CIKAR BURI

3 0 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
       *CIKAR BURI..!*
    🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌸🌸🌸🌸
              🌸🌸
                🌸

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Bro Muhammad Karim*
*Bro Nazifi yarima*

_Bismillahir rahamanir rahim._

_Wannan littafi na kud'i ne mai buk'atar karantawa cikin aminci saiya turo katin MTN na 200 ta wannan number 08163650557,ko kuma ta wannan account number 6020308418 Keystone bank._

*PAGE 20*

Subai'a natsuwa tayi tana sauraron nasihar yayanta agareta yayinda takejin rauni azuciyarta sassan jikinta duk sunyi lak'was,fara'ar fuskarta ta ragu duk da tasan cewar gaskiya ne yake gaya mata amma bata ji dad'in yadda bai nuna damuwarsa k'iri k'iri akan yanayin da take ciki ba,ya dad'e sosai yana karantar abinda ke k'unshe cikin zuciyarta ya gano bata ji dad'in zancensa ba.
Cikeda tausayinta ya tallabo fuskarta cikin k'auna yace"nasan zuciyarki tana kwankwanto ne akaina saboda ban nuna damuwata a bayyane ba..!". Subai'a ta kauda kai gefe tana kallon wani b'angare tace"a'a yah Shamsudeen..".
Girgiza kanshi yayi alamar rashin yarda da maganarta murya atausashe cikin hikima da tsara lafazi mai sanyaya rai yace"k'anwata ki sani yayanki ya damu da damuwarki fiyeda tsammaninki amma banason in fad'i kalamai masu zafi da harzuk'a zuciya wad'anda zasu k'ara zafafa miki rai da hassasa wutar gaba tsakaninki da Umaiyah ta cancanci rangwame awurinki koba komai kunyi zaman amana da mutunci..!".
Subai'a ta mere baki cikin son basar da zancen tace"kaine kasan haka yayah Umaiyah batasan mi ake kira da amana ba saboda idan tasan haka alokacin dana kirata nake k'ok'arin lurar da ita cewar Babangida munafuki ne cimin mutunci tayi..".
"Kiyi mata uzuri Subai'a rashin sani ne wanda yafi dare duhu..".
Subai'a taja numfashi tace"aduniya babu alfarmar da zaka nema awurina face ka samu domin kai d'in tamkar mahaifi kake awurina idan su Abba basa raye saboda haka nayi mata uzuri da lamuni komai ya wuce agurinah..".
Cikin jin dad'in kalamanta yah Shamsudeen ya rik'o tafin hannunta cikin nashi yace"shiyasa nake alfahari dake domin ke ta musamman ce awurinah..".
"Fad'ar muhimmancinka agareni yah Shamsudeen b'ata lokaci ne saboda dazan tashi tun safe har zuwa dare in dinga fad'a maka matsayinka awurina to tabbas zamu kai tsawon lokaci bamu k'arasa muhimmiyar maganar ba..".
Lakato hancinta yayi yana sakin murmushi afuska yace"kayyyyy k'anwata badai iya tsara zance ba a ina kika koyo iya magana haka..?".
Azolaye Subai'a ta murmusa kad'an tace"awurin yayanah..".

Harararta da wasa yayi yace mata"zan cire miki idanu kin rainani ko..?".

"Idan ka cire idanun da wane iri zan kalleka inji dad'i azuciyata..?".

"Da zuciyarki...".

Cikin mad'aukakin mamaki Subai'a ta jaye jikinta anashi tace"ita zuciya tana gani ne alhalin babu k'wayar idanuwana atattare dani..?".

Shamsudeen ya jijjiga kansa cikin shauk'in k'aunarta yace"k'warai kuwa zuciya tana gani domin kuwa da itace makafi ke gane matansu,'ya'yansu da dukkanin wad'anda suke mu'amala dasu shiyasa hausawa ke cewa hankali ke gani ba ido ba..".
Rik'e baki Subai'a tayi tace"hmmm ikon Allah kenan..".
"Yafi gaban mamaki..".
Atare suka k'yalk'yale da dariya cikeda nishad'i da tsantsar shak'uwa sai kace d'azu ba cikin damuwa yazo ya taradda Subai'a ba,amma asanadiyyar iya lafuzza masu sanyaya zuciya da ruhi har yayi nasarar mantar da ita yanayin da take ciki...

((()))((()))((()))((()))((()))()

*WA NENE BABANGIDA*
Babangida asalin sunanshi na gaskiya Mujaheed d'a ne ga Alhaji Hassan da hajiya Amina asalinsu 'yan jahar kebbi ne acikin wani gari da ake kira Fana,su Babangida su kusan shida ne awurin mahaifansu Aunty Sharifah,Aunty Hindatu,Bashir, Babangida,Ridwan,sai Auta Isma'il shi Mujaheed yaci sunan kakanshi ne na wurin mahaifi shiyasa ake kiransa da suna Babangida,mahaifinsa yayi aikin gwamnati na tsawon shekaru talatin daga baya yayi retire suka tarkato suka dawo garinsu yayinda Aunty Sharifah ke auren hamshak'in d'an boko kuma d'an kasuwa mai suna Basheer,bayan aurenta ne mahaifin Babangida ya hannuntashi awurin mijin yayarsa rayuwarsa ta koma can Kaduna itama Aunty Hindatu anan garinsu ta auri miji mai rufin asiri da wadatar zuci.
Rayuwar ahlinsu rayuwa ce ta k'auna da soyayya domin bayan mahaifiyarsu babansu bai k'ara aure ba su kad'ai suke yin rayuwarsu cikin kwanciyar hankali da wadata,kasancewar kansu a had'e yake shiyasa idan wata lalura ta kunnowa kai atsakaninsu suke kashewa su binne babu mai sanin sirrinsu, wannan hali nasu yana burge wasu daga cikin mak'wabtansu yayinda wasunsu suke k'ebewa gefe suna zund'e da gulma akan cewar basu tab'a barin aga wallensu ba.
Babangida tun yana k'arami ya taso cikin gata da kulawa awurin iyayensa shiyasa ya kasance sangartacce kuma shagwab'ab'b'e,idan yana magana agaban mahaifiyarsa abin sai ya baka matuk'ar mamaki yadda zai dingayi mata shagwab'a ita kuma sai riritashi takeyi tana biye masa tamkar shine autanta tabbas ubangiji shike d'ora soyayya da k'auna a zuk'atan bayinsa but soyayyar da iyayen Babangida ke nuna masa yafi gaban kwatance saboda kamar shi kad'ai ne suka haifa wannan dalilin ne yasa wasu daga cikinsu Bashir suke kishinsa.
Koda yake yabon gwani ya zama dole duk da Babangida ya taso cikin rayuwar ilimi da wayewa ya kasance nagartacce mai tsananin biyayya da hak'uri ga bin umurnin iyayensa,dukkan abinda iyayensa suka ce yayi ko yayi masa dad'i ko baiyi ba baya tab'a d'aga kai yace a'a bazai yi ba sannan dukkanin abinda yasan zai dad'ad'a ya faranta musu rai shi yakeyi dayake yasan ciwon kanshi har sana'a yakeyi yana samun kud'ad'en dazai dinga rufawa kanshi asiri.

CIKAR BURIWhere stories live. Discover now