(The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟
BOYAYYIYAR ALKARYA(the hidden island )🌄🌄🌄🌄🌄
phone number:09035784150telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0
whatpad :@SAKHNA03
chp(11)
Saida yazo tabb ta ita kana yaja ya tsaya a gabanta,kallo suke ido cikin ido kowa da abinda yake sakawa a cikin ransa,wata tsawa da akayine a garin yasa su zubewa akan gadon mulaifah a tare yayinda mulaifah ta kankameshi saboda razanar da tayi.
Labarinnasu ne yasanja salo inda suka lula sabuwar duniyar da basu taba tsintar kansu a cikiba,a ranar ne suka mai da ruhinsu abu guda, tare da tabbatar wa junansu cewar sun zama abu guda a halin yanzu.
Dasafe sameer ne ya naima musu abin karya yayinda yake ta nan nan da ita tamkar wani zaizo yakwaceta daga wajensa ,abinne yabawa mulaifah mamaki ganin yanda yake bata kulawa tamkar wanda aka haifeta a sannan ,shakuwa ce da soyayya hadi da kauna yakara ruruwa acikin zuciyarsu sosai fiye da tunanin mai tunani,haka rayuwansu yacigaba da tafiya cikin dadi.
Bayan wata
sameer ne yafito daga dakinsu wanda a yanzu suke a sabon dakin da suka sake ginawa suka bar na da dinsu ,saboda yanda yake tuna musu da iyayensu da suka rasa,fitowa sukayi suna tsaye a farfajiyar muhallin su sunyi shiru kamar basu da niyyar magana ,mulaifah ce ta katse shirun ta hanyar cewar "ya sameer da kayi hakuri dazuwa daji yau ni hankalina bai kwanta ba yau da zuwanka daji ,haka kawai yau natsinci kaina da faduwar gaba "takarisa maganar fuskarta dauke da damuwa ,ganin damuwar da tayine yasashi kara matsowa kusa da ita ,yarike fuskarta da hannu biyu ,ya kalli cikin idonta kafin yace"hmmm kidaina irin wannan damuwar nafada miki banason kidinga shiga damuwa saboda hakan na saka ni cikin damuwa ,ki kwantar da hankalinki ki huta kafin nadawo banyarda kiyi aikin komaiba sai kinsami sauki,"shiru tayi itama tana kallonsa kafin tace"uhmm amma kuma ai iya zazzabi nake kuma shima saida daddare,zan iya aikin komai ,sannan inaso ka tabbatar min dazaka dawo da wuri kuma nima da wuri zanyi komai kafin kadawo nagama" "shikenan amman kikula sosai ,karkimin wasa da kanki ,sannan da sannu zan dawo da wuri ,kuma na miki alkawarin yin farautar da ban taba yiba a kwanannan "yafada mata yana murmushi kafin ya matsa daga kusa da ita yazuya domin tafiya,har yafara mata nisa ta kwala masa kira tare da yimasa alamar yajirata tana zuwa,tsayawa yayi a inda yake yayinda itakuma ta zuya dakinsu domin dauko abu,bayan ta shigane ta fito ta makullin da babansu yabawa sameer a hannunta ,har ta iso kusa dashi yana mata kallon alamar tambaya batare da ya ce komaiba ,zuwa tayi kusa dashi kana ta saka masa sarkar a wuyansa fuskarta dauke da murmushi kana tace "kadinga barinta a wuyanka domin tun ranar da abba yabaka kasa a wuya yayi maka kyau sosai ,sannan kuma haka kawai nakeji a jikina gwanda kadinga yawo da ita a wajenka dan tana da muhimmanci sosai ka kasance tare da ita "dauke fuskarsa yayi daga kallonta bayan tagama yimasa bayanin kana yace "gaskiya a da hankalina bai kwanta da ina fita da ita amma zan saka idan har hakan shine ra'ayinki matata "sumbatar gefen kumatunta yayi kafin yajuya yashiga cikin daji ,yayinda itakuma ta tsaya tana kallonsa har ya bacewa ganinta kana ta juya domin komawa gidannasu tana mai sauke ajiyar zuciya tare adduar neman sauki a wajen mai komai mai kowa wato allah.
Tafiya yakeyi acikin daji amma hankalinsa naga matarsa daya baro a gida,wanda shikadai yake murmushi idan yatuna abubuwan dasuke faruwa ,dahaka har ya iso ga ainihin cikin daji ,haka yayi ta zagayawa tare da dubawa kozai samu abinda ajalinsa yake kiransa,haka ya karishi dubansa amma bai hadu da wani abu yayi kama da abin kamawa ba,ganin lokaci na kure masane yasa shi shirin juyawa domin komawa da baya ,saikuma hankalinsa yakai ga wata kada da take yin kiwo a gefen wani rafi ,dana kwari da bakarsa yayi tare da fara shirin afkamata,saikuma zuciyarsa ta tuno masa da alkawarin da yayiwa mulaifah na dawowa da wuri ,sannan kuma da shima alkawarin da yayimata na yin farautar da bai taba yiba a kwanakin sannan din ,ganin bashida mafitar abinda zai dauka a cikin al'amarin sai kawai ya afkawa kadar,domin yana ganin ai idan har ya samu nasarar kama dabbar bazai sha wuyar shawo kan mutumiyar tasa ba ,duk cikin gudun kama kadar yake wannan tunanin ,amma har suka yi nisa da gudun amma bai kama abin harinsa ba ,zuciyarsa ne ya buga tare da sarawar kansa a lokaci daya ,kwakwalwarsane ya tuno masa wani abu kamar,hakan yataba kasancewa da shi a baya ,hankalinsa ne yafara daukewa yayinda kuma gangar jikinsa ya yaudareshi ta hanyar kin tsayawa da gudun da yakeyi ,sanadiyyar tunaninsa daya tafi har takai ga sunzo wajen gangara daga tudun da suke wanda har kadar da yake bi tqbacewa ganinsa batare daya sani ba ,jikinsa ne yatsaya da aiki lokaci daya hakan yajawo sanadiyyar fadawar sa gangaren dake gabansa,inda gangar jikinsa yadinga mirginawa har saida yakai ga kasa ya daki wani dutse.
Saida sameer ya shafe tsawon sa'a ashirin da takwas yana cikin wannan halin kana daga baya yafarfado daga doguwar suman dayayi ,abinda ya fara fitowa daga bakinsa shine "me kuma nake anan wajen ?wannan kayan fah ?"yafada yana kallon kansa da kansa ,ganin duk tambayar dayakeyi babu mai amsa masa ne yasashi tashi daga wajen da yake,tafiya yafara yi batare da yasan inda zai je ba ,saida yayi tafiya mai dan nisa kafin ya iso ga wani dan gari mai matsakaicin girma ,tafiya yakeyi har ya shiga cikin garin ,yana cikin tafiyane yaji wasu daga bayansa suna magana ,juyawa yayi domin ganin meke magana ,amma sai ganin mutanen dake bayansa sun rusuna alamar nuna girma ,nuna daya daga cikinsu yayi tare da yimasa magana "kai nan inane ?me nake a wajennan kuma ?"mutumin da ake tambayarsane yakara sunkuyar dakai kafin yace yallabai banida masaniyar abinda kake tambaya ta ba ,abinda nasani kadai shine nan wani garine dayake arewa da kasar khaisira sannan mu yan kasarne munzo nanne a matsayin fatakai ,shiru yayi yana kallonsa kafin yace "shikenan kubani kaya na sanja sannan da doki inason komawa kasar khaisira a yanzu ""angama ranka ya dade shine abinda suka fada a tare tare da nuna girma ".
Bayan shirya masa kaya da akayi dakuma doki sai yashirya yanufi garin khaisira wanda saida yashafe kwana guda da yini a hanya kafin ya isa ga garin kasar khaisira .
Tun daga hanya mutane suka fara tururuwa domin ganinsa da sukayi tamkqr abin bazata ,abinne yabashi mamaki dakuma haushi ganin yanada kowa ke kallonsa kaman bai sanshiba ciki kuwa harda wanda suka sanshi sosai ,haka yadinga wuce mutane har saida yazo ga farfajiyar fadar khaisira kana yaja linzamin dokinsa yatsaya ,gimbiya jazila ce tafara fitowa kafin sarki shammaz ,da alama yan gulma har sun kai musu labari ,tahowa tayi tarungumeshi cikin dauki dakuma kewa yayinda shima sarki shammaz yake bayansu yana kallon dannasa,ganin abin yayi yawane yanda suke kallonsa ciki da kewarsa yabashi mamaki har yasa shi fadin "wani abune yafarune ?naga kuna ta wannan abin kaman na dade bana gida ?wai me yafarune ?iyeee ?"gimbiya jazila ce ta bude baki zatayi magana sai sarki shammaz yayi saurin katseta ta hanyar cewa "a'a bakomai dana ,mushiga ciki ka huta dan nasan ka gaji sosai "ya karisa maganar yana dafa kafadar dannasa fuskarsa dauke da murmushi .
Bayan gama hidimar da'akayine na dawowar sa yariman kasar khaisira ,wanda shi har a sannan abin yana bashi mamaki ,sai kuma aka natsa dan bashi damar yasamu yahuta ,hanya yamike zuwa sashensa yayinda yake ganin komai tamkar an sanja masa shi,tafiya yake kallon wajen har ya isa ga turakarsa inda yafara rage kayansa domin watsa ruwa ,arba yayi da sarkar dake wuyansa ta cikin madubi ,yayinda yayi saurin kallonta a zahiri kaman wanda aka zubureshi ,kare mata kallo yayi har zai jefa ta wajen shara sai kuma kallin da dutsin yake sai ya dau hankalinsa kawai sai ya jefa a wajen kayansa ,bayan ya shirya ne sai kuma yanemi zoben dake hannunsa shima yarasa ,abinne kuma yafara masa abin tambaya ,akan anya kuwa shine komuma akwai abinda yake faruwa ?.
**** *********************************
Koda kawo nan da al'amarin da yarima samhal yake gani acikin madubi sahir sai hankalinsa yatashi matuka inda yafara saka da warwara azuciyarsa ta hanyar cewa "mulaifah !mulaifah !! mulaifah !!!,shin ba mafarki nakeba kuwa ?kuma al'amarin kamar a gaske dan shaidu sun nuna kansu tuntuni bani da ikon musawa ,indan gaskiya ne kuwa mena aikata kenan ?nabar amanar da'aka bani har tsawon watanni to a wane hali take a yanzu ?sannan da gaskene duk zancen boyayyiyar alkarya da nakeji anayi ,duk suna rataye a kai na a halin yanzu?wannan wane irin al'amarine mai wuyar ganewa ?.
(😊😊😊,yarima samhal na tambayarmu dunkulalliyar rayuwarsa gashi muma bamu da amsa a halin yanzu ,saidai a gaba koda zamu ji amsoshin tambayoyinnasa masu cike da sarkakiya 😀😀🌄🌄👿👿💓💖).
Koda yagama jehowa kansa tambayoyi da shi kansa shima bai amsarsu kuma yasan baizai samu ba ,sai ya ajiye matihul sahir a inda yake tamkar ba'a duba komai a ciki ba ,yajuya da sauri yanu fi kofar dazata sadashi da hanyar fita ,fitarsa bai wani bata lokaciba yakama dokinsa ya hau ,yanufi kasar khaisira da mungun gudu ,wanda babu alamar yada zango a tafiyar tasa .
*******************************
A kasar dhulkam kuwa a sashen jabalul aswad ,wato fadar boka gazaza zaune yake a gaban tukunyar tsafinsa yana keta dariya mai matsanancin amo marar dadin sauraro ,wanda take dauke da mugunta dakuma cin nasara .
Domin kuwa fara kallon rayuwa ta baya da yarima samhal yayi a madubin matihul sahir har izuwa gamawa dadai yake dafara kallon rayuwar da shima boka gazaza yayi a cikin tukunyar tsafinsa .
Sake kecewa da wata dariyar yayi kan yafara cewa "hmmm hakika matakin cikar burina yafara ,domin kuwa abubuwan danasa a gaba da sannu sai nasara nake samu daya bayan daya ,,kayi kuskure yakai maigadin boyayyiyar alkarya da har zakayi tunanin akwai wanda zai kare boyayyiyar alkarya daga gareni ,kai kuma wannan yaro dan karamin alhaki ,hakika rayuwarka da kaddarar ka sun cuceka dahar suka tsoma ka cikin wannan al'amari ,kayi zaman jiran zuwana kanka ,mummunan matakin dazan dauka na tsawon shekaru danayi ina neman boyayyiyar alkarya .hhhhhhhhhhhhhhhhh sai ni boka gazaza ,dan bokanya urai hilwa .
Tohh abinda yafito daga bakin boka gazaza kenan saura kuma muji wane irin hukunci ya ikirarin aikatawa .
Kukasance dani a chapter na gaba danjin mai zai kasance ........💖SADI-SAKHNA 💖🌄🌄(the legendary novelist)🌄🌄👿👿👿.
YOU ARE READING
Boyayyiyar Alkarya
AventuraThe legendary story about the mysterious hidden🌄🌄 island the numerous of people and evils fails to find out about it. But find by the unremembered prince 🤴 without his knowing 🤔🤔🤔