(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)
🌄🌄BOYAYYIYAR ALKARYA🌄🌄(the hidden island)
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
(The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟
BOYAYYIYAR ALKARYA(the hidden island )🌄🌄🌄🌄🌄
chp[13]Kwance yasamu mace mai dauke da cikin da za'a iya haihuwarsa ko yau ko gobe saidai yanayin da mai dauke da cikin take ciki yafi gaban kwatance a fuskr tausayi ,domin kwance take cikin mawuyacin hali tana fidda numfashi daga bayan daya ,ga wane turiri dayake fita akan katon cikin abin gwanin ban tausayi ,koda yarima samhal ya kare mata kallo bai san lokacin da hawaye mai zafi ya gangaro daga ramin idonsa ba ,karisawa yayi tsakiyar dakin cikin sanyin jiki kaman wanda kwai yafashe masa a ciki ,jubewa yayi akan gwiwoyinsa agaban gadon data ke idonsa kuma na kanta ka kiftawa baya yi,jin zaman mutum a kusa da ita yasa mulaifah juyowa dan ganin waye a gabanta ,idonta ne yayi arba da mijinta wanda idanuwanta suka mata rowar ganinsa tsawon wata da watanni ,murmushine ya kubece daga bakin ta ,wanda duk wanda yakalla yasan karfin hali kawai take duba da yanayin da take ciki ,daga hannunta tayi a hankali ta kai ga kan fuskarsa kama hannunnata yayi da hannusa har sannan idonsa na kanta yana zubar da hawaye ,daurewa yayi ganin shirun yayiwa kana yace "menene nake gani haka ,meyasa meki waye ya miki wannan abin ki fadamin kinji !!😥",shiru tayi kafin tafara fadin "ya sameer kasamu nasarar tuna rayuwarka?kana lfy?" "hmmm menene haka mulaifah ina tambayarki menene yasameki a cikinki kekuma kina wata tambaya ko ?inaso ki fadamin abinda yafaru tun daga tafiyata kinji ?",shiru tayi kaman bazata ce komaiba sai kuma tafara bashi abinda yafaru.
******WATANNIN BAYA ,BAYAN TAFIYAR YARIMA SAMHAL DAGA DAJIN SHAGIR*****
Koda mulaifah tagama gyara gidan ,saita hau dora musu abinci ,kaman yanda sukayi da sameer cewar zai dawo da wuri itama tagama aikin daya ke gabanta ,hakan kuwane yafaru bayan tagama aikinta tai wanka sai ta zauna domin jiransa kaman yanda sukayi dashi ,haka tafara bawa yarima samhal abinda yafaru kaman haka:.
Lokacin dana ga rana tana shirin faduwa baka dawoba sai hankalina yatashi sosai inda muka shiga daji nemanka nida jaaruun ,munyi tafiya mai amma bamu sameka ba ,haka muka dawo muka kwanta a bakin daki muna jiranka akan inka dawo katasheni ,amma ganin har gari yawaye banga kaba sai hakan yatabbatarmin baka dawo gidaba ,nashiga damuwa sosai ga kuma zazzabi da amai danake fama dashi wanda yafi nada zafi sanadiyyar tashin hankalin dana shiga dakuma yawon da mukayi da jaaruun a cikin jeji.
Haka kwanaki da watanni suka shude tun ina jiran dawowarka har nafara cire rai da ganinka,abinda yafi dagamin hankali na shine kar wani abune ya cinye ka a jeji ,amma daga baya danayi tunanin cewar kai tamkar bakone a rayuwa tabiyu a koda yaushe zaka iya tuna rayuwarka ka tafi kabarni sai hakan ya fara sakamin dangana acikin zuciyata ,saidai zuciyata ta fidda rai da samun wani dadi a cikinta.
Bayan wasu watanni ne nafara ganin canji ajikina cikina yana girma bakaman yanda yake ba ,sai hankalina yatashi daga baya ne kuma daya fara motsi lokaci bayan lokaci sai nalura da cewar da ne a kwance a cikina ,lokaci daya zuciyata ta cika da farin cikin zan samu wanda zamu rayu dashi nima bazan zauna nikadai ba ,kuma zuciyata tabani cewar baka tafi ka barni gabadaya ba ,kabarmin abinda zan dinga tunawa dakai.
Haka nacigaba da rainon cikina ,wanda sanadinsa walwala ta tafara dawowa musamman idan naji yana motsi a cikina ,rayuwarmu ta dawo mu biyu ,daga ni sai jaaruun ,saikuma dan cikina da bai fito duniya ba ,saidai farin cikin dana fara samu shima yazo yagushe wata daya daya wuce,sanadiyyar wani abu daya faru.
Domin kuwa abinda ya faru wata rana ina kwance da daddare sainaji motsi dama kuma nika dai ce jaaruun yafita bai dawo ba ,wanda hakan yamin dadi ,nasan da mutanen dasuka zo sun yi arba dashi ,dasun kasheshi ,ina kan gado naga wani mutum mai bakin kaya ya shigo ya jani da karfi zuwa waje ,gaban wani mutumi ma'abocin bakin kwarjini da kuma bakin kaya,tambayata yafayi akan nasan inda boyayyiyar alkarya take ?inda yayi ikirarin idan ban fadaba zai kasheni ,shiru nayi ban masa maganaba ,wanda saida yasa wuka yafara yanka jikina ,nace masa bansan inda take ba ,kama fuskata yayi yaduba idona wai ko da gaske nake ko akasin hakan ,ganin dagaske ne abinda nafada masa ,yasashi jefar dani akasa ,kara nayi sanadiyyar ciwon danaji a cikina ,wanda har yafara tafiya yadawo da baya ,tare da cewar"bari nabar miki sako game da mijinki nasan tunda ya tuna rayuwar dayayi dake a halin yanzu to tabbas a kowane lokaci zai iya zuwa gareki"diban kasa yayi a kasa yafara wani surutu a jiki kafin ya hurata ackina ,wani irin azababben zafine ya jiyarci cikina tareda wani irin kullewa ,wani irin kara nasaka ,yayinda shikuma ya sheke da dariya tare da fadin cewar "da sannu zai dawo gareki inaso ki fada masa cewar ,nidashi dole muna neman boyayyiyar alkarya ,domin wannan bakin zafin dayake jikinki a yanzu bazai taba barin jikinki ba har sai a samo ruwa boyayyiyar alkarya ,idan kuwa ba hakaba daga sanda kika fara nakuda ba ayi nasarar magance shiba ,to zaku bakunci lahira keda abinda yake cikinki ,yanzu zan gani shin zai iya bari ki mutu ko kuma zai bada rayukan mutane domin ceto naki ran ".
Bayan tafiyasu ne naja dakyar na shiga daki wanda tun daga wannan ranar bana iya komai sai jaaruun ne yake kawomin ruwa dakuma yayan itatuwa ,wanda su suka kasance abincina har kawo yanzu .
Nayi farinciki da ganin cewa kana raye kuma raina yatabbatarmin ka tuna rayuwarka ta ,da a baya kazo zanyi farincikn ganinka ,ya sameer amma yanzu bana farinciki da hakan ,saboda naso kar wancan mutumin yayi nasara a kanmu har ka ganni a wannan yanayin ,naso kazo bayan na tafi inda iyayena sukaje ,saboda nasan a yanda nake bana saka rai da rayuwa ,sannan ina tsoron wane hukunci zaka yanke ,ina tsoron kazabeni akan mutane kaman yanda wancan mutumin yafada "tun farkon da mulaifah tafara bawa yarima samhal abinda yafaru ya kuka har zuwa sanda ta gama ,jin tayi shirune yasashi dagowa kafin yace "bancika d'a ba kaman yanda baba yake tunanin zanyi ba ,ban rike amanar da'aka baniba ,ina rokon afuwarki mulaifah akan hakan ,tabbas naji kunyar kaina ,kaicona da wannan abu dana aikata ,","ahah ya sameer kadaina fadin haka ,karka manata duk zaman dakayi damu ,dama ba acikin ainihin tunaninka kke ba ,sannan hakan kaddara tace na karbeta hannu biyu ,kadaina damuwa akan hakan ,ko a yanzu allah ya karbi raina zan kasance cikin farin ciki sosai ","ahah karki sake fadin hakan dasannu zaki samu lfy wahalar da kikayi zai kasance tahiri ,koda ba wanda yataba shiga boyayyiyar alkarya to tabbas zan shiga kuma na nemo miki magani "jijjiga kai tafara yi tare da fadin "ahah ya sameer karka bude boyayyiyar alkarya saboda raina daya ,yazo yayi sanadin ran mutane da yawa indai sadaukar da raine akan wannan wurin ba akaina aka fara yiba ,kar ka manta mahaifiyata ma tayi ,kamanta dani kafara sabuwar rayuwarka sannan ..............."bai bari ta karisa ba yakatseta ta hanyar cewa1"kibar wannan zancen ,domin bazan taba barki cikin wannan yanayinba sai inda karfina ya kare ,sannan lokaci yayi dazamuyi fito na fito da dukkan wasu miyagu akan boyayyiyar alkarya ,saboda kawar dasu daga kanta "batare da yabarta ta sake magana ba ,ya dauketa ya fito da ita daga cikin dakin yanufi waje da ita .
Fahsir suna tsaye shida jaaruun a waje suka ga yarima samhal yafito da mace a hannunsa ,karisa wa kusa da su fahsir yayi fuskarsa1dauke da mamakin abinda yagani ,wanda har yama kasa magana ,sai bin yarima samhal kawai da yayi a baya ,tafiya sukeyi yana gaba dauke da mulaifah a hannusa ,yayinda fahsir dakuma jaaruun suke biye dashi har suka kai ga masaukin su da suka kafa da farko ,yana zuwa bai bata lokaciba yasamu shimfida ya kwantar da mulaifah akai ,kana yajuya yayiwa fahsir magana "fahsir yakamata mu juya gida a yau domin mulaifah tana bukatar taimako gaggawa dan haka bamu da lokacin dazamu bata a yanzu ,"mamakine ya bayyana a fuskar fahsir kana yace ,"wai wannan wajen inane ?sannan wannan matar wacece ?iyeee ?" "wannan wajen shine inda na zauna lokacin da hankalina yagushe a baya sannan wannan matar da kake gani matata ce ,kaji amsarka ?to shirya mu tafi dan akwai matsala rashin komawar mu dawuri ".
Shiryawa suka yi kana suka kama hanyar kasar khaisira ,yarima samhal ne ya saka mulaifah a gabansa inda suke tafiya cikin nutsuwa da kulawa saboda halin da take ciki ,yayinda jaaruun kuma suka barshi a dajin shajir ,domin hasashen dawowa.
Lokaci mai tsawo suka dauka kafin suka iso ga kasar khaisira ,tundaga bakin kofa aka fara hura kaho wanda yatabbatarwa sauran dakaru wanda ake nema daya gudu yadawo ,
kafin isarsu bakin fadar har wajen yacika da mutanen fada ,harma da sarki ,wanda ransa yake matukar bace tun lokacin da yarima ya fita daga cikin masarauta,kowa yazo da gulma domin suga hukuncin da za'a yanke ,tsaye suke a bakin fada har lokacin da yarima samhal da fahsir suka iso bakin kofa ,cikin fahsir ne yaduri ruwa jikinsa sai rawa yake domin karbar hukuncinsa ,a inda a bangaren samhal kuwa sauka yayi a hankali kana ya riko mulaifah daga kan dokinsa ,kana yadauketa ya nufi kofar shiga cikin masarauta da ita a hannunsa ,tsayawa yayi a gaban mahaifinsa kafin yace "ina rokonka yafiya akan fita danayi bayan kuma ka haneni da fitar ,bazan kasance mai rokon ka jikaina ba a wannan lokacin ,a shirye nake da karbar duk hukuncin dazaka yimin saidai a yanzu ina rokon alfarmar ka na bawa wannan baiwar allah taimakon a cikin garinka saboda halin da take ciki"koda yagama bayaninsa sai yayi shiru domin yaji abinda mahaifinsa zai ce ,"zan karbi alfarmar ka na bata taimako amma sai ka fadamin wacece sannan menene yasameta ?" "nayi alkwarin fadawa kowa wacece wannan dakuma abinda yasameta ,amma da farko tana bukatar taimako daga wajen wannan masarauta,kuma .......................bai karisa maganarsa ba takatse sakamakon wani kara da mulaifah tayi,wanda yafirgita dukka mutanen dasuke kusa dasu ,ganin halin da ta shigane yasa yarima samhal yin cikin gidan batare daya jira abinda mahaifinnasa zai ceba ,bai zarce ko ina da itaba sai dakin bada taimako wanda iya jinin sarauta ake dubawa a wajen ,shimfida ta yayi akan gadon jinyar yayinda masu kulada marasa lafiyar suka rufu a akanta danganin sun baje filahimtarsu dan ceto rayuwarta ,cikin sauri gami da gaggawa suke komai a wajen yayinda shima yarima samhal ya shiga ake damawa dashi saidai duk da haka hakar su ta gaza cimma,domin turirin dake fita daga jikin mulaifah ba kasa yayi ba ,saima karuwa da yake yi wanda duk wanda yaganta sai ya tausaya mata domin halin data ke ciki,bayan wani lokacine sai kuma jikinta ya saki kaman wanda aka zare duk wani motsi na jikin ta ,gyara mata kwanciya sukayi cikin wani akwati wanda ake ganin komai daga waje mai hanyoyin iska da magani kafin yarima samhal yasamu fitowa daga wajen .
A bakin kofar wucewa sashensa suka ci karo da iyayensa wanda suka zuba masa ido alamar tambaya ,shiru yayi yana sosa keya ,saida mahaifinnasa yayi magana kafin yadago kansa ,"me kke nufi da abinda ka aikata ?inaso kamin bayanin me yake faruwa yanzunnan " "kayi hakuri abba kaman yanda nafada dasannu zan bada labarin abinda yake faruwa bama ga ku kadaiba harma da mutanen nahiyar gabaki daya ,inshaallah gobe a fadar khaisira"har mahaifinsa yabude baki zai yi magana saikuma gimbiya jazila ta katseshi ta hanyar cewar "shikenan zamu baka damar yau da gobe kaman yanda ka bukata muna jiran bayaninka a goben ,kuma kaman yanda ka bukata kowa zai hallara danjin mai kake tafe dashi ,saidai ka tanadi abin fadi mai amfani dan kwanannan ban yadda da hankalinka ba sam "tana gama fadin haka tabar gun yayinda shima sarki shammaz dogaransa suka take masa baya zuwa fada ,bayan tafiyarsune yarima samhal yaza ajiyar zuciya kafin yace "allah ya kaimu".
Washagari da safe bayan kowa yafara harkarsa inda kowa yake shiri domin tafiya fada danjin mai zai fito daga bakinsa ,bayan hallarar kowa a wajen da aka tanada domin sauraron jawabin ,saikuma akayi shiru domin isowar sarki da kuma iyalansa ,sarewa ce ta fara isowa kafin kuma sarki shima ya bayyano cikin kayan alfarma da kasaita ,hayaniyar mutane ce ta kaure dayin arba da adalin sarkinnasu ,wanda saida yazaunane kuma guri ya lafa aka fara jiran jawabin dazai fito daga bakin yarima samhal ,yarima samhal ne yataso daga wajen dayake zaune kafin yakarisa zuwa wajen da aka tanada domin yin magana ,sanye yake shima da kaya na alfarma yayinda kowa yayi shiru hankalinsa yana gareshi domin jin mai zai fito daga bakinsa.
Saida yadaga kai ya karewa daukacin jama'ar wajen kallo kafin yafara da fadin cewa .....................
Gashi nadauko rubutun alkalami ya karye kutara dani agaba danjin yanda zata kaya a jawabin na yarima samhal .
kar ku manta tare kuke da...SADI-SAKHNA (the legendary novelist )
YOU ARE READING
Boyayyiyar Alkarya
AdventureThe legendary story about the mysterious hidden🌄🌄 island the numerous of people and evils fails to find out about it. But find by the unremembered prince 🤴 without his knowing 🤔🤔🤔