Season Fifty Three

88 11 4
                                    

🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
🐾🐾🐾🐾🐾
🍇🍇🍇🍇🍇
*RAUDHA*
🍇🍇🍇🍇🍇
🐾🐾🐾🐾🐾
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂

*MALLAKAR:* ✍️
_Nafisat Ismail Lawal Goma._

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*RAMADHAN MUBARAKH*🤲🏽🕌
2021.

             *HADHISI*
_An karɓo daga Baban Salma Allah ya ƙara musu yarda ya ce, "na tambayi A'ishah matar Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama, nawa ne sadakin Manzon Allah?" Sai tace, "sadakin Manzon Allah ga matan sa uƙiya goma sha ɗaya da rabi (nashsha). Sai ta sake cewa "shin kasan Nashshu?" Sai yace mata, "a'a"  Sai tace, "rabin uƙiya shi ne darhami ɗari biyar". Muslim ya ruwaito. Ingantaccen hadisi daga Muslim._

.

*NOT EDITED* ___________________________📗

*SEASON FIFTY THREE*

_______📖 Hannun ta ta saka ta kamo nashi, hakan yasa ya juyo yana kallon ta, ido cikin ido suke wa junan su kallo, batare da ko wannen su yana ƙyafta wa ba

Sun ɗau tsawon soconni a haka kafin ita ta soma ɗauke kanta tana jan numfashi, sai tace, "I love you".

Tsaban maganar ta zo masa a bazata be san sanda ya fiddo idanuwan sa waje ba yana kallon ta da tsananin farin cikin da ya fito tun daga zuciyar sa, sai dai ya kasa magana illa kallon ta da yake yi

Jin yayi shiru sai ta mayar da idanun ta kansa, ganin kallon da yake mata sai ta taɓe baki tace, "Ina son ka ba yana nufin na amince zan aure ka bane". Tana gama faɗar haka ta saki hannun sa ta juya zata koma

Yayi saurin riƙe mata hannun, dole taja ta tsaya, but ta kasa juyo wa illa lumshe idanuwan ta da tayi tana sauraren bugun zuciyar ta

Tako wa yayi ya dawo gaban ta, idanun sa a kan ta da tsananin murna yace, "idan har kina so na, na tabbata zaki iya aure na, kenan kina nufin kin amince dani a matsayin masoyin ki?"

Huro hanci tayi sai dai ta kasa kallon sa, illa shiru da tayi tana haɗiyar yawu

Shi kansa ya lura akwai Magana a bakin ta, sabida yanda take ta motsa bakin tamkar zata buɗe tayi magana. Murmushi yayi yace, "I love You so Much RAUDHA! Ina son ki da yawa wanda baki ma bazai iya furta wa ba, kiyi haƙuri da duk abinda nayi miki kinji?"

Sai a lokacin ta ɗago manyan idanuwan ta ta sake kallon sa, sai tayi saurin ɗauke kai tare da janye hannun ta, ta gifta shi tana faɗin, "Ni fa ba ina nufin zan iya auren ka bane, duk da na faɗa maka wannan kalman, zuciya ta ce ta aiko Ni, but a zahiri baka yi min ba".

Sosai maganar nata ta ba shi dariya memakon haushi, sai da ya murmusa yana shirin magana, sai ji suka yi an buɗo ƙofan, daga shi har ita juya wa suka yi su ga wanene

Suhaib ne tsaye yana bin su da kallon tuhuma, ganin su cirko-cirko da yayi a tsaye kusa da juna, sai kawai ya saki fara'a a fuskar sa yana faɗin, "Baby kin.."

Saurin katse sa tayi da faɗin, "Yaya Ni dama Toilet zan je shi ne na sauko". Sai ta juya kuma tayi Toilet ɗin da sauri har tana kanannaɗe skert ɗin ta tun kafin ta isa don ya tabbatar Toilet ɗin take son zuwa

Daga shi har Ray da kallo suka bi ta, ko wanne na sakin murmushin da be shirya ba, sai kuma suka jiyo da kallon su ga juna suna ci gaba da murmushin

RAUDHA 2021Where stories live. Discover now