CIKAR BURI

1 0 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
       *CIKAR BURI..!*
    🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌸🌸🌸🌸
              🌸🌸
                🌸

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Bro Muhammad Karim*
*Bro Nazifi yarima*

_Bismillahir rahamanir rahim._

_Wannan littafi na kud'i ne mai buk'atar karantawa cikin aminci saiya turo katin MTN na 200 naira ta wannan number 08163650557,ko kuma ta wannan account number 6020308418 Keystone bank._

*PAGE 25*

Tana wucewa Babangida ya saki nannauyar ajiyar zuciya cikin zafin zuciya da tsantsar bak'in cikin dake nuk'urk'usar zuciyarsa yatsa ya d'ora a baki yana d'aga kai sama alamar tunani,can abubuwan da suka faru tun daga had'uwarsa da Subai'a har zuwa Umaiyah suka dinga haskowa cikin k'wak'walwarsa nadamar yaudarar Subai'a ne ya yawaita aransa nan take jikinsa yayi lak'was tamkar k'ank'ara.
Tabbas ya hak'ik'ance alhakin cin amanar Subai'a ne ke bibiyarsa da kuma Bello daya mato akan soyayyar Umaiyah ya shiga ya fita ya rabasu, ayanzun nan ya gano ya aikata laifi mai girman gaske ya aikata babban kuskuren da bazai tab'a gogewa a k'ok'on zuciyarsa ba har sai yaje ya nemi gafararsu Bello,ya k'udurta aranshi zaiyi k'ok'arin ganin na gana dasu tareda wanke laifina awurinsu ko rikitattun al'amurran dake tunkaro rayuwarsa zasu ragu.
Jiki asab'ule ya mik'e tsaye ya tattara phone da laptop d'insa daya zo da ita yana wani bincike akan wani aiki da mijin Aunty Sharifah ya d'orashi akai wato Alhaji Bashir,phone ya zura cikin aljihu yayinda laptop ya rungume abarsa a k'irji cikin tafiyarsa ta k'asaita ya iso wurin motarsa key ya zura ya bud'e k'ofar motar ya ajiye laptop akan kujera mai zaman banza sannan ya zagaya b'angaren driver seat ya zauna akan kujera sannan ya tada motar directly ya d'auki hanyar zuwa gida.

{{}}{{}}{{}}{{}}{{}}{{}}{{}}{{}}

Aparking lot Babangida ya parker motar ya fito d'auke da laptop ahannunsa dayake ranar weekend ne ya hangosu Nasreen da k'anenta suna guje-guje atsakiyar compound,hangoshi da sukayi ne suka shek'o da gudu suka rungumeshi cikin jin dad'i wata irin ratsatsiyar k'auna da soyayyar d'iyan Auntynsa ya dirar masa azuciya cikin dabara ya rungumesu d'aya bayan d'aya yana sakin murmushi afuska daga k'arshe ya rik'o hannun Waleeda sauran suka biyoshi rututuuuuu sunata sakin surutunsu wanda baya tab'a k'arewa.
Suna isowa tsakiyar parlourn suka iske Aunty Sharifah zaune tana hutawa masauki yayi akan cushion su Nasreen suka tattaushe masa k'afafu ya dinga cije baki yana shan k'amshi.
Aunty Sharifah ta kalli su Nasreen da suka wani irin k'ank'ame masa jiki tace"Nasreen ja hannunsu Waleeda kuje d'aki kubar uncle ya huta ya gaji sosai..".
Nasreen dakeda wayo ta dubi mahaifiyarta tace"Mom zamu bar uncle ya huta murnar ganinsa mukeyi shiyasa muka mak'ale masa ajiki..".
Abdul ya logaye wuya ashagwab'e yace"ni kam ina tareda uncle d'ina jiransa zanyi har yayi wanka yayimin story-story...".
Waleeda k'aramarsu wadda bata iya magana sosai ba cikin hausarta mara kan gado tace"yima iya son shitoyi (nima ina son story)..".
Harararta Abdulgafar yayi yace"ji ta dan Allah Anti Nasreen ko magana bata iya sosai ba amma take wani cewa tana son story-story..".Ya karkace wuya tareda koyon muryar Waleeda yana dariya..
Waleeda ta chuno baki agaba kamar zata fashe da kuka idanunta akan uncle Babangida tace"ancle chaza yah Abdul ko (uncle kaga yah Abdu)..?".
Cikin gargad'i da jan kunne Babangida ya kalli fuskar Abdulgafar yace"Abdul ka rabuda ita bana son neman magana..!".
"Sorry uncle..".
Numfashi ya safke cikeda son hutawa yace"oyah go to your room my children i need to rest..".
Babu b'ata lokaci Nasreen taja hannunsu Waleeda suka bar parlourn aguje kowanensu na son fara isa cikin tsakiyar d'akin domin yayiwa d'an uwansa gwalo..

Ficewarsu keda Babangida ya d'ora kanshi akan hannun cushion yana safke ajiyar zuciya da numfashin takaici Aunty Sharifah kallonsa kawai takeyi zuciyarta na fad'a mata akwai abinda ke damun k'anenta can tace"Babangida mi yake damunka..?".
Cikin basarwa Babangida yace"ba komai hajiya Aunty gajiya ce..".
"Gajiya ce zata saka kayi kwance kamar mara lafiya..".
"Hmm ki yarda dani Aunty Sharifah babu abinda yake damuna na fad'a miki gajiya ce..".

CIKAR BURIWhere stories live. Discover now