Season THIRTY FIVE

66 9 0
                                    

🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
🐾🐾🐾🐾🐾
🍇🍇🍇🍇🍇
   *RAUDHA*
🍇🍇🍇🍇🍇
🐾🐾🐾🐾🐾
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂

*MALLAKAR:* ✍️
              _Nafisat Ismail Lawal Goma._

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

         *\F.W.A📚/*

.

  *NOT EDITED* ___________________________📗

        *SEASON THIRTY FIVE*

_______📖 A ranan da su Maan suka shirya gagarumin birthday ɗin shi, ƙarfe 05:00pm. RAUDHA ta shirya ta wuce, kasancewar dama da yamma za'a soma har zuwa dare.

    Sosai partyn ya haɗa manya-manyan guys masu ji da kansu, gashi ba ƙarya an kashe kuɗi sosai a wajen, wines ɗin ma da akayi ordaring ɗin su masu tsananin tsada ne

Haka suka wuni suna cashewa, ita kanta RAUDHA sosai ta saki jikin ta, ta shige cikin su Zen ana ta raha. sosai a ranan ta bugu, don ƙwayoyin da tasha ma sun fi ƙarfin ta, sai dai Rash ne ta dawo da ita gida, a time ɗin ƙarfe 08:pm. Ne na dare, lokacin Suhaib na masallaci sai Farida dake zaune a Parlour ita kaɗai, tunda Rayyan ba ya nan

Hankalin Farida ya tashi sosai sanda Rash ta shigo da RAUDHA tana surutai tamkar mara kai, sai dariya take yi tana maganganu, amsar ta tayi tana kallon Rash tace, "ke wai me tasha haka take wannan abun?"

Rash na sosa Kai tace, "kiyi haƙuri aunty, wlh party muka yi.." Sai tayi shiru ta kasa ƙarisawa

Tsaki Farida taja tana hararan ta tace, "dalla wuce ki bar mana gida, wlh idan baku ji tsoron Allah ba, watarana zaku yi nadama".

Ita dai Rash bata ce komi ba, tayi gaba abunta.

    Har ɗaki Farida ta shigar da ita, a time ɗin RAUDHA tayi ta kwarara amai kamar zata amayar da hanjin cikin ta, babu yanda ta iya dole ta wanke mata, sannan ta sauya mata kaya. har a time ɗin bata bar surutun da take yi ba tana ɓaɓɓaka dariya, kwantar da iya tayi ta fice a ɗakin

A Parlour ta tarar da Suhaib, nan ta faɗa masa duk abinda ke faruwa, ai babu ɓata lokaci yayi ɗakin RAUDHA, a kwance ya ganta idanun ta a rufe fuskarta ɗauke da murmushi

Ƙarisawa yayi kusa da ita ya zauna a gefen gadon yana kiran sunan ta

Buɗe idanun ta tayi ta aza a kansa, sai ta ƙyalƙyale da dariya ta hau yin masa maganganu, har da su zagi, ko kaɗan babu kan gado

Ajiyan zuciya ya sauke, ya ɗaura hannu a kanta ya soma tofa mata addu'a cike da damuwa a cikin ransa, ya daɗe yana mata addu'a, har sanda barci ya ɗauke ta sannan ne ya tashi yabar ɗakin.

      A taƙaice dai kwana biyu cur RAUDHA tana cikin wannan halin, taƙi komawa normal, dole Suhaib ya ɗauke ta zuwa asibiti. Sai dai bayanin da likita yayi masa, ya ɗaga masa hankali matuƙa

Ƙwayoyin da tasha sun taɓa mata ƙwaƙwalwa, that's why take irin Wannan abun

Har kuka sai da Suhaib yayi, ya rasa yanda zai yi, nan ya kira Rayyan ya sanar masa halin da ake ciki, shima hankalin sa yayi matuƙar tashi, nan ya taho asibitin akai ta zirga-zirga dashi, sannan aka ɗaura RAUDHA akan magani

Bayan kwana biyu ta ɗan samu sauƙi aka sallame ta, a ranan ne ta sake mugun mafarkin da ya ɗaga mata hankali, take ta farka tana kwatsa ihun da ya karaɗe ilahirin gidan

RAUDHA 2021Where stories live. Discover now