Season THIRTY SIX

60 12 0
                                    

🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
🐾🐾🐾🐾🐾
🍇🍇🍇🍇🍇
   *RAUDHA*
🍇🍇🍇🍇🍇
🐾🐾🐾🐾🐾
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂

*MALLAKAR:* ✍️
              _Nafisat Isma'il Lawal Goma._

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓'''

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

         *\F.W.A📚/*

.

  *NOT EDITED* ___________________________📗

        *SEASON THIRTY SIX*

_______📖 Ba don Allah yasa Daddy me saurin yarda da ƙaddara bane, da babu abinda zai sa be zube musu anan ba, sai dai kuma sosai ya dage wajen danne kaso sittin cikin ɗari na daga damuwar sa, amma hakan be sa fuskar sa ta hana bayyanuwar tsantsan damuwa da tashin hankalin da yake ciki ba, idanuwan sa gaba ɗaya sun kaɗa sun yi jazur, muryan sa na rawa ya ce da su, "yanzu tana asibitin ne?"

Rayyan ya ba shi amsa da "Eh".

"Ok ku mu je ku kai Ni". Yafaɗa yana miƙe wa tsaye da hanzari

Tare suka fice suka shiga motar Suhaib, Rayyan ne ya ja su zuwa asibitin.

    Suna isa ɗakin da aka kwantar da RAUDHA, Daddy yayi saurin ƙarisawa wajen ta, zama yayi ya ɗaura tafukan hannayen sa biyu saman fuskar ta yana shafa wa, ji yake yi tamkar yayi ta kurma kuka sabida tsananin tausayin ɗiyar sa. Wai yau RAUDHA ce kwance cikin wani hali na taɓin hankali, duk a sabida sakacin su

Lumshe idanu yayi yana sake sauke wa akan kyakkyawar fuskar ta, wanda ya rame sosai, sai haske da ta sake yi, barci take yi har yanzu sabida alluran barcin da aka yi mata. Ahankali Daddy ya saka hannun sa ya ɗauke hawayen da ya silalo masa a kuncin sa, sannan ya juyo yana kallon su yace, "ina ne Office ɗin doctorn dake duba ta?"

"Daddy bari in Kai ka". Rayyan yayi saurin faɗar haka

Gyaɗa kai kawai yayi yabi bayan sa

Shi kuma Suhaib ya koma kusa da ita ya zauna a gefen gadon, ya riƙe hannun ta ɗaya wanda akayi mata ƙarin ruwa aka cire.

     Wajen mintuna ashirin da fitan su Daddy kafin suka dawo, dayake magriba tayi, sai suka wuce gaba ɗaya masallaci, har bayan sallan isha'i suna nan a asibitin, har sannan kuma RAUDHA bata farka ba, dole suka taho gida suka bar ta cikin kulawar likitoci, tunda dama asibitin ba kasafai suke barin mutane suna kwana da mara lafiya ba. Daddy ya so ya kwana amma sai su Rayyan suka taushe shi akan ya koma gida, tunda shima yana buƙatar hutu a wannan lokacin

Sai da suka mayar dashi gidan sa, kafin suka wuce su ma, da zummar gobe Suhaib zai kawo mishi Haneep da Farida, sai su gaisa tunda yau basu samu sun haɗu ba.

     A taƙaice ranan Daddy be iya runtsa wa ba, kwana yayi a zaune yana nema wa ƴar sa samun lafiya daga wurin mahaliccin mu.

    Washe gari tare suka taho da Farida gidan Daddy ɗin, anan suka gaisa, Daddy ya amshi Haneep yana ta faman mishi wasa, sosai soyayyar yaron ya shiga ransa, kuma ya tausaya mishi da rashin lafiyan da yake yi, yayi masa addu'a sosai kafin ya miƙa ma Farida shi, sannan suka fito suka nufi asibitin, daga can Rayyan ya wuce wurin aikin sa.

     Wajen awanni biyu da zuwan su, sannan ne RAUDHA ta farka, amma kuma gaba ɗaya ta rikita su da koke-koken ta, kuka take yi sosai tana surutu kamar zautacciya, ba ma ta gane wanda ke kanta

RAUDHA 2021Where stories live. Discover now