(The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟
BOYAYYIYAR ALKARYA(the hidden island )🌄🌄🌄🌄🌄phone number:09035784150
telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0
whatpad :@SAKHNA03
Chp 10
Bayan sun gama maganane sameer yafito daga dakin babannasu hannunsa daukeda sarkar da yabashi yana juyata cike da mamaki,mulaifahce ta tari gabansa kafin tace"meyasamu wannan jaruminnawa yashiga cikin wannan zullumin?"kallonta sameer yayi cike da mamakin maganarta dakuma sauyawarta tashi daya,itama hakan dayayine yasa ta lura da meyasa yake mata wannan kallon,rike hannunsa tayi kana tace"kana mamaki da yanayina ko,to kabar hakan domin a yanzu yakamata zuciyata takoyi daure duk wani kalubale da zata fuskanta,domin inaji a jikina cewar wannan bashine iya abinda zan fuskanta ba,dan haka yakamata nakoyi dauriya ko dan gaba"kodajin bayanin ta da yayi sai ya ruko hannunta data rikeshi da shi,kana ya kai hannunta izuwa bakinsa ya sumbaceta a yatsun hannunta kafin yace"hakika naji dadi da kika dauki dangana akan abinda yashafi rayuwarmu saidai banso naji kinacewa wuyar damuke ciki bazata kareba kinji,domin hakan tamkar yanke kaunane ga rahamar allah"janta yayi suka zauna akan dakalin dake jikin dakinsu suna rike da hannun juna amma bawanda yayi magana acikinsu kowa da abinda yake sakawa aransa,saida suka shafe tsawon lokaci a haka kafin sameer ya ciro sarkar da uzairu yabashi acikin jakar dake gefen rigarsa yamikawa mulaifah,kallonsa tayi kana ta kalli sarkar amma bata karba kaman yanda ya ke bukataba,saia yakara mika mata a karo nabiyu kana ta karba,jujjuya sarkar take kafin ta ce"meyasa ka bani wannan abin?"sa hannunsa yayi shima akan sarkar dake hannunta kafin yace"inaso ki ajiyeta ne a wajenki idan ina bukata saina karba,dan ni ban iya ajiya,sannan wannan abun yana da muhimmancin dayake bukatar adanawa a wajen daya dace,"bayan ya gama bayaninnasane mulaifah ta jijjiga kai alamr ta yadda da abindayace,kana ta tashi domin adanawa kaman yanda mijinnata yabukata,bayan ta dawone dukkansu sukayi turakar da mahaifinnasu yake ciki domin tayashi hira karsu barshi shikadai a dakin.
Koda shigarsu dakin zama sukayi a gaban babannasu,a inda a bangarensa shima ya kuresu da ido tun lokacin da suka shigo,idonsa cike da jin alfaharin yayannasa, murmushi yasakarmusu kana yace"ya yinin yau yazomuku dakuma kewar rashi da muke ciki"alhamdullilahi shine abinda suka ce kana daga bisani mulaifah tace"abbah kaine yakamata muyi maka ya wunin hakuri domin domin kaine kafi kowa rashi fiye damu,a da a rashin hankalina ina tunanin na fikowa rashi saidai a yanzu nagane cewar nice yakamata nadinga kwantar maka da hankali bawai na dinga daga maka ba,kayi hakkuri abbah da sannu ina mai tabbatar maka dacewar bazan sake tayar maka da hankali irin na daba"haka maganar tare da dan guntun hawayenta daga karshe,shima uzairun dafa kanta yayi tare da cewar"ahah karki fadi haka yata hakika nasan kema kina cikin damuwa saidai innso ki koyi dauriya a rayuwarki saboda bawanda yasan yanda rayuwarsa zata kasnce,amma nayi farinciki danaga cewar duwar dake tattare dake taraguu bakamar da ba,wanda nasan har da taimakon mijinki ahakan,shima nasan yana cikin wani irin yanayi dan haka inarokonki da kidinga taimakamasa karki kasance ke kadaice mai bukatar kulawa,inaso ku hadu kukula da junanku sosai".
Haka rayuwar ma'abotan zaman jejin takasance inda yanzu indan sungama duk wani abu nabukata tare suke haduwa a dakin babannasu suyi ta hira,inda shikuma uzairu a bangarensa kullum yake musu nasiha a boye domin su iya rayuwa sukadai idan baya tare dasu,hakan kuwa takance domin duk kular da mulaifah kebawa mahaifinnasu hakan bai hanashi boyemusu abinda yake cikiba a karo nabiyu,domin a halin yanzu ciwon dake jikinsa yaci karfinsa sosai yazamana cewar baya iya koda fita daga dakinsu,sannan bayason yarannasa sukula da halin dake cikin saboda lokaci yayi dayakeso suma suyi rayuwar farin ciki batare da yana kawomusu damuwa a rayuwarsu ba.
Bayan kwana biyu da ciwon uzairu yafara tsanani sai yazamana yanzu su mulaifah a wajen sa suke kwana basason duk wani dazai gifar ya matsar dasu daga kallon mahaifinnasu.
cikin dare suna kwancene sameer yaji tarin da babannasu yake yi yayi yawa hakanne yasashi tashi domin yaga meyake faru,abiine yarazanashi ganain yanda uzairun yake \tare batare da tsayawaba,matsawa yayi wajen sa dasauri ya rikeshi yana masa sannu kana daga baya uzairun yafara masa magana a hankali dan kar ya tashi mulaifah da take bacci"ahah karka damu sameer koda a yau na amsa kirana nasan zaku rayu cikin farin ciki a wannan waje,duk da cewar na jawo ka zuwa cikin kaddararmu na zama a cikin jeji bayan baka kasance daya cikinmu ba,kayimin afuwar hakan sannan abu na karshe dazan maimaita kurike junanku da amana,kasani ita mai raunice intayi wani abu \ba dadai ba ka sakata a hanya,katuna kai tamkar uwa da ubane a gareta sannan kuma dan uwa da kuma miji,katuna da cewar tamkar rainonta kke,hakika ina alhafahari dakai sameer kuma inshaalahu zakaga dadai a rayuwarka,kaman yanda kataimaki wannan uban mai neman wanda zai taimaka masa"ya fada yana nuna kansa cikin halin jinya,"abbah kadaina fadin haka ciwone kawai bazaka mutuba kadaina fada,yanzunnan zan kaika wajen mlm uwaisu a birni yanzu"sameer ne yake fada cikin rudani dakuma kokarin daga uzairun daga kan gadon da yake,saidai kafin yakai ga daga shi uzairun ya katseshi ta hanyar cemasa,"ahah dawainiyar da kukayi dani a baya ma allah ya muku albarka ya kuma baku kuma mai muku rayuwarku sannan............."yana cikin magana ne tarin yasake sarkakeshi inda jikinsa yasaki yana cigaba da fadan magana wanda sameer baya jin meyake fada har bakinsa yayi shiru ,inda komai na jikinsa ma yatsaya da aiki,rai yayi halinsa(wato gujewa gangar jiki a lokacin da bata tsammata ba,allah ya mu cika da imani a rayuwar mu),lokacin da sameer yaga abinda yake faruwa sai yazamana cewar shima jikinnasa yatsaya da aiki na wucin gadi,kafin yajijjiga mahaifinnasu yanaso ya tabbatar shin dagaskene cewar mahaifinnasu ya rasu ko kuma suma yayi iirin na kwanaki,saidai lokacin daya sake dubawa ya tabbatar da cewar tabbas ya cika,sai yatsinci bakisa dayin kalmar salati a zuciya har ya fito fili sannan ya fara amsa amo dakin,wanda hakanne ya tashi mulaifah a bacci wanda sai a sannan takula da abinda yake faruwa,koda tazo taduba babannata ta tabbatar da abinda yake faruwa,sai kawai yaka tafara dariya tana cewa"shima fa wai yatafi ya barmu ko shima saida yatafi ko"ganin abinda takeyi ba a cikin hankalinta ba yasa sameer yin saurin riketa kafin yafara jijjigata akan da ta dawo cikin hankalinta,saiai koda yafara jijjigat sai kawai yaga ta ja numfashi mai karfi ta ta faadi a gabansa,binta yayi ya rike ta a rude kafin dagabaya ya gane cewar suma tayi,daukarta yayi zuwa dakinta kana daga baya yarubuta sako yabawa jaaruun akan yakai cikin garin domin susan meyake faruwa.
Dasafe jejin ciki yai da mutane domin sallatar maharbi uzairu,bayan an gama dawowa daga binneshi har sannan mulaifah bata farka dags suman datayi ba,mlm uwaisune yakatse tunanin da sameer yayi ta hanyar cewar,"hakika nasan kuna ganin jarabawa a rayuwarku saidai allah yabaku iokn cinta sannan kai kuma allah yabaka ikon amanar da suka bar maka,dama inaso in tambayeka shin zaku dawo cikin garin da zama ko zaku cigaba da zama ne wannan wajen?"ahah shine abinda sameer yace kafin yakara cewar"nagode da abinda kace saidai zamu cigaba da zama anan har zuwa muga yanda allah zai yi damu"dafashi yayi kafin yace"shikenan allah ya tallafah muku"ameeeeen shine abinda yace shima".
Dakin da mulaifah take ciki sameer ya nufa tare da shiga sannnan ya zauna akan gadon da take kwance akai,tsayawa yayi yana kallonta na tsawon wani lokaci tareda tunanin yanda rayuwa take zo mata daya bayan daya,yadade yana kallonta batare da ya kula sanda ta tashiba,sai ji kawai yayi tana cewa" ya sameer menene,ya faru?dagaskene cewa babana ya rasu? inaso kawai ka fadamin dan nafita daga wasi-wasin danake ciki"shiru yayi kafin yace"hakane mulaifah abba yatafi yabarmu saidai muyi masa addu'a shikadai yake bukata a halin yanzu" "uhm nasani zuwa yanzu yakamata nazama mai karfin zuciya idan har inaso nacika duk wani abinda iyayena suka dinga fadamun kafin su tafi su barni dan ba abinda zance sai allah ya jikansu da rahama yabamu ikon yimusu addu'a",ba karamin dadi sameer yajiba dajin abinda mulaifah tace ba saboda kafin ta tashi daga suman da tayi zuciyarsa na cikin fargabar yanda zai fara bata baki da kuma yanayin halin zata shiga,amma yanayin data nuna masa a yanzu yakara masa kwarin gwiwar fara damarar faranta mata matukar yana tare da ita kuma yanada rai da lafiya.
Yaye mayafin dake rufe da rabin jikinta yayi kafin yace,yakamata ki yi wanka sannan kici abinci domin babu komai acikinki tun ranar jiya,kallonsa tayi alamar batason abinda yace kafin kuma tace"ahah sameer kakaini inda aka binne abba namasa addu'a tukunna" "ahah mulaifah saikinci abinci tukunna ko kinaso mufaraa kin bin maganar su tun daga yanzune uhmm? kitashi ki ci abinci tukunna kinji"duk maganar dayake mata yana matane da fuskar lallashi kafin daga baya yariko hannunta tatashi daga kan gadon.Batare da wani bata lokaciba sameer yafara zare kayan dake jikinta da nufin rage mata su saboda yanayin da take ciki,a bangaren mulaifah kuwa hankalintane ya tafi wani wajen na dan lokaci ganin abinda yayannata yake mata,a inda a bangarensa kuwa da ta kalli idonsa ba abinda ta gani dayake nuna mata yanayinsa yasanja a game da abinda yake.
Lokacin daya zo daga rigarta samane mulaifah ta sa hannu ta rike kana tace cikin sansanyar murya"yaaa sameer zan iya dakaina nasamu sauki fah""uhuhm jikinki babu karfi kuma bansan meyasa bakyaso na taimaka miki ba,ko kin manta ne to kisani cewar da sannu namiki alkawarin cike waennan gurbi uku dakika rasa a rayuwarki harma naa dora da daya gurbin dani kadai keda alhalin cika miki shi wato matsayin miji""ahah bahaka nake nufi ba yaya sameer kawai....""kawai me?banason wannan sabon halin na musu mulaifah"ganin yanayinsane yasa ta sakin rigar da ta rike daga hannunsa kafin tace "kayi hakuri yaya sameer karkayi fushi dani"batare daya kulata ba ya cigaba da rigar dake jikinta,kallon idonta yayi dayake rufe kafin ya kai idonsa kan kyakykyawan jikinta da kullum yake rufe acikin tufafinta yau ya fito fili a idonsa,gani shiru bai yi magana yasata bude idonta,saidai dataga idonsa akanta sai tayi saurin rufe idonta tare cewa ciki muryar shagwaba"yaaaayaaa to wankan fah"sai da tayi magana hankalinsa yadawo jikinsa kafin ya dauki farin mayafin dake gefen kayanta yana de jikinta dashi batare daya cire kananan kayanta na cikiba,saida yarakata har gaban bayan gida kafin yace"zaki iya yin wankan da kanki ko kuma na taimakamiki?"saurin jijjiga kai tayi kafin tace zan iya da sauri,murmushi yayi kafin yazuya ya barta abakin bandakin batare da yace komaiba.
Bayan ta fitone ta shiga dakinta inda tasameshi a zaune da kwanon abinci a gabansa,dagowa yayi ya kalleta kafin yace "zoki zauna kici abinci""bansaka kaya ba fah,""ehh nasani ba bukatar jiran hakan cikinki akwai yunwa sosai "ganin bazai bartaba yasata zuwa ta zauna a gabansa,yayinda shikuma ya fara hada abincin a karamin kwano,saida ya gama kafin ya iba yakai bakinta,shiru tayi tana kallonsa saida ya yaske kaiwa kusa da bakita kafin ta bude yasaka mata.Haka yacigaba da ciyar da ita a hankali har ta ci dayawa batare da sun kulaba,saida suka duba kwanonne dukkansu abin yabasu mamaki,inda sukayi sake kallon juna a tare,daukar sauran kayan abincin yayi yahada su waje daya kana yafara bata ruwa shima da kansa,saida tagama cin abincin abu biyu suka bata mamaki sosai,;yanda ya ke mata abubuwa a yau yash banban da yanda yake mata akullum,sai kuma yanda ta sau ciki ta ci abinci dayawa batare da kulaba,maganar sace takatseta da tunaninnata "ki shirya ina jiranki a waje zamuje wajen kabarin su abbah"batare da yaji mezata ce masa ba yafito yabata waje.
Zaune suke a dan nesa da kabarin sun kuramusu ido,inda kowa yayi shiru da abinda yake sakawa a ransa,bangaren mulaifah kam harda hawayenta sannan ta dora kanta a kafadar sameer hannunsu kuma na rike da na juna,mulaifah ce tace"yaya sameer duk sun tafi kamar basu zoba sai tunaninsu dayake zukatanmu,yanzu kaikadai karagemun,kaima dan allah karka tafi ka barni,kabari nafara tafiya nabarka,kaji yaya sameer""kidaina fadin hakan kinji,banason naganki cikin damuwa,saboda dazu kinnuna dauriya shiyasa nabarki kika zo wajennan yanzu,a yanzu haka damuwarki ita kadaice raunina mulaifah,dn tun lokacin da na bude ido a duniyar wannan dajin ba abinda yakasance yana huda zuciiya ta tashi daya sai damuwarki,inso kitayanin cika matsayin dana yiwa abba da ummi alkwarin zan cika a rayuwarki wato,nazama tamkar mahaifiyarki,mahaifinki,yayanki,mijinki,sannan uwa uba masoyinki,inason duk wata kulawa dazan baki karki kasance mai kin bani hadi kai akan hakan saidai idan hakan yakasance yafara cutar dake,duk da ma bana fatan a wannan rayuwar a zo lokacin dazan kasance namiki wani abu dazai kasance ya cutar da rayuwarki,saboda INA SONKI MULAIFAH,INA KAUNARKI SOSAI tun lokacin da kika kasance kina jinyata lokacin dana ke bukatar taimako,dan haka a yanzu nadauki alkawarin kulawa da ruyawr sai inda karfina yakare,burina shine hadin kanki a halin yanzu."tunda yafara magana mulaifah ta tsura masa ido tana jin meyake fito daga bakin mijinnata wanda take jinsa kamar mafarki,saboda yanda abin yazo mata a bazata,kallonsa take cike da mamaki inda daga karshe hawaye yazubo daga idonta batare da dauke kallon dake tsakaninsu ba,shima kallonta yake anasa bangaren kana yace "menene yasameki wani abune yafaru ki fadamin kinji?" "ahah ba abinda yasameni sai mamaki dakuma abinda allah yasake mallakamin a yau,kaman yanda kake bukata zan kasance mai matukar biyayya a gareka a koda yaushe sannan zan kasance mahadin farincikinka dakuma kauracewa duk abinda bakaso,hakika ina alfahari dakai,sannan nagode matuka da kulawarka a gareni sannan dakuma soyayyarka,ni ma inasonka mijina"duk maganar tanayine lokacin da idonsu ke hade da na zuna,inda sameer batare da ya furta ko kalma daya ba bayan bayaninta yasa hannu ya rungumeta acikin jikinsa kamar za'a kwace masa ita daga gareshi.
haka ranar ta karemusu suna tare da juna,cikin san juna dakuma kaunar junansu,bayan darene yayi sun gama abinda zasuyi da wuri saboda yanayin jejinnnasu daya kasance na damina sai yazamo cewar basu zauna a wajeba kaman yanda suka saba,mulaifah ce a dakinta tana sanja kaya zuwa na kwanciya,saikuma tunannin abinda yafaru yadawo mata a ranta ita kadai tafar murmushi wanda lokacin daya hadu yanayin damina sai yakara armashi da yanayin da take ciki,wanda batasan lokacin data fara maganar dake cikin ranta ba yafito fili,tare da cewar"inasonka mijina sosai" "nima inasoki sosai matata"juyawa tayi da sauri dajin amsawar da aka mata a bayanta,murmushi yasakar mata mai taushi dake kan fuskarsa,yayinda itakuma ta tsaya kawai tana kallon sa cikin so da kauna,tako yafara yi tmaku bayan taku cikin nutsuwa izuwa gareta,yayinda itakuma ta tsaya tamkar andasata a wajen,saida yazo tabb da ita kana....................hhhhhhhh fans😍🥰🥰🥰 kubini a chp ta gaba tana zuwa bada dadewa ba.👌👌👌❤️♥️SADI-SAKHNAce❤️♥️(the legendary novelist)🌄🌄🖌️🖌️🖌️
YOU ARE READING
Boyayyiyar Alkarya
MaceraThe legendary story about the mysterious hidden🌄🌄 island the numerous of people and evils fails to find out about it. But find by the unremembered prince 🤴 without his knowing 🤔🤔🤔