CIKAR BURI

1 0 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
       *CIKAR BURI..!*
    🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌸🌸🌸🌸
              🌸🌸
                🌸

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Bro Muhammad Karim*
*Bro Nazifi yarima*

_Bismillahir rahamanir rahim._

_Wannan littafin na kud'i ne mai buk'atar karantawa cikin aminci saiya turo katin MTN na 200 naira ta wannan number 08163650557,ko kuma ta wannan account number 6020308418 Keystone bank._

*PAGE 24*

Kamar yadda yah Shamsudeen ya fad'a haka al'amarin ya kasance washe gari da safe bayan sunyi breakfast,suka d'auki ratsattsen wanka mai shigar rai da d'aukar ido yah Shamsudeen ya sanya wani irin had'ad'd'en yadi mai azababben tsada dark pink yaji aiki hularsa da aikin sunyi daidai ya kawo agogo rolex ya d'aura a tsintsiyar hannunsa sannan ya feshe jikinsa da turarurka masu k'amshi,Subai'a atamfa ta saka ash and light blue colour mayafi da handbag d'inta light blue colour ta zura flat shoe light blue colour saida taje ta sanarwa mahaifiyarta hajiya Mabarukah inda zataje sannan ta wuce parking lot koda ta k'araso yah Shamsudeen yana kwance akan kujerar mota,zagayawa tayi gefen driver seat ta bud'e k'ofa ta shiga ciki ta zauna akai.
Murya atausashe yace mata"Subai'a anya kinyi niyar fitowa daga ciki..?".
Idanunta akansa Subai'a tace"saboda mi kayimin wannan tambayar yayah..?".
Shamsudeen ya mere baki yace"saboda naga kin dad'e da fitowa daga bathroom but kwalliyarki ta d'auki kusan one hour kina yinta...".
Murmushi Subai'a ta saki tace"kayyyyy yayah one hour fa kace sai kace kwalliyar biki..?".
"Waya sani ko bikin zakije idan na maidoki gida..'.
"A'a babu inda zanje..".
"Okay...".
Tada motar yah Shamsudeen yayi suka fice daga cikin harabar gidan gaba d'aya.

{££}{££}{££}{££}{££}{££}

Suna k'arasowa bakin katafaren shagon saida wayoyi yah Shamsudeen ya parker motarsa agaban shagon,shi ya fara fitowa daga ciki sannan ya juya b'angaren da Subai'a take yaje ya bud'e mata k'ofar ta fito suka rankaya cikin shagon.
Suna shiga aka kawo musu wayoyi kala-kala domin ta zab'i wadda take so saida ta kalli dukansu sannan ta zab'i Infinix S5 dubu arba'in da shida sabuwa fil cikin kwalinta aka sanya musu cikin leda mai d'auke da tambarin sunan shagon suka fito daga ciki.

Abakin k'ofar shagon sukayi kicib'is da Falmata k'awarsu Subai'a suna ganin juna suka ja sukayi tsattsaye Falmata ta gaida yah Shamsudeen ya amsa cikin sakin fuska ya k'arasa wurin mota ya basu wuri domin suji dad'in zantawa.
Falmata ta jawo hannun Subai'a suka rakub'e gefe ta rik'e baki tace"Subai'a ashe ana ganinki..?".
Subai'a ta kalleta cikin zolaya tace"idan ba'a ganina ke zaki ganni ne..?".
Falmata ta bintsire baki cikin iyayi tace"bakida kirki k'awata wai ace kin dawo daga Gwandu daga ke har Umaiyah aka kasa wadda zata gayamin cewar kina cikin Kaduna ai wannan bayi bane..".
Subai'a ta saki numfashi tace"Falmata kiyi hak'uri nasan ban k'yauta ba da ban sanar miki cewar na dawo ba kiyimin uzuri kinji kaina bisa wuya..".
Falmata ta jinjina kai tace"ok ba damuwa yaushe zaki kawomin ziyara..?".
Subai'a ta d'aga kai sama alamar tunani can ta saki ajiyar zuciya tace"ki bani kwana biyu zan zo gidanku..".
Falmata tace"to shikenan ina dubin hanyarki ki cika alk'awari kar fa ki b'atamin lokaci...".
"Zan zamo mai cika alk'awari Falmata..".
"Idan kin koma gida ki gaidamin Mami da Umaiyah..".

"Zasuji...".

"Bari in k'arasa ciki sai gani na biyu...".

"To k'awar kirki..".

Falmata ta juya ta shige cikin katafaren shagon yayinda Subai'a ta iso wurin yayanta Shamsudeen ta bud'e k'ofar motar ta shiga ciki,zaunawarta keda wuya yah Shamsudeen ya tada motar tareda saitata saman kwalta sun fara tafiya kenan shiru kakeji sansanyar iska mai dad'in gaske sai kad'awa takeyi tana shigowa cikin motar kad'an kad'an can taji ya sako mata tambaya idanunsa akan titi yace"Subai'a wa cece wannan da kika tsaya da ita kuna magana..?".

CIKAR BURIWhere stories live. Discover now