Chapter 3

90 11 2
                                    

↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟

BOYAYYIYAR ALKARYA(the hidden island )🌄🌄🌄🌄🌄

phone number:09035784150

telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

whatpad :@SAKHNA03

chp[03]

Al'amarin yarima samhal kuwa koda ya koma sashensa tunani ne ya rufe shi akan wannan al'amari kana kuma da shawarar da abokinsa yabashi.
Bayan wani sa'o'ine dasuka wuce ya yanke shawarar bin abinda zuciyar tasa ta bashi wanda bakomai bane illa samo amsar abinda yake nema ,dahaka ne yana ta tunani har lokacin yayi aikinsa inda ya kwanta da burin tafiya wajen shaihu nurul zaman.Washagari da safe bayan ya shirya ne ya nufi sashen mahaifannasa cikn zullumin shin yafada musu abinda yake shirin yi kokuwa ya bari sai yasamo amsar ?Haka ya isa sashennasu batare da ya yanke shawara daya ba game da tafiyar tasa.
"ABI ina ka shigane tunda kayi bacci nadawo banganka ba sannan har dare banga ka shigoba?menene yake damunkane haka wanda ya sauya maka duk wani hali da ka tashi dashi ne ?"Dukkan wannan tambayoyin sunfito ne daga bakin gimbiya jazila sannan fuskarta dauke da damuwa da kuma alamar tambaya,"a'a umma bakomai banjin dadi ne kawai lokacin dana fita.Ina abba naje fada akace yayi tafiya jiya ?", "ehh bayanan tafiyane ta gaggawa ta taso masa wanda nima bansan dalilin tafiyar ba sai dai idan ydawo."UHM dama zanyi tafiyane zuwa wajen MU'ALLIM wanda bazan dade ba zandawo"koda yagama bayaninsa sai da ta kalleshi nadan lokaci kafin taja ajiyar zuciya sannan tace "hankalina baya kwanciya duk sanda kayimin maganar fita daga masarautar nan sannan kuma nasan mahaifinka yananan nasan bazai bari kafita ba,sai dai zan barka katafi saboda dalilai biyu:nadaya saboda yanayin damuwar danake ganin ka aciki,nabiyu saboda kaace min wajen mu'allim zakaje watakil garage damuwar dakake ciki.Danhaka nabaka izinin tafiya amma kadawo cikin kankanin lokaci"Tabbas yanayin yanda tabashi yardarta akan tafiyar yabashi mamaki duba da yanda suke nuna kin amicewar su a game da duk wata fita idan yace zai yi,wanda yakasa gano meyasa suke hakan wanda kosanda yana yaro basayimasa haka bare ya girma.Kawar da tunanin hakan yayi aransa sannan ya amsa mata da zai yi kokarin dawowa kamar yanda tace ,sannan yamata sallama yanufi inda ingarmar dokinsa yake.Domin a yanda yake ji bayason duk wani al'amari dazai bata masa lokaci bare kuma yakaishi ga jiran kwana guda a masarautar su.
Saida yashafe daukacin sa'o'in dasuke cikn ranar yana gudu a doki batare da ya yada zango a ko'ina ba,gudu yake tareda kwarewa dakuma sanin duk wani abu dayake kan hanyar tasa ta isa ga masaukin malamin.Byan rana tafadine kana ta sake bayyana a rana tabiyu da tafiyar tasa,yayi dadai kawowarsa gaban wani dutsi mai kyau haske da kyalkyali,dutsen nada tsayi ta waje guda sannan kuma yanada matsakaicin tsayi ta daya barin, wanda hakan ne zaibawa duk wani ma'abocin san hawa dutsen damar isa kan dutsin.Batareda da bata lokaci ba yatasamma dutsen ba bata lokaci wanda cikib kankanin lokaci ya isa ga saman farfajiyar wajen ,wajene mai yalwar fili dakuma haske mai walwali inada yazagate wata bukka guda dya,ita dai wannan bukka anyi tane da farar kasa mai haske sannan anyi rufinta da jelar dawisu mai kalala,tabbas a takaice wajen yahadu matuka wanda zai kayatar daduk wanda yakalli wajen.Sallama yayi daga bakin kofa,sannan aka amsa daga ciki cike da kamala dakuma ilimi,bayan amsawarne ya shiga cikin bukkar kana ya zauna agaban malamin wanda yake zaune akan buzu da akayishi da fatar barewa."YA kai magajin masarautar khaisira menene yake tafe dakai haka a wannan lokacin ?domin daga ganin yanayinka bai nuna alamar zuwa neman sani akan littatafaiba kaman kowane lokaci ?"Bayan da mu'allim ya gama jero masa tamabayoyi saida ya shafe wasu dakiku yana tunani kafin ya numfasa tare fara masa bayanin abin da yake damunsa atakaice,"Tabbas kaman yanda kafada ya mu'allim ba karatu nazao karawa ba a wannan lokacin nazao ne domin neman hanyar da zanbi domin magance matsalar datake damuna a tsawon wannan kwanakin,ina yawan yin mafarkin wata mace datake neman taimmako a wajena sannan idan nayi kokarin daukarsa kawai a kaman sauran mafarki sainaji kaman abun da gaske ne.Wanda ba iya a mafarkin yake damuna ba harma da zahiri dakuma walwala ta,wannan shine a takaice me yake damuna shin kokasan maganin matsalata ko hanyar dazanbi na magance ta ?"Saida ya mu'allim yagama jin dukkan abinda ke tafe dashi kana yafara masa bayani"HMM tohhh yakai yarima sahal kayi sani cewa lallai wannan al'amari akwai wani abu boyayye aciki wanda gaskiya ni bansaniba,saidai watakila yanada nasaba da fatan dakayi shekaru dasuka wuce wanda baka tashi bayyanaba har sai watanni takwas baya dasuka wuce.Wanda bawanda ya tambayeka ina katafi, sannan aka hana kowa tambayarka ina katafi ,domin tsoran rasaka a karo nabiyu"Saida yagama bayaninsa sannan yadaga ido yakalli fusakar yarima sahal wanda take cike da razana ,rudani kana dakuma alamr tambaya,sannan yacigaba da fadin"to inaga wannan mafarki dakake yi zai iya yiyuwa yanada nasaba da rayuwar dakayi a wannan lokacin."Bbbbbbata kkkkuma"shine abinda yarima samhal yafada cikin in'ina bakin sa kuma yana rawa kamar me koyar magana ,saida yasake yin shiru kana ya cigaba da magana"to ina naje ?a ina nake ?meyasa natafi to ?gun su wa naje ?meyasa namanta inda naje kuma ?"Duk wannan tambayoyi yana yin su ne jere batare da yatsaya ya ji amsar daya ba,shidai shaihu nurul zaman kallansa kawai yake sannan ya jijjiga kai da murmushi dauke a fusakar sa tafara magana "tohhhh duk wannan tambayoyi dakamun banda amsar kodaya aciki a halin yanzu ,saidai tunda abinda yashafi tuna wani abune a rayuwar baya watakil za'a iya samun amsar abinda kke nema amma babu tabbacin hakan shima,"A ina za'a samu amsar?inaso kafada mun koma inane ?yarima samhal yafada cike da gaggawa."tohh abinda za'a iya samun masalahar wannan matsala bakomai bane illa MADUBIN"" MATIHUL SAHIR "wanda yake cikin kogon SAHIR ,idan samu sa'ar zuwa gun madubin ,ka kalli fuskarka a cikin kana ka hure kurar da take kai to watakil zaka iya ganin boyayyiyar rayuwar dakayi a baya wadda baka da masaniyarta,sannan daga masarautar khaisira zuwa kogon sahir tafiya ce dazata dauke ka tsawon mako guda,bazan ce maka hanyar nada matsala ba sannan bazan cemaka lafiyarta kalau ba ,yadanganta da yayayin yanda ka ganta ,sannan abu nakarshe shine zan baka wasu kalmomi dazaka fada idan kaje bakin kogon wanda zai taimaka maka waje bude kofar."hmmmm Shikena nagode ya mu'allim da bayanin dakamu sannan ina mai sanar dakai cewar da sannu zan jega ga kogon matihul sahir domin samo amsar wannan boyayyen al'amari.Koda kawo nan da bayaninsa kawai sai tashi yayi ma shaihu nurul zaman sallama kana ya jiyo izuwa masarautar khaisira.

Boyayyiyar AlkaryaWhere stories live. Discover now