CIKAR BURI

1 0 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
       *CIKAR BURI..!*
    🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌸🌸🌸🌸
              🌸🌸
                🌸

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Bro Muhammad Karim*
*Bro Nazifi yarima*

_Bismillahir rahamanir rahim._

_Free page._

*PAGE 15*

Suna kammala cin abinci akan dinning table su Abba ne suka fara mimmik'ewa tsaye suka rankayo suka dawo cikin parlour,sannan yah Shamsudeen yabi bayansu Subai'a itace ta k'arshe domin dama ta dakata ne har kowa ya gama cin abincin alokacin ne zata d'auki tiren abincin da kulolin takai cikin kitchen ta wawwakesu tass ta adanasu inda ya dace.
Saida ta tsabtace hannayenta da sabulu mai k'amshi sosai ta d'ora a famfon dake cikin kitchen sannan ta fito daga ciki ta iso tsakiyar parlourn,kai tsaye wurin yayanta Shamsudeen ta isa ta zauna tana turo baki agaba tana wani irin langwab'e wuya adole ita shagwab'ab'b'iya ta zauna cikeda k'auna yah Shamsudeen ya fuskanceta fuska d'auke da fara'a yace"k'anwata ya akayi ne..?".

Subai'a ta karkace wuya kamar k'aramar yarinya tace"yah Shamsudeen sabuwar phone nakeson ka siyomin..".

Kallonta yayi cikin k'auna ya murmusa yace"wace iri kike so k'anwata..?".

Subai'a ta d'aga kai sama alamar tunani ganin tayi shiru bata fad'i sunan wayar da take so ba yasa yah Shamsudeen ya tab'o kafad'arta ta dawo cikin natsuwarta yace"kinyi shiru baki fad'i irin wadda kike so ba..".
Subai'a ta numfasa tace"duk irin wadda ka siyo zanyi godiya da farin ciki azuciyata..".
Shamsudeen ya musk'uta yana jujjuya maganar aransa yace"shikenan tunda kin bani zab'i k'anwata da yardar Allah yayanki zanyi k'ok'arin ganin ya faranta miki tareda tarairayarki tamkar k'wai..".
Cikin jin dad'i Subai'a ta rufe baki tana sakin k'ayataccen murmushi tace"godiya nake yah Shamsudeen..".

Shamsudeen ya jaye mata hannu abaki yana jijjiga kai yace"ki daina yimin godiya Subai'a ke d'in ta musamman ce awurin yayanki dukkanin farin ciki da gatanki ya rataya awuyana..".
"Tabbas haka ne yayanah..".
Su Mami dake hakimce akan cushion suna tattaunawa atsakaninsu basu lura da maganar dake wakana atsakanin 'ya'yansu ba domin yadda suke nunawa junansu k'auna,soyayya, shak'uwa abin yana matuƙar burgesu saboda sunyi matuk'ar imani da cewar ko basu raye yah Shamsudeen zai kula da tarbiya da rayuwar k'anwarsa.

[{}][{}][{}][{}][{}][{}][{}][{}][{}]

Wata rana Subai'a ta fad'a cikin kitchen tana k'ok'arin ta sarrafa girkin tarbon habibinta Mujaheed,saboda tun shekaranjiya ya sanar da ita zai zo gidansu zance ita kuma shine ta dinga zumud'i ta k'agu ranar yau ta tazo.
Tana tsaye k'yam tana motsa miya k'amshin girkinta duk ya karad'e gidan baki d'aya yah Shamsudeen dake kwance akan cushion k'amshin sai bugar masa hanci yakeyi,lumshe fararen idanunsa yayi ya saukar da numfashi ahankali ahankali ya mik'e tsaye ya tunkari hanyar kitchen.
Isowarsa keda wuya ya tsaya bakin k'ofar kitchen yana kallon bayan Subai'a tareda sakin murmushinsa mai d'auke da fara'a yace"k'anwata girki akeyi mana..?".

Babu zato ta jiyo muryar yayanta a gaggauce Subai'a ta waigo idanunta ya sauka akansa kallon k'auna tayi masa tace"yah Shamsudeen wannan girkin na musamman ne bana gida bane..".
Murmushi ya koma saki akaro na biyu yace"ai kuwa ina kishi da wanda akeyiwa wannan girki na musamman domin alamu sun nuna cewar ya fini babban matsayi a k'ok'on zuciyar k'anwata..".

Firfito da idanu waje Subai'a tayi tace"rufamin asiri yayanah har akwai wanda zai taka koda rabin matsayinka ne azuciyata bale kayi tunanin ya zartaka?Yah Shamsudeen baki yayi kad'an wurin fallasa babban tagomashi da matsayin daka taka a muhallin rayuwata..!".
"Kai abin bugun gaba ne da alfahari awurin kowace k'anwa matsayinka aguna ya zarce tunani ko a iya misaltashi bana tantanma akanka zan iya alfahari agaban ko waye kasancewarka d'an uwan jini agareni..!".

CIKAR BURIWhere stories live. Discover now