(The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟
BOYAYYIYAR ALKARYA(the hidden island )🌄🌄🌄🌄🌄phone number:09035784150
telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0
whatpad :@SAKHNA03
💓💓💓 I DEDICATED THIS FIRST CHAPTER TO MY FRIEND UMMU ~NAJMA ,FOR THE SAKE OF FRIEND SHIP ,AND HER CONTRIBUTION ON ME ,I LOVE YOU SO MUCH .💓💓💓
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM
chapter[01]
kyakkyawan dakine na alfarma daya kawatu da kayan alatu masu daukar hankalin me kallo a ta fuskar kallo, hankalina tafiya yayi zuwa kan gadon dayasamu waje na musamman a dakin,gadone na alfarma da bakowane gidajen sarauta ake samun irinsuba ,tabbas wannan gado yatafi da hakalina.Saidai a sanda idona yayi arba da mamallakin gadon wanda tunda ashe shine ya kawata gadon harnake wannan surutun akai,saina ga dakin yamin duhu shikadai nake kallo a dakin.Kyakkyawane nagaban kwatance wanda yanayin siffarsa harya kaini da dubansa domin naga ya yake,farine irin wanda baida haske sosai hakika fuskarsa da kawatu matuka faffadan kirjinsa da yasamu horon motsa jiki yafito da ainihin zatinsa,zarazaran gashin idonsa da suka kewaye idanuwansa kana sukabada tazara a tsakaninsu domin bada damar ganin hancinsa daya yayi dosss👃akan fuskarsa fitowa fili,idon nakai kan bakinsa dayake dauke launin ruwan powder mai kyau,duba nayi ga ji......Firgitar danayine yahanani karissa karewa wannan halitta ta maliki yaumiddini kallo sakamakon wani tashi dayayi daga baccin sa wanda alama ya nuna tabbas wani mafarki yayi mai firgitarwa,!
Wacece ke !? shine abinda yafito daga bakin kyakkyawan saurayin wanda yasani rudani tare daku baki daya......kubiyoni ni SAKHNA domin jin yadda zata kaya acikin littafin.
yarima SAMHAL kenan da daya tilo a wajen sarki SHARZAMAN da kuma gimbiya JAZILA na kasar KHAISIRA,kasar datayiwa sauran kasashe fintikau kana kuma tasamu zagorancin jarumin basarake wato sarki sharzaman.
Taku yake cikin kasaita dakuma nutsuwa inda kayan alfarma dayake sanye a jiknsa yara fito da anihin izzarsa,yanayin dayake ciki wanda shi bana damuwa ba kuma bana farinciki ba shiya taimaka wajen rashin amsa gaisuwar da dogarai dakuma bayi suke aika masa tasiri,tafiya kawai yake batare da amsa koda gaisuwa dayaba da ake aika masa.Ganin inda ya nufa ne yasani kaiwa hakalina wajen ,bawani waje bane face fadar mahaifinsa koda isarsa jakadiya tayima sa iso ya shiga,bai zame ko inaba sai gaban mai martaba inda fadawa suka amsa gaisuwar dayake mikawa ga sarki.alamar da sarki yayimusu ne yasa su barin fadar dan basu damar tattauna wa a sirrance.
samhal inaso kasani cewa hakika mun fara gajiya da wannan al'mari naka nakin zabar abokiyar rayuwa,tun kana shekara 30 mukaso nida mahaifiyarka kayi aure amma yaci tura to hakika kafara kaini bango a dalilin wannan halin naka,saboda haka zan yanke shawarar zaba maka daya daga cikin yayan wannan nahiya dasuke kewaye damu,cewar mai marta kenan kana ya tsaya da bayaninsa don jin mekuma dannasa zai fada,jin shirun daya biyo bayane yasa yarima samhal dagowa tare da fuskantar mahaifinnasa,tare da cewa'hakika kaida ummi nasan kun bani lokaci kuma kunyi kokarinku wajen bani damar zabar abokiyar zama amman na gagara cika muku wannan buri...!saida yarima samhal ya nisa kana ya cigaba da bayaninsa"ina bukatar kukaramin lokaci da sannu zan kawo wacce zuciyar ku ta yarda ita,ina da bukatar karin lokaci agareku ya abbana"koda yakai karshen jawabinsa sai yasake sunkuyar da kansa tare da girmamawa,shirune ya biyo baya kana mai martaba yafara magana"shikenan zamu kara baka lokaci amma kasani bazai kai wanda muka baka a baya ba".sunkuyar dakai da yarima samhal yayi shiya bada alamar cewa ya amince da abinda mahaifinsa yayi.Tsayawa yayi da barin fadar sakamakon maganar da mai martaba yasake yi masa"yanayinka ya sanza sosai wanda nida ummika munkasa gano abinda yake damunka,amma bazamu takura maka hakika komai yanada maganinsa,sannan kaje ka duba mahaifiyar ka hankanlita na kanka tsawon wannan lokacin"Batare da ya juyoba yayi naam da maganar sannan fita batare da bata lokaciba.
Bayan fitarsa daga fada bai zame ko ina ba sai turakar umminsa wanda sameta tana zaune hadimanta nayi mata hidima,dago ta fuskar tayi tasauke idon ta akan farincikin rayuwarta wato danta wanda take sansa fiye da komai,murmushin dayake fuskartane yakara fadada kana tamika masa hannu alamar ya matso gareta.karisawa yayi ya durkusa kafin yayiwa kansa masauki akan cinyarta.hummmm ta nisa kafin tafara yimasa bayani bayan barin hadimannata a dakin da dan wani lokaci"babana meyake damun kanene haka ?tun jiya nake rabon dana ganka sanda kazo gaisheni da maraice sannan babban abinda yafi dagamin hankali maganar auranka da kakibada hankalinka akai,tabbas abin yafara damuna sosai"juyowa yayi ya kalli idanuwanta fuskarsa cike da damuwa yace "ummina ba abinda yake damuna,zancen yin aure kuma mungama magana da mai martaba zan fito da wacce nake so ba da dadewaba,sannan banason naga kina damuwa akan hakan"."shikenan ABI(sunan datake kiransa dashi kenan sakamakon sunan mahaifinta dayake dashi).kallonta yake cike da soyyarta shima acikin zuciyarsa,sannan tacigaba da bayaninta"mahaifinka yasha sakawa a tara yayan sarki nahiyar nan domin ya baka damar kazabi wacce kke so acikinsu amma kaki zabar kodaya,inaso katsaida hankalinka kusa banaso kajawo mana magana daga sauran kasashen dasuke kewaye damu duk da nasan hakan bazata faruba amma kayi tunani akai sosai.shikenan umma zan gyara hakan bazata sake faruwa ba yafada tare da sake komawa ya kwanta akan cinyarta,tausar datake masa acikin sumarsa ne yasashi tafiya wani bacci mai dadi wanda yake dauke da nishadi kala kala.
gudu yake tayi yana mika hannu domin taimakawa matar datake tsaye a gabansa tana mika masa hannu wani abu kuma kamar sarsari na bakin karfe yana janta cikin duhu mai tsanani,a duk sanda hannunsu yakusa haduwa sai sarkar tasake janta da karfi,tana ihune tana kiran sunan da cewa "kar ka barni karka tafi daga gareni ka dawo izuwa gareni karka basu damar cin galaba koda baka ceceniba karka manta dani"yana jin sautin muryar ta acikin kunnensa haka kuma gangar jikinsa takasa tsayawa ga barin bin bayanta da haka har ta bacewa ganinsa gabaki daya......jikinsa sai jijjiga yake gumi ya rufe shi sharkaf yadade sannan yasamu damar farkawa tareda sautin magana a bakinsa"wacece keeeeeee ...😊to wacece kubiyoni a gaba dan jin yanda zata kasance daga marubuciyar ku wato 💟SAKHNA💟
kukasance tare dani inayinku sosai fans 👪💑💓...
YOU ARE READING
Boyayyiyar Alkarya
AdventureThe legendary story about the mysterious hidden🌄🌄 island the numerous of people and evils fails to find out about it. But find by the unremembered prince 🤴 without his knowing 🤔🤔🤔