Forty Six

71 8 0
                                    

🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
🐾🐾🐾🐾🐾
🍇🍇🍇🍇🍇
      *RAUDHA*
🍇🍇🍇🍇🍇
🐾🐾🐾🐾🐾
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂

*MALLAKAR:* ✍️
              _Nafisat Ismail Lawal Goma._

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

         *\F.W.A📚/*

*RAMADHAN MUBARAKH*🤲🏽🕌
                     2021.

.

  *NOT EDITED* ___________________________📗

        *SEASON FORTY SIX*

_______📖 Sun Isa Bayelsa wajen gabanin magriba, driver ya zo ya kwashe su ya nufi da su tanƙamemen gidan su, gidan flet ne me kyan gaske

Suna shiga parlour'n matasan duk suka wuce ɗakunan su, inda Ammee ta nuna wa RAUDHA ɗakin da zata zauna, tana fita ta shiga Toilet tayi wanka sannan ta ɗauro alwala, doguwar riga blue ta saka kafin ta gabatar da sallah

Bayan ta idar ta fito Parlour, babu kowa sai Ammee da itama zaman ta kenan

Tace, "ƙariko mana ɗiya ta".

Taho wa tayi ta zauna a gefen ta

Ammee na murmushi tace, "kin ji sabon wuri, da fatan dai ya miki?"

Itama murmushin tayi tace, "Yayi min Ammee".

"To Masha Allah haka nake so, bari in saka a kawo miki abinci ko kina jin yunwa".

"A'a Ammee a bari sai anjima zan ci".

Ammee tace, "to shikenan, kinga dai gidan mu ko. Nasan yanzu dare yayi ne shiyasa babu wanda zai zo sai zuwa gobe zaki ga ƴan uwa, Family House ɗin mu na nan baya ne, mutanen gidan duk ƙannin Uncle ne da matan su da ƴaƴan su, zuwa gobe insha Allahu sai mu je ku gaisa".

"To Ammee". RAUDHA tafaɗa tana murmushi.

    A lokacin su Faruk suka shigo da sallaman su

Amsa musu suka yi.

Zannurain sarkin tsokana yace, "Hajiya RAUDHA ga ki ga garin mu, to ya kika ji namu garin? Da fatan dai yayi miki zam-zam ko?"

Dariya tayi tace, "Bro Zannu ai komi zam-zam". Har da mishi waigi da hannu 👍

Wannan karon dukan su suka yi dariyan

Abubakar yace, "ai sai kin gaji da yawo, Allah ya kai mu dai gobe, gaba ɗaya babu inda bazan zaga dake a garin namu ba".

Ammee tace, "a'a babu inda ɗiya ta zata je gobe, hutu zata yi, idan ma yawon zaku fita sai dai zuwa jibi, yanzu ku tashi ku je ku ci abinci don ga yi can Asabe ta gama jera wa. Ina Uncle ɗin ku?"

"Yana wajen su Baba Iliya a waje". Abubakar ya bata amsan hakan

Tashi suka yi su ukun zasu nufi kan dainning, har sun yi gaba sai Abubakar ya dawo yana cewa, "Friend ke fa? Baza ki taso mu ci abincin ba?"

Girgiza kanta tayi tace, "ba yanzu ba".

"Cabb.. don Allah ke kuwa ba kya jin yunwa? Duk uwar daɗewan nan da muka sha a hanya?"

Hararan sa Ammee tayi tace, "dayake ance maka kowa ma irin ka ne, wuce ka tafi kai dai kaje kaci abincin ka".

Turo baki yayi yayi gaba

RAUDHA 2021Where stories live. Discover now