CIKAR BURI

3 0 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
       *CIKAR BURI..!*
    🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌸🌸🌸🌸
              🌸🌸
                🌸

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Bro Muhammad Karim*
*Bro Nazifi yarima*

_Bismillahir rahamanir rahim._

_Wannan littafi na kud'i ne mai buk'atar karantawa cikin aminci saiya turo katin MTN na 200 ta wannan number 08163650557,ko kuma ta wannan account number 6020308418 Keystone bank._

*PAGE 19*

Ganin yadda A'isha ta shiga cikin matsanancin tashin hankali tareda nuna damuwarta yasa jikin Umaiyah ya gauraye da sanyi wata irin ratsatsiyar kasala ce ta dirar mata a k'ofofin jiki,kallon k'wayar idanun A'isha kawai takeyi tana hango damuwa da tsantsar tashin hankali k'arara acikinsu miyau ta had'a mai k'unshe da narkakken d'aci dak'yar ta iya had'a kalmomi wurin ganin ta kwantarwa 'yar uwarta da hankali tace"kiyi hak'uri A'isha bazan iya fad'a miki ainahin abinda ya rabani da Bello ba sai nan gaba kad'an..".
A'isha tayi murmushin yak'e tace"saboda mi..?".
"Ko don baki yarda dani ba baki yarda cewar ni d'in mai iya rik'e miki sirrin zuciyarki bace Aunty..!?".
Jikin Umaiyah ya k'ara mutuwa hannayenta ta had'a da nata tareda marairaice fuska cikin sigar rarrashi tace"ki fahimceni 'yar uwata ko d'aya bana tab'a tunanin zaki iya fallasa sirrina ga wasu kawai dai dalilin dayasa nace miki haka zuciyata ayanzu tana cikin zafi da tararrabin rabuwa da cikar burinta..!".
"Tabbas arayuwa kowane d'an Adam ubangiji yakan jarabcesa ta hanyoyi daban daban domin ya gwada imaninsa ko zaiyi hak'uri nayi imani ni tawa k'addarar ce tazo ahaka..!".
A'isha ta saki guntun murmushi tana jujjuya maganar a kwanyarta tace"shikenan Aunty nayi miki uzuri da lamuni har sai lokacin da zuciyarki zata rage k'una da rad'ad'i amma na rok'eki ba domin ni ba sai don iyayenmu ki rage yawan damuwa da kad'aicewa cikin d'aki saboda hakan da kikeyi baya yiwa iyayenmu dad'i matuk'a azuciya kina k'ara karya musu zuk'ata ne..".
"Sannan dukkanin abinda ubangiji ya jarrabi bawa daidai ne hak'uri da addu'a shine ya kamaceki saboda komai yayi zafi maganinsa Allah..".
Umaiyah ta murmusa cikin jinjinawa wayo da iya kalamai na A'isha tace"never mind sister da yardar Allah zan dinga jurewa ina b'oye damuwata agabansu Momy saboda bana fatar damuwata ta shafi d'aya daga cikinku domin ku ne rayuwata..!".
"Kamar yadda yake kece rayuwata Aunty Umaiyah bana jurar ganin b'acin ranki ko na rana d'aya ne saboda ke ce kad'ai nake kallo amatsayin 'yar uwata ta jini inji dad'i da alfaharin zamowarmu tushe d'aya..!".
Umaiyah ta jaye hannayenta tace"ki kwantar da hankalinki komai ya wuce k'anwata..".
A'isha ta saki k'ayataccen murmushi na murnar ganin Umaiyah ta fara sakewa da ita ta langwab'e wuya a shagwab'e tace"idan ko haka ne ina son in tabbatar..".
"Mi kike buk'ata inyi yanzun nan wanda zaisa ki tabbatar..?".
"Uhmmm yanzu yanzun nan na kammala girki abinci na jajjare komai a dinning table ki fito muje mu ci abinci taredasu daddy hakan nasan zai iya faranta musu zuciya..".
Umaiyah ta jinjina kai fuska asake tace"muje wannan ba damuwa bace..".
Babu b'ata lokaci A'isha ta sak'alo hannunta cikin na Umaiyah zuciyarta wasai na jin dad'in tayi nasarar shawo kan Umaiyah zata shiga cikinsu aci abinci,koda suka iso tsakiyar parlourn su daddy har sun babbaje akan kujerun dake k'awace wurin dinning table,suna ganin A'isha tareda Umaiyah zuk'atansu suka cika fal da tsananin farin ciki da mamakin yadda tayi nasarar lallaso 'yar uwarta.

  Cikin mad'aukakin farin ciki da nishad'i A'isha ta mik'e tsaye tayi serving d'insu abinci bayan ta gama ne ta zuba nata,kowa yaja plate ya fara bawa ciki hak'k'insa atsanake shiru ne ya gifta bakajin k'arar komai saina TV stand.

{{}}{{}}{{}}{{}}{{}}{{}}{{}}{{}}{}

Ab'angaren Bello kuma tuntuni ya dage da yawan rok'on ubangiji Allah ya sassauta masa soyayyar Umaiyah acikin k'ok'on ranshi,dayake addu'a takobin mumini ce damuwarsa ta ragu sosai domin yana gudanar da rayuwarsa cikin jin dad'i da walwala yayinda k'aunar da yakeyiwa Umaiyah tana nan daram manne cikin zuciyarsa,yayi addu'a yayi addu'a but ina soyayyarta sai k'ara ruruwa takeyi a muhallin rayuwarsa wanda ya hak'ik'ance cewar babu mai rabashi da k'aunarta face mutuwa.
Tabbas hausawa sunyi gaskiya da suke cewa da yawa masoya na rabuwa saboda tilasci daga wajen mahaifan
d'aya daga cikinsu,ban ta6a ganin inda aka raba hanta da jini ba kuma aka rayu ba.Babu sauran numfashi daga ranar da zuciya ta daina amsar
jini daga cikin gangar jiki,kamar yadda yake babu sauran farinciki daga ranar da aka raba uwa da d'anta.Rayuwa ta zamo mai k'unci agareni daga ranar da akara bani
da ke,miyasa akeson tarwatsa rayuwata da hargitsa k'wak'walwata tunda sauran k'urciyana,miyasa ake son rusa dukkan wani tanadin dana dad'e ina yi maki don k'yautata
rayuwarki?Zan iya jurewa duk k'addara amma banda ta rasa ki.Har yanzu ina kallonki ne amatsayin matata har gobe zuciyata na muradinki,kuma rayuwata ta ginu ne don samar da
farinciki saboda tarayyar soyayyarmu,yanzu aka rabamu mi nene
makomar rayuwarmu..!?..

CIKAR BURIWhere stories live. Discover now