aranta domin ba k'arya kalaman Bello sun d'aure jijiyoyin jikinsu tareda haifar musu rashin kuzari.
Dak'yar Umaiyah ta iya cewa"okay ba matsala ka bani kwana biyu zanyi tunani da dogon nazari akan maganarka..".

CIKAR BURIWhere stories live. Discover now