Forty Five

72 11 0
                                    

🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
🐾🐾🐾🐾🐾
🍇🍇🍇🍇🍇
      *RAUDHA*
🍇🍇🍇🍇🍇
🐾🐾🐾🐾🐾
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂

*MALLAKAR:* ✍️
              _Nafisat Ismail Lawal Goma._

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

         *\F.W.A📚/*

*RAMADHAN MUBARAKH*🤲🏽🕌
                     2021.

                  *NASIHA*
     '''Muna iya lura cewa ga al'ada in an Kira talaka zuwa fadar sarki yakan gyara fuska, ya yi ado don ya sami kyakykyawar maraba daga Sarki. To, in haka ne, ina ga in ya tashi zuwa tsayuwa gaban  Ubangijin sa? Bawan da aka neme shi ya zo gaban Ubangiji, Sarkin sarakuna, mamallakin mamallaka, lalle kam ya fi kamata ya gyara kansa saboda wannan muhimmin muƙami. Ya kamata ya gyara kansa ta tsarkake tufafin sa da jikin sa, ya fito cikin kama mafi kyawu, kamar dai yadda aka umurci musulmi duka a cikin suratul A'ARAF, aya ta 31:
       _"ya ɗiyan Adam! Ku riƙi ƙawar ku a wurin ko wane masallaci"_
  Allah yasa mu dace.'''

.

  *NOT EDITED* ___________________________📗

        *SEASON FORTY FIVE*

_______📖 Lokacin da Rayyan ya shigo gidan, time ɗin su Daddy gaba ɗaya suna masallaci, sai Ammee dake zaune a Parlour, RAUDHA ta ɗaura kanta a saman cinyoyin ta suna ta hira suna dariya, sosai RAUDHA ta saki jiki da Ammee, sai tana kallon ta tamkar Mahaifiyar ta, bata taɓa kewar Mahaifiyar ta ba tunda take, sabida Daddy da Suhaib sun ɗauke mata komi, duk abinda uwa zata yi mata suna mata, ba su taɓa barin gurbin da zata ji kewar Maman ta ba, shiyasa ta taso ko kaɗan bata taɓa tuna wa da ita ba, ko a hoto ba ta ganin ta, duk da suna da hoton nata, amma ita ba ta ɓata time ɗin ta wajen ganin ta a hoto. shiyasa yanzu da Ammee take nuna mata ƙauna da kulawa, sai taji sosai take kewar Maman ta, sai taji tana matuƙar ƙaunar ta, har tana jin da ma tana raye ta so ta itama kamar yanda Ammee take mata fa. a jiya da take tunanin nan har sai da tayi kuka sosai, shiyasa a ranta yanzu ta ɗauki Ammee tamkar tana tare da maman ta ne, komi da zata iya faɗa mata zata iya sanar wa Ammee

Yanda RAUDHA ta saki jiki sosai, hakan sai ya faranta ran Ammee matuƙa, sosai take jin soyayyar ta a ranta, kasancewar ta me ƙaunar ɗiya mace, tunda Allah be bata ba.

     Sallaman Ray, shi ya dakatar da su daga hiran da suke yi suna dariya, a tare suka amsa mishi har RAUDHA da tayi tunanin ko Faruk ne, tunda muryan su ba shi da banbanci, sai dai yanda taji ƙamshin turaren sa ya daki hancin ta, sai tayi saurin lumshe idanu tana sake zuƙo turaren sosai, but duk a tunanin ta ba shi bane.

      Allah ya sani turaren sa yana matuƙar mata daɗi, bata san meyasa ba. tana jin sanda suke gaisa wa da Ammee, sai hakan ya bata mamaki tayi saurin ɗago kanta tana sauke idanun ta akan shi, yanda idanun ta suka faɗa cikin nasa sai tayi saurin ɗauke kai tana koma wa ta kwanta

Murmushi shi kuwa yayi, ya kalli Ammee dake shafa kanta a yanzu ɗin yace, "Ammee su Uncle fa?"

"Sun je masallaci".

"Ok Nima bari inje dama ban yi sallan ba". Har ya miƙe kuma sai ya kalli RAUDHA da idanun ta ke rufe yace, "pretty babu gaisuwa?"

Wani irin sara wa gaban ta yayi, dasauri ta buɗe idanun ta tana sakin numfashi me ƙarfi, sake mayar da idanun ta tayi, ahankali ta furta, "naharan sa'idan".

RAUDHA 2021Where stories live. Discover now