Thirty Seven

57 11 1
                                    

🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
🐾🐾🐾🐾🐾
🍇🍇🍇🍇🍇
   *RAUDHA*
🍇🍇🍇🍇🍇
🐾🐾🐾🐾🐾
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂

*MALLAKAR:* ✍️
              _Nafisat Isma'il Lawal Goma._

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓'''

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

         *\F.W.A📚/*

.

  *NOT EDITED* ___________________________📗

        *SEASON THIRTY SEVEN*

_______📖 Sun daɗe a wajen likitan yana musu bayani, har yayi musu hanyar wani babban Malami dake garin Zaria, kuma sun amince zasu gwada ɗin ko Allah zai sa a dace.

    Sai da suka duba RAUDHA kafin suka bar asibitin.

     A cikin kwana biyu har an gama shirye-shiryen yanda zasu tafi da RAUDHA zuwa Zaria, tunda an rigada an sanar wa malamin kuma ya ce a kawo ta, gaba ɗayan su zasu yi tafiyan har Farida, tunda dama gida ne zasu koma shiyasa zasu tafi gaba ɗaya

Rayyan ya so ya bi su, sai dai yanayin aikin sa bazai bar sa ba, dole ya haƙura ba don ya so ba.

      A jirgi suka isa Zaria, gidan Daddy suka sauka inda anan ne Malamin zai zo ya riƙa duba ta, bisa alfarman da Daddy ya nema a wajen sa, (Chemist) cibiya ce babba suke da shi a Zarian, wanda aikin su ne cire ma mutane aljanu

    A ranan da suka zo, a ranan ne Malamin da zai duba ta shima ya iso gidan, a time ɗin RAUDHA na barci ne sabida alluran barcin da aka yi mata daga can asibiti, saboda samun sauƙin tahowa da ita

A tare da Daddy da Suhaib suka raka sa ɗakin da aka ajiye RAUDHA, sai da ya nemi abubuwan da yake buƙata wajen su, sannan ya zauna ya saka mata magani a cikin kasko, ta yanda idan har tana da aljanu dole zasu bayyana kansu idan turaren ya shiga hancin ta

Ilai kuwa, ana saka wa sai ta farka a firgice, gaba ɗaya zubo musu idanu tayi tana kallon su tamkar zata cinye su, sabida yanda ta waro idon nata waje, sai yamutsa fuska take yi tana cije baki

Malamin ta kafa ma idanu, wanda shima ita yake kallo, nan da nan idanun ta suka soma sauya kala zuwa ja, sai ta kawar da kai ta koma ta kwanta batare da ta sake ko motsi ba

Su dai su Daddy suna zaune akan sofa suna kallon ta, ko wannen su ya buga tagumi

Ajiyan zuciya Malamin yayi kafin ya kalli su Daddy yace, "tabbas yarinyan ka tana da aljanu a jikin ta, da alamu dai manya ne, saboda duk wanda na saka mishi maganin nan, dole ne su tashi a lokaci ɗaya su bayyana kansu, amma kuma ita ba haka ba, sai dai ta yanda ta farka ɗin nan, da kuma yanda idanuwan ta suka sauya kala, to, tabbas tana tare da su. Insha Allahu zamu fara aikin mu nan ba da jima wa ba idan abokan aikina sun zo, zamu fara mata ruƙiya ne su fara bayyana kansu, sannan mu san abun yi".

Suhaib da Daddy jinjina kai suka yi alamun gamsuwa.

      Suna nan zaune Sai ga wasu Maza su kusan biyar sun shigo ɗakin

Malamin kallon su yayi yace, "su zauna su soma karatun".

Gaba ɗaya zama suka yi suka zagaye RAUDHA da har yanzu tana kwance idanu a rufe taƙi motsawa

Karatu suka soma yi da ƙarfin muryan su. sun daɗe suna karatun amma RAUDHA bata yi wani motsi ba, su kuma basu fasa karatun ba, sai da suka ɗau kusan mintuna talatin suna karatu kafin ta soma wani irin gurnani har yanzu idanun ta a rufe, hakan yasa suka sake dage wa suna sake ɗaga murya, nan da nan ta soma ihu tamkar wani ƙaton gardi, kukan yana fita ne kashi-kashi wanda baza ka gane na mutane nawa bane, kukan kawai take yi bata motsa ba, kuma idanuwan ta a rufe

RAUDHA 2021Where stories live. Discover now