CIKAR BURI

9 0 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
       *CIKAR BURI..!*
    🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌸🌸🌸🌸
              🌸🌸
                🌸

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Bro Muhammad Karim*
*Bro Nazifi yarima*

_Bismillahir rahamanir rahim._

_Free page._

*PAGE 8*

Tun daga wannan ranar Momy da A'isha basa tab'a barin Umaiyah ta k'unshe d'aki ita kad'ai akowane lokaci tana taredasu,idan Momy bata nan A'isha tana kusa da ita wannan dalilin yasa tun bata saba ba ta fara sabo da rashin Subai'a aduniyarta duk dayake akullum Bello zai kirata awaya ya tsumata da kalaman soyayya masu ratsa jini da b'argon jiki hakan bazai haifar mata da komai ba illah takaici,saboda akwanakin nan batasan ko mi yake damunta ba haka kawai takejin haushin Bello azuciyarta wanda ta rasa dalilin dayasa takejin haka agame dashi.
Ita kanta mamakin sauyawar kanta takeyi domin Bello baiyi mata laifin komai ba balantana tayi masa hukunci akan laifinsa.

  Ab'angaren Babangida kuwa yana nan yana tsare-tsaren yadda zaiyi nasarar sace zuciyar Umaiyah daga Bello,shi kad'ai yake k'unshewa cikin tamfatseten room d'insa ya k'issima maganganun daya kamata yayi mata idan yaje gidan idan kuma da mahaifiyarta ya ci karo ya riga ya tanadi irin kalaman dazai furta mata batare da an samu akasi ba.
  Shi kad'ai ne yake zarya a cikin dak'insa yana tunanin hanya mafi sauk'i da zaiyi saurin tozali da Umaiyah batare da Momynta taga laifinsa ba,sai jijjiga kai yakeyi yana k'issima yadda zai b'ullowa al'amarin azuciyarsa can ya saki nannauyar ajiyar zuciya yana sakin killer smile ma'ana kenan ya samu mafitar data dace wadda yake ganin zata kaishi ga kundin nasara akan soyayyar Umaiyah.

************************

Umaiyah ce zaune tana charting da Subai'a awayarta sai sakin murmushi takeyi akan fuskarta,yayinda A'isha take zaune gefenta tana hankalce da duk wani motsin Auntynta,ganin murmushin Umaiyah ya kasa gushewa yasa A'isha tayi gyaran murya tace"Aunty Umaiyah da wa kike charting..?".

Batare data d'ago fuskarta ba tace"mi kika gani A'isha..?".

"Naga tun lokacin da Aunty Subai'a tabar garin nan kike cikin k'unci da rashin sakewa ban tab'a ganin kin saki jikinki kina murmushi irin yau ba, shiyasa abin ya bani matuk'ar mamaki na tambayeki da wa kike charting..".
Umaiyah tace"hmmm A'isha ba dai sa ido ba to da Bestyna nake charting..".
A'isha ta saki guntun murmushi tace"kina nufin Aunty Subai'a ce kike charting da ita..?".

"Ehhhh..".

"To dan Allah ki isarmin da sak'on gaisuwata zuwa gareta da yah Shamsudeen..".

"Sak'onki zai isa k'anwata...".

"Godiya nake babbar Aunty..".

¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶

*BAYAN KWANA UKU*
Har ilah yau Babangida saida ya sake komawa majalisarsu ya fad'awa abokaninsa yau zaije wurin Umaiyah,nan take yanayin fuskar Bello ta sauya wani irin narkakken d'aci da bak'in ciki ne ya mak'ale masa a mak'ogwaro amma gudun kada ya nuna gazawarsa da tsoro yasa yace su Abba subi bayan Babangida idan zaije wurin Umaiyah domin a gasgata yaje ko baije ba,dukansu sun yarda da wannan maganar haka dai suka cigaba da firarsu atsanake tamkar babu wani agreement atsakaninsu.

Zuwa wani lokaci kad'an suka fara watsewa suna tafiya gidajen iyayensu Babangida ma yayi haramar tafiya gida su Abba suka biyo bayansa har ya isa gidansu yayi wanka ya chanza tufafinsa,koda ya fito baiga su Jabir ba girgiza kai yayi yana sakin k'ayataccen murmushi sannan ya tunkari hanyar zuwa gidansu Umaiyah cikin tafiyarsa ta mazantaka da yanga wannan yanayin halittarsa ce idan baka sani ba zaka iya cewa girman kai ne yasa yake chanza salon tafiya.
Isowarshi keda wuya bakin get d'in gidansu Umaiyah ya shiga cikin harabar gidan dayake ba bak'o bane shiyasa maigadi bai tsayardashi ba,gaisawa atsakaninsu sukayi ya k'ara gaba yayinda su Jabir suke biye dashi tamkar sun ga mai laifi,bayan sun kawo bakin get suka gaida maigadi ya amsa musu cikin sakin fuska tambayarsu yayi daga ina suka ce masa tareda Babangida,jin haka yasa maigadi ya basu damar shiga cikin gidan suka samu wuri suka d'an rakub'e gefe yadda zasu hango Babangida idan ya samu damar zantawa da Umaiyah.
Abakin k'ofar parlour Babangida ya fara knocking door ahankali yakai minti biyar atsaye yana k'wank'wasa k'ofa,can dai cikeda tsananin haushi Umaiyah ta taso ta bud'e k'ofar da niyar yiwa wanda yake damunsu da knocking masifa,idanunta ne suka sauka akan Babangida jikinta ne ya d'auki sanyi yayinda gab'ob'inta suka gauraye da wani irin yanayi akunyace kanta na k'asa ta gaidashi ya amsa mata cikin fara'a yace"k'anwata A'isha Auntynki Umaiyah nake son gani..".
Umaiyah ta saki numfashi tace"ai nice Umaiyah..".
"Allah sarki kiyi hak'uri na zata kece A'isha..".

CIKAR BURIWhere stories live. Discover now