Chapter 4

58 9 2
                                    

💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟
               
BOYAYYIYAR ALKARYA(the hidden island )🌄🌄🌄🌄🌄
 
phone number:09035784150

telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

whatpad :@SAKHNA03

chp [04]

           *** ***   *** ***   *** ***
Bayan dawaowar yarima samhal daga wajen shaihu nurul zaman sai yazamana ya kebe kanshi daga masarau tarsu,domin tunanin yanda zai samu nasarar fita daga masarautar batare da sanin kowa ,wanda yana da tabbacin idan har mahaifansa sukasan da fitarsa bazasu aminceba.
  Washagari da safe tunkafin rana ta fito yarima samhal yayi shirin fara tafiyarsa izuwa ga kogon matihul sahir ,inda batare dasanin masu tsaron kofaba yayi nasarar fita daga yankinnasu ba ya nausa cikin daji batare da tsoro ko shakkah ba ,tafiya wanda take cikie da burin samun abu koda kuwa ta halin yaya ne.Saida yashafe wunin ranar yana tafiya kafin yasamu nasarar yada zango hakan ma badan kansaba saidan dokinsa dayake bukatar hutawa dakuma abinci,bayan yabawa dokinsa duk abinda yake bukata ne yafara zagaya wajen domin bawa idanunsa shima abincinsa "wajene ma'abocin dogayen bishiyoyi dakuma wasu irin kananan halittu dasuke zaune agun "hakika wajen ya kawatar dashi sosai wanda har ya yanze shawarar kwana a wajen kana washagari kuma yasake daukar hanya .
   Haka yarima samhal yayi ta fadi tashi a jejin na tsawon wani lokaci ,inda a kwana na shida ne ya tsinci kansa a wani nau'in jeji wanda ba komai acikinsa sai filin maliki yaumiddini ,mamaki ne yakamashi matuka domin duk wani jeji dayake wucewa a vaya babu wanda yayi kama da wannan wanda yake ciki a yanzu ,saida ya tsaya da dokinsa da dan wani lokaci kana ya numfasa sannan ya kutsa cikin sararin filin da bakomai acikinsa sai tarin tafiya bisa rairayin da ba'a ganin komai a wajen saishi.
  A haka yarima samhal yayi ta tafiya acikin wannan tsabirin harna tsawon wuni guda amma bai gamu da koda tsikene ba a hanyarsa ,ganin hakanne yasashi yafara karaya da tafiyar domin baya tunanin akwai wani abu a hanyar dayake tafiya,har ya fara juya akalar tafiyarsa ne idonsa yagano masa kaman wani tsibiri daga nesa,hakan ne yasa shi kara tasamma tafiyarsa cikin karfin gwiwa .Farin cikinr yacika shi wanda har ya bayyana akan fuskarsa sakamakon samunsa tsaye dayayi agaban wani farin dutse wanda aka rubuta kogon sahil ajikin dutsen da koren rubutu mai daukar hankali .Fara zaga dutsen yayi yana shafa shi da hannunsa da zummar yana neman kofar shiga cikin dutsen ,saida yaje yazagayo amma bai ga komai ba daya nuna masa wani alama ba tashiga kofar dutsen .Tsayawa yasake yi a karo nabiyu agaban koren rubutun kana daga bisanine yayi arba wani wasu kalmomi wanda suka bada wani magana amma ba'a cikeba ,saida yakare wa rubutun kallo sannan ya kula da inda kalmomin basu cikaba ,fitowa yayi da wata takarda a cikin jakarsa wanda take dauke da wasu kalmomi da shaihu nurul zaman yabashi sannan ya jerasu wajen da babu su a jikin dutsen .Yi hakan ke da wuya datsen yafara wata irin girgiza yana sauya salo zuwa wani kala nadaban ,saida yadau wani lokacin yana sanjawa kafinnan yajuye daga halittar dutsi zuwan wani irin kogo mai wata irin hanya a mike wadda zata kaika har izuwa cikin kogon .
  Nanma saida yasaya ya shirya kafinnan ya tasamma shiga cikn kogon daga shi sai takobinsa dayake rataye a bayansa ,saida yayi tafiya mai nisa a cikn kogon batare da yasan inda yake takawa ba saboda matsanancin duhun daya ke kewaye da wajen,duhun dayake cikin wajenne yafara alamar gushewa inda ya tsinci kansa a wajen wani fili mai madaidaicin fadi wajene a kewaye sannan babu wata kofa datake nuna alamar kofar fita daga wajenba ,ja yayi ya tsaya kana yajuya dasauri sakamakon ganin kofar daya biyo ta cikinta ta rufe kirif tamkar bata taba wanzu a wajen ba .jujjuyawa yafara yi a wajen amma babu wani abu dayake kama da hanyar fita a wajen ,motsin da kunnesa yake juyo masane yasashi juyawa da sauri amma babu mamallakin motsin a waren ,juyowa yasake yi inda yayi arba da wani abu da shi ake kira tashin hankali tsirararsa domin kuwa bakomai idonsa yagane masaba illah .........😊 ni 😀😀

    **** ***   *** ***  *** *** 
A can kuwa waje iyayen kasar wato sarakan kasar tunda sukaji bayanin da masanin yamusu suka shiga tashin hankali har kawo wani lokaci babu wanda nutusawarsa ta dawo acikinsu ,sannan abinda yakara musu tashin hakalima shine :shikansa mai gaba dayan wato boka gazaza wanda yake hulda da kalr aljanun da ba mahalukin da yake amfani da irinsu ,shima baida masaniya akan inda wani abun waishi boyayyiyar alkarya yake bare kuma su dayanzu ma sukaji labarin .Sannan abu nabiyu shima masanin dayake sanar dasu maganin matsalarsu ita ce boyayyiyar alkarya ,shima baisan yatake ba bare har yasan inda take a wannan duniyar .Ganin basu dayanda zasuyine yasasu yi wa masanin sallama kana kuma kowa tadoshi kasarsa ko akwai wani abu da zai iya yi kafin sake haduwa a karo na biyu akan al'amarin.
  Bayan sarki sharzaman yadawo gidane yasamu mummunan lbr na rashin tilon dansa da ya bace dagani tun jiya bayan dawaowar sa daga wajen shaihu nurul zaman ,abun ne taru yayi masa yawa gakuma tashin hankalin da uwar gidansa gimbiya jazila take ciki na batan danta sannan kuma mafi soyuwa a gareta .
    Gimbiya jazila ce a zaune a gaban wani babban takarda mai karfi  wanda yake dauke da zanen hoton yarima samhal a jikin ,daga kallon yanda idonta yake dakuma yanayin ta zai tabbatar maka da zancen zuci takr ko kuma kukan zuciya ,zancen zucin datake ne yafara fitowa fili batare da saninta ba inda tafara fadin cewa "mai yasa kke haka yakai dana ?mai yasa kke son ka dinga tafiya kana barina ?me yake damunka a wannan shekarun kke abubuwan da bahaka kke ba a da ?ko kuma auren da muka matsa maka kayi ne yasa kke gudun mu ?meyasa zaka tafi a karo nabiyu ?mu haka kaddarar mu zata dinga kasancewa damu dakai ?iyeeee ?😧😧😧"duk abinda take sarki sharzaman na zaune a gefenta ,ganin abin nata bana karewa kusa bane yasashi rukota zuwa kafadar shi ya fara lallashinta cike da tausayinta ,domin yasan indai a wajen dannata ne bata nuna wasa akan hakan ,"kiyi hakuri ummi ABI ,dasannu zai dawo gareki cikin kankanin lokaci kuma nasa ana kan bincike inshaallah baza a dau lokaciba za a ganshi, kokuma zai dawo kaman yanda yadawo gareki a karo na farko sannan.........bata bari ya karisa maganar sa ba takatseshi ta hanyar cewa "ahah ahah meyasa kke cewa irin batanshi na farko ?kana nufin najirashi nakusan tsayin shekara biyu kaman yanda nayi a baya ?ahah baxan iyaba wannan karon bazanyi shiruva dole na tambayeshi inda yake zuwa ,hakan yafara damuna matuka " dukka maganarta tanayine cikin damuwa sannan da kuma kin fahimtar duk wani wanda zai fada mata wata magana .Haka aka cigaba da neman yarima samhal a masarautar khaisira amma baabu alamr bayyanarsa a lokacin hakanne yasa damuwarsu ta kasu kashi biyu ,ga lbrin bakar wasikar da aka kawo musu,wanda yake nuni dacewa kasarsu nadaya daga cikin wanda za'a shafe matsawar bokanya urai -hilwa ta bayyana ,wanda a yanzu kowa nada takaitaccen lbr akan boyayyiyar alkarya sannan kuma wata damuwar tarashin bayyanar yarima a wasu kwanaki da suka wuce.
    HAKA masarautar ta khaisira dama sauran masarautun suke ta fadi tashinsu a tsakanin wannan lokacin ,inda a bangare guda ma dakaru kasar khaisira suka iya kokarinsu na neman yarima samhal dan kwantar wa da sarki sharzaman da gimbiya jazila hankali dama sauran mutanen gari
   
      *** ***   *** ***  ****
   
TOhhhhhh acan kuwa kogon na sahir yarima samhal ya gamu da gamonsa fah inda nima dana koma rahoto da kyar nasamu nasarar shiga ,danma ina shigewa ta iska shiyasa 😀😀😀😁😁
    Razanar da ta bayyana a fuskarsa bata komai bace illah arba da wata irin halitta da idanuwansa suka yi da ita."Halittar nada suffar mutum amma ta kere mutun girma nesa ba kusa ba tana da bangare guda biyu a jikinta ,daya na dauke da siffa kyakykyawa sannan daya barin da dauke da siffa mummuna "hakika duk wanda yayi arba da ita sai hantar cikinsa ta kada tsabar tashin hankali da rudani ,cikin zuciya sannan cike da jarumta yarima samhal yayi kanta da takobi tsirara batare ta jin shakkaba ,amma kafin ya isa gareta wata irin iska tatareshi daga isa gare ta ,dubanshi tayi a yanayin1 da bazaice wane kala bane sannan tace cikin wata murya da ta amsa amo acikin dodon kunnensa "Habaaaaa dan samari kana tunanin zaka iya yaki dani ka samu nasarar isa ga matihul sahir ?to koda kasamu nasarar yaki dani baza ka iya samun kofaba saidai idan nina bude maka ,sannan koda kasheni zakayi bazan bude maka kofaba saika bani amsar TAMBAYATA kuda daya kacal,bakomaibane tambaya ta face kafada min SUNANA [menene suna na ]?"tsayawa yayi yana kallonta cike da mamaki matuka dajin yanda tambayar tazo masa har takai ga yakasa koda kalma gudane daga bakinsa.Ganin datayi bazai bata amsaba yasa sake yi masa magana "shin yakai wannan saurayi kana mamakin tambayar danayi maka ne to kasani bawanipad mahaluki dazai ratsani yawuce tanan batare da ya amsa min tambaya ta ba ,wanda tambayace mai sauki amma zata kasance abar wuya wajen gane wacece .Sannan mutane dayawa sun sha zuwa wajennen saidai basa isa ga cikar burinsu,sannan kuma kasani amsa tambayata yanada sharadi da idan lokacinka na tsawon sa'a guda ya cika dole zaka koma dabaya ,ko kuma kuskuren jinkrta yin hakan zai kasan dadai da samu abincina a jikinka .
  Duk wannan surutun da halittar take ba abunda yafito daga bakin yarima samhal wanda ganin hakan yasa ta cigaba da bayaninta "shin baka magana ne hakika kanada sa'a  daga sunana da har kasa naji inajanka da magana  wanda kuma shine yakawoka har izuwa nan yakuma sa natsare ka daga isa gare shi,.........ganin lokacin dayake dashine yazo karewa yasa tanuna masa alamar ya fara shirin komawa da baya .koda yarima samhal ya gama jin bayaninta wanda ba daya daya tamka mata aciki sai ya juya domin fita daga kogon ......saidai abinda yaji yafito daga bakinta ne yasashi tsayawa cakkkk a inda yake,..."haka kuma shine daga cikin rayuwarka daya hanaka isa ga cikar burinka hahahahahaha ..."koda gama fadin haka datayi saita ga yatsaya a inda yake batare da fita daga kogon ba,bakomai yarima samhal yake ba sai shiga cikin wani zurfin tunani lokacin daya gama tuno duk wani magana da ta fadamasa ...Dafarko sunanta ne yasashi zuwa nan wajen ,sannan yanada sa'ar sunan ta dahar take zansa da surutu sannan sunanta yake so yaduba kyma hanashi shiga wajen datayi shima sunanta ne daya shafeshi ,daga karshe kuma sunanta ne yasa shi juyawa da baya yafuskanci kuncin sunanta ,to menene sunanta kenan ???
   Ganin lokacinsa ya cikane yasa ta fusata kana ta iyo kansa tana fadin "lallai taurin kanka yajawu maka yau "yayin da faratanta masu mugun dafi da sukayi dirar mikiya akansa suka tsaya cak domin jin kalmomin dasuke fitowa daga bakinsa bakomai banea illah "yake wannan halitta kafin ke naki sunan yakasan ce miki fainciki na samun yin kalaci dani to ki sani hakika da sannu sunannaki na bangaren rayuwata zai kasance mai sa'a har ya kaini ga cimma burina,tabbas kina nufin kice sunanki KADDARA "zaro ido tayi dajin mai ya fada sannan tace hakika kayi nasarar fadar sunana kuma ka kasance kai mutumne mai sa'a ,ina maka fatan alkhairi "koda gama fadan haka sai tabace tamkar bata taba wanzuwa ba kana kuma kofa tabayyana a gabansa ,inda yataka izuwa gaba dan ganin mai zai tarar .Idansane yayi arba da wani dutsi fari a tsakiyar wajen sannan haske na zagaye dashi ,yayin da yataka izuwa gaban dutsen kuwa sai yayi arba da wani madubi da baka ganin menene a cikinsa sakamakon farar kurar datake kansa .
   YARIMA samhal bai yi wani dogon bata lokaciba ya dauki madubin sannan yakawoshi izuwa ga saitin fuskarsa sannan yahura iska izuwa ga madubin ,sai da ya dauki wani lokaci ba abinda yake gani acikin madubin faace fuskar sa ,kana daga bayane haton yafara sauyawa izuwa ga wani al'amari daban ,abinda yabayyana a jikin madubinne yasa ka yarima samhal cikin rudani matuka ,bakomai yayi arba dashi ba illah ............???😊
  Wayana ba caji sai wani jikon yan uwa ,inasonku kuma ina muku missing.
  karku manta daga marubuciyar wato SADI ~SAKHNA (the legendary novelist )
         ku tara dani a gaba danjin mai yarima samhal yagani acikin madubin matihul sahir 💓
             

Boyayyiyar AlkaryaWhere stories live. Discover now