The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟BOYAYYIYAR ALKARYA(the hidden island )🌄🌄🌄🌄🌄
phone number:09035784150
telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0
whatpad :@SAKHNA03
chp(08)
Dasafe bayan sun gama ayyukansu kaman yanda suka saba,sai yazamana an zauna ana cin abinci.Bayan sun kammalane uzairu ya kalli sameer kana yace"uhm dana ka shirya zaka rakani shiga gari yau"to shine abinda sameer din yace,kafin agama maganar ne mulaifa tai sauri tace"nima zanje abba nadade banjeba zan rakaku" ahah yar imminta kibari sai wataran idan za'akoma amma yanzu mu biyune zamuje kinji"har ta bude baki zata sake magana alamar bata yarda dacewar babantaba,kafin takaki ga sake magananr ne salma tayi sauri tace"ahah mulaifah banason wannan gardamar taki,yau tafiyarsu ba bukatar kije yau kiyi hakuri kaman yanda yace sai watarana kinji".
Haka tayi shiru dajin abinda iyayenta suka fada amma tana mamakin wane tafiyane baza'aje da itaba.Bayan gama kamalla abinda zasuyi ne uzairu shida sameer suka kama hanyar tafiya izuwa cikin garin wanda shine a kusa da garin nasu,tafiya mai tsawo sukayi kafin suka iso ga garin bayan rana tafara zafi,tun daga hanya yanda uzairu ke gaiawa da mutane yatabbatarwa sameer cewa uzairun yasan garin sosai,amma abinda yabashi mamaki shine menene yasasu zamam acikin wannan jejin su kadai,tunanain nasane ya katse dajin wani mutum na masa magana,juyowa yayi da dan alamar razanan kadan,kafin ya amsa gaisuwar da mutumin yamasa,murmushi uzairu yayi kafin yace"menene yafaru dana kke tafiya tunani haka?to wannan shine mlm uwaisu aminina ne sosai sannan gunsa muka zo saboda wani muhimmin abu"jijjiga kai sameer yayi kafin yakara sukuyar da kansa alamar girmamawa,kafin mlm uwaisun yamusu iso zuwa cikin turakarsa.
Bayan sun zauna ne uzairu ya nunawa sameer waje ya zauna,abinne yabawa sameer mamaki ganin yanda ya tarar mutane a wajen tamkar su ake jira da ma a wajen,bayan a dan samu nutsuwane a wajen kafin mlm uwaisu yayi gyaran murya kafin yace"to kai yaro nasan zakayi mamakin me ya hadamu a wajennan ,to wannan bakomai bane illah bukatar shi mahaifinnaka domin shine yakirani ya bukaci a hada wanna taro,amma waka a bakin mai ita tafi dadi dan haka,yanzu zai maka bayanin meyasa muka taru anan wajen dagamu har kai dakuma shi"bayan gamam jawabin mlm uwaisunne uzairu yajuya ga sameer din domin bawa maganar sa muhimmanci,kafin yafara yi masa bayani."da farko zan kira sunanka da wanda muke kiranka dashi ko kuma wanda mulaifah kekiranka da shi wato sameer tunda har yanzu bamu da masaniya menene sunanka har yanzu, kafin nafada maka abinda yakawomu nan wajen inaso namaka wata tambaya,domin naji manene kai ra'ayinka,tambabyr shine inaso naji daga bakin ka shin menene matsayina a wajenka?meka daukeni a ranka?"tmabayar a bazata tazowa sameer kana kum tabugeshi matuka,saidai yayi shiru yana tunani kafin ya fara fadn cewa"na daukeka amatsayin mahaifina sannan dagaske nanke har cikin zuciyata"alhamdulillah shine abinda uzair yace bayan yaji menene yafito daga bakinsameer din,yacigaba da cewa"hakika na jidadin hakan saidai duk da haka ina baka hakuri game da hukuncin dana yanke a game da rayuwarka yanzu wato,ina so na hada k aure da mulaifah idan har ka amince,kuma ka yara dani a matsayin mahaifinka sannan kuma ka yarda bazan cutar da kai ba"dagowa sameer yayi a razane hade da kaduwa da jin abinda uzairun yace,suma mutanen dake wajen sun yi mamakin yanayin dasuka ga sameer din a ciki bare kuma uzairun dake maganar,saidai kuma yananyin abinne yasanza musu dasu kaga hawayen da ke fitowa daga idon sameer din kafin yafara cewa cikie da karayar zuciya"ahah bancancanta da mulaifah ba abba i bakone wanda baisan asalinsa ba bare da ga inda afito,taya zaka bani ita amatsayin mata,saidai nayi alkawarin zama a matsayin yayanta da ta rasa a baya matsayin ina tuna ta a rayuwataamma gatan da kamun ma na matsayi da kuma muhalli kamin komai amma wannan dakake shirin karamin bai cancanta dani ba sam ga bakon mutum irina,domin aure ba abin wasa bane sam,"
Haka ya cigaba da kuka cikin raunin zuciya yana magana wanda duk mai saurare sai yasan maganar na taba masa zuciya matuka,shima uzairu cikin duriya yarikeshi kafin yafar fadin"kenan maganar a kamun na cewa ka daukeni kaman yanda mulaifah ta daukeni ba gaskiya bane ko?"ahah hakane"shine abinda sameer ya fada yana girgiza kai kafin uzairun ya cidaba da cewa"to idan hakane abinda kafada na baka mulaifah halak malak kuma har abda banaso ka sake nuna wariya tsakaninka da wanda suke iyalina,sannan ko bayan raina nabaka amanar ta matsayin hankalinka yana a gare ta.
Shiru sameer yayi yana jin bayanin da baban mulaifan yake masa,kafin daga baya yaji uzairun yanafadin"yanzunnan za'a daura aurenku a wannan wajen domin banajin zanyi iya bari sai wani lokacin,sannan ni da kaina zan biya maka sadakin ka yanzu"dagowa sameer yayi kafin yace nagode nagode sosai da wannan abinda kamin,kuma inshaallah zan kasance mai riko da abinda ka bani matsawar ina numfashi,amma batun sadaki inaso na bayar dakaina"kafin yakai ga karisa maganar ya ciro zoben dake hannunsa ya mika ga mlm uwaisu,tambayrsa uzairun yayi tare da cewar"amma ya akayi ka samo wannan zoben?" ahah haka nima na sameshi a hannuna lokacin dana ta shi daga jinya"kara tamabayarsa uzairun yayi a karo na biyu"amma ba ka ganin cewa bazai iya kasancewa yana da muhimmanci a rayuwarka?" "koda yana da muhimmacin da yakai rayuwata zan iya bayarwa akan yazama ban bada komai ba sannan shine burina ya kasance yana da muhimmanci sosai domin shine abinda ya kasance mallakina kadai a wannan duniyar."
Shiru sukayi dajin abinda ya fada kafin,aka bada zoben akak fara shirye shiryen aure.
Bayan angama abinda za'ayine sukayi shirin komawa a rananr lokacin rana ta fara juyawa zuwa wajen saukarta,tafiya suke amma kwata kwata hankalin sameer baya jikinsa sam,domin shi har yanzu bayajin shine a yau kuma wai aka daura masa aure,yanzufa kenan hakkinta dukka yana kansa,kum.....uzairune ya katse tunanin dayakeyi ta hanyar fadin"kana tunanin sabuwar rayuwa ko?kar ka damu komai zaizo da sauki".
Shigowa sukayi bakinsu dauke da salamma,mulaifah ce ta amsa masa da suka sameta a bakin shigowar gidan,kafin kuma salma bayan taji muryarsu itama ta shigo domin tarbarsu,har ta kariso wajen tana murmushi cike da murnar ganin dawowartasu,kafin tace"uhm to yanzu hankalinki ya kwanta kinga sun dawo ko?"ta karsa maganar tana kallon mulaifah wanda dagajin anyi maganar tayi murmushi kafin ta boye fuskarta da tafin hannunta,dukkansu dariya suka mata kafin uzairu yasake cewa "amma duk dokin dawowar mune kko kuma tayi kewar yayantane,"uhmm kaima ka fada domin ko aika taki taje wai ita jaaruun bazai rakata ba sannan kuma tanaji haushi kki tafiya da ita"dariya dukka suke ta mata,wanda shikuma sameer a bangarensa yatafi wani tunani daban,inda mulaifahn takara tafiya da hankalinsa barema lokacin da tayi dariya tana rufe ido,gani yayi duk duniya ba ya ita kyau,sannan ta masa kyau fiye da kowane lokaci a baya,mamakin sauyin dayaji akanta yake na dan wani lokaci haka,katse masa tunani mulaifah tayi ta hanyar cemasa ya zo su shiga gida yatsaya shidaya.
Koda suka shiga gida abubawan dazasuyi sukayi kafn daga bisani kuma uzairun yayi kiran dukkan iyalannasa domin sheda musu abinda yake tafe dashi,bayan sun zauna ne kamar kullum sameer na gefensa yayinda mulaifah kuma take a bangaren mahaifiyarsu,saikuma yazu tsarin ya sauya,domin uzairunne yayiwa mulaifah umarni da ta tashi ta dawo bangaren sameer ta zauna,abnne yabata mamaki saidai bata musa abinda mahaifinnata ya fada ba,koda tazo kusa da sameer din matsa mata yayi gefe dashi ta zauna ba tare dakowa ya ce komai ba.
Shirune yabiyo baya kafin kuma uzairu ya fara gyaran murya tare da shaida musu duk abinda ya wakana bayan fitarsu daga gida har zuwa dawowarsu gidan,bayan sunji abinda ya fada ne mulaifah ta daga ido ta kalli sameer din amma koda suka hada ido sai tayi saurin saukar da nata idon cikin jin kunya,maganar da uzairun yacigaba da yine yasa hankalinsu yakara komawa gareshi,"to da fatan kunji abinda nace kuma zakuyi biyayya a game da sabon nauyi da hau kanku sannan zakuyi hakuri da junanaku sosai,"bayan yakai nanne da zancensa sai kuma yamika mata zoben dake hannunsa kanan yace"wannan shine sadakinki daga wajen mijinki dafatan kinyarda da shi amatsayin sadakinnaki?"ehh abba na amince kuma zan kasance mai karbar duk wani hukunci da ka yanke akain sannan zan kasance mai biyayya a kansa".
Bayan ya gamam musu bayanin abinda yakasance sai kuma yafar musu bayanin akan sha'anin aure dama zaman ita kanta wannan duniyar,".
To da farko inaso kusa hakuri domin saidashi komai zai tafi yarda akeso,sannan kusani cewa rayuwar da kukayi baya ba ita ce zakuyi a yanzuba hakkin da yake kanku ya banbanta da wanda yake kanku abaya,barema ke mulaifah kece mace to kiyi sani cewa hakkin da yake kanki yafi wanda yake kansa shi mijinki yawa,dan a yanzu daya kuke a mahaifiyarki a wajen matsayin matar aure dan haka inaso na karamiki tuni akan abinda nasan kinriga kin sani,a da hakkinki yana kanmu ne yimana biyayyaa da kuma kiyaye fushinmu wanda munsan kinyi kokari akan hakn ,to kisani yanzu wani nauyin ya hau kanki wanda a yanzu yafi namu nauyi akanki,kiyiwa mijinki biyayya dakuma kiyaye abinda bayaso matsawar bai sababwa mahaliccinki ba,sannan kaima sameer sai kafi hadawa da hakuri domin tunanin ku ba daya bane domin ta fika rauni dakuma kajeren hankali,sannan daga karshe ina jan hankalinku daku rike junanku da amana,allah yamuku albarka gabadaya,ameen suka amsa gabada yansu,tun da'aka fara bayani salma batasa bakiba sai yanzu da ta cemusu "duk abin zan fada babanku ya fada ba abinda zance sai allah yamuku albarka sannan ke kuma mulaifah kicigabab daga inda muka doraki banyarda ki kauce daga turbar da muka doraki ba komin tsanani yanayi dazaki riska kisani akwai sauki,kiyiwa mijinki biyayya dadai gwargwadon iyawarki,allah ya muku albarka,da aurenku harma da zuri'arku"sameer kansa na kasa yayinda mulaifah kuma takasa rike kukan datake a cikin zuciyarta har saida yafito fili,dukkansu suka amsa a tare wajen cewar ameeeeeeeen.
Bayan wannan farin ciki dakuma cikar buri da wannan iyalai suka gani a yau saikuam labari ya sha banban,inda abin mamaki yafaru wanda ya sauya kaddarar wannan ahali gaba daya daga haske zuwa duhu.🌌🌌🌌🌑🌑wane duhune🤔🤔kubiyoni a gaba domin jin menene😊😊😊.......
❤️♥️SADI-SAKHNA♥️♥️ ce(the legendary novelist)🌄🌄🌄
YOU ARE READING
Boyayyiyar Alkarya
AdventureThe legendary story about the mysterious hidden🌄🌄 island the numerous of people and evils fails to find out about it. But find by the unremembered prince 🤴 without his knowing 🤔🤔🤔