CIKAR BURI

1 0 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
       *CIKAR BURI..!*
    🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌸🌸🌸🌸
              🌸🌸
                🌸

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Bro Muhammad Karim*
*Bro Nazifi yarima*

_Bismillahir rahamanir rahim._

_Wannan littafi na kud'i ne mai buk'atar karantawa cikin aminci saiya turo katin MTN na 200 naira ta wannan number 08163650557,ko kuma ta wannan account number 6020308418 Keystone bank._

*PAGE 23*

Tun ranar da yah Shamsudeen ya zaunar da Subai'a yayi mata wa'azi da nasihohi akan zamantakewar rayuwar duniya,ya zamana ta daina zaman k'unci da kad'aici arayuwarta kullum cikin dare take tashi takai kukanta ga mad'aukakin sarki akan ya zab'a mata abinda yafi zama alkhairi aduniyarta da rayuwarta,dayake dukkanin abinda bawa ya fawwalawa ubangiji to koda yana cikin k'unci da damuwa ubangiji yakan sauk'ak'e masa damuwarsa ya yassare masa buk'atunsa cikin sauk'i batare da wahala ba,ni shaida ce akan haka duk wanda yake cikin damuwa ya daure yana tashi tsakiyar dare yana kai kukanshi ga Allah da izinin rabbi komai zai zamo tarihi tamkar bai tab'a faruwa ba,saboda alokuttan da mutane suke barci alokacin ne ubangiji mabuwayin sarki ke saukowa daga kan al'arshi yana cewa ina mai neman buk'ata ya rok'eni in amsa masa idan kanada rabo matuk'ar kayi addu'a za'a amsheta idan kuma kaga abin bai yiyu ba to wannan abu ba alkhairi bane arayuwarka kuma akwai babban tanadi da ubangiji yayi maka sai anan gaba zaka fahimci hakan.
Sau da yawa muna lura da la'akarin cewar rayuwa duniya batada tabbas kuma ba dawwamammiya bace,babu ta yadda za'ayi akowane lokaci ka tsinci kanka cikin farin ciki, bak'in ciki,jin dad'i,k'unci, arzik'i,talauci da sauransu dole wata rana ajarabceka da wad'annan abubuwan idan kayi hak'uri alal hak'ik'a zaka ga sakamakon Alkhairi arayuwa don babu yadda zai kasance don ka taso cikin rayuwar daula ka dawwama cikinta har k'arshen numfashi,sannan ba yadda zai kasance don kana fama da k'uncin talauci ka dawwama cikinsa har mutuwa ta yiyu farkonka ka taso cikin arzik'i k'arshenka ka talauce ko farkonka ka taso cikin rayuwar talauci k'arshenka ubangiji ya d'aukaka ka zamo hamshak'in mai arzik'i wannan yana daga cikin kudira ta ubangiji mad'aukakin sarki.

Saboda haka ina shawaratar 'yan uwana maza da mata muyi taka-tsan-tsan da duniya mu sani cewa duk yadda kake cikin tsanani da hali na rashi wani yana can zaune bayada ko abinda zai ci ayau.

(((())))(((())))(((())))(((())))

*BAYAN SATI BIYU*
Agidansu Umaiyah suna zazzaune cikin parlour ana fira cikin nishad'i da kwanciyar hankali Momy na kusa ga mijinta Alhaji Nuhu,Umaiyah da bata fiye saka baki cikin firarsu ba tana nan tana k'issima kitumurmurar da zata k'ullawa Subai'a wurin iyayenta ko zata huce takaicinta da takeji azuciyarta A'isha tana hankalceta da ita saidai batasan mi take k'ullawa ba.
Bayan ta gama tsara abinda ya dace ta fad'a domin tasan Momynta tayi mata kashedi da sanya mata dokar kula samari har sai ta kammala karatu ta langwab'e kai cikin yanayin bak'in ciki tace"daddy Momy inada magana daku..".

Gaba d'ayansu suka karkato hankalinsu gareta suka ce"muna saurarenki daughter..".

A'isha ta d'ago kai idanunta suka sark'e cikin nata tana mata alama da ido mi zata fad'a musu..? Umaiyah tayi tamkar bata fahimci abinda take nufi ba ta kauda kai ta fuskanci iyayenta tace"daddy Momy dama dalilin dayasa kukaga akwanakin baya ina k'unshewa cikin d'aki sukuni da walwala suka k'auracemin arayuwa farin ciki yayi hijara daga cikin zuciyata wannan yanada nasaba da...............".Har zata fad'a musu gaskiyar abinda yake faruwa sai kuma ta kasa k'arasa maganarta adalilin tsabar fargaba da zullumin dake kai mata farmaki akowane lungu na sassan jiki da zuciya.

CIKAR BURIWhere stories live. Discover now