Chapter 6

56 10 1
                                    

(The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟
               
  BOYAYYIYAR ALKARYA(the hidden island )🌄🌄🌄🌄🌄
 
phone number:09035784150

telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

whatpad :@SAKHNA03
   
    [06]

    Juyawa sukayi a firgice domin ganin meyake2 gurnani a bayansu ,ganin wani irin hallita da sukayine wanda baikai kuraba amma kuma yafi kare yanayin firgita ,yasa sameer tashi a firgice domin neman abinda zai kare kansa .koda yazuya ga mulaifah sai yaga bata nuna alamar razana ba saima tsayawa da tayi tana kallon halittar ,bai gama mamakin hakanba ya tsinci muryar ta tanama hallitar magana ."ya isa haka ba abinda zai faru ,kar kamasa komai bakon mune sannan kuma yazama dan gida a halin yanzu "jin abinda ta fadane yasa halittar juyawa izuwa ainihin siffarta wanda a sannan ne yakula da cewa kyerkyacine amma ya girma sosai ,tafiya yayi izuwa gare ta yana shafa kansa a jikinta ,ganin hakanne yasa sameer sauke ajiyar zuciya kana ya matsa kusa dasu domin karewa halittar kallo .Dagowa tayi ta kalli sameer kana tace "ya sameer wannan shine JAARUUN ,mai tsaro ,aboki dakuma daya daga cikin danginmu ,jaaruun nada amfani dayawa a rayuwar mu harma da wani amfanin wanda ni bansaniba saidai naji mahaifina yafada ,yayi tafiya tsawon sati biyu shiyasa baka ganshi ba ",har mulaifah tagama bayaninta shadai sameer yanajinta sannan kuma idonshi nakan jaaruun ,cike da mamakin yanayin halittarsa .Ganin lokaci yaja ne yasa su juyowa gida,inda bayan sun dawone maharbi uzairu ya umarci sameer yafada massa ko yana da bukatar zama dasu a ckin dajin kokuma zai je izuwa cikin2gari ?batare da bata lokaciba sameer ya amince da zama tare dasu a dajin na shajir ,inda hakan yayima iyalan dadi matuka ,babu ma ya mulaifah da hakan yafimata dadi sosai ,haka rayuwannasu ta cigaba da tafiya a cikin dajin na shajir cikin farin ciki da kaunar juna .
      *BAYAN WASU WATANNI* 

Kyakykyawan jarumine idona ya hango cikin kayan fata da suka amshi kakkarfan jikinshi ,yana gudu cikin zafin nama dakuma kwarewa ,a bayansa kuma kadan kyerkyacine (wolf )yake binsa shima da gudu ,saida suka kai ga harabar gidannasu kafin sukaja birki a gaban mulaifah .saida na matso kusane nakula da cewa ashe sameer ne ya juye har na kasa ganeshi da farko; ,saida mulaifah ta k'aare musu kallo cikin murmushi nadan wani lokaci kafin ta ce "eehhh tohhh kayi kokari wannan lokacin dan a yanzu ka zarce jaaruun da tsawon dakika daya a bangaren gudu ,to yanzu sai farauta gobe zamuga shin mai zaka kamo da zai sake nunamin bajintarka ,"kallanta kawai yake yi dayanayin datake magana dakuma muryar ta, hakika yatafi da dukkan hankalinsa, inda har ta gama bayaninta baisan takai karsheba ,saida ta gama maganar takula da inda ta yake kallo ,ya tsura mata ido baya koda motsawa tamkar wanda aka zarewa rai ,hura mishi iska tayi a fuska ,wanda yaji tamkar andagashi sama yana yawo a cikin gajimare .murmushin tane ya dawo da shi daga gajeren mafarkin daya tafi ,kana tace "ya sameer me kke tunani ne haka ,bayan kasan cewar abba ya hanaka yawan tunani hakan zai iya cutar da zuciyarka "bayan ta gama maganarta ne tajuya dan shiga ,amma sai ta jiyo muryarsa yana magana ,wanda batayi tsammanin zaibata amsaba ,domin a dan kwanakin bayasan yi mata magana saidai tuk abinda tafada masa ,zai tashi ya aikata idan yanada ra'ayi batare da ya tamka ba ,wanda hakan yana damunta ,domin tun lokacin dasuka fara shakuwa dashi ,ba abinda yake sakata cikin farinciki daya wuce ta ganshi cikin farinciki da kuma annashuwa ,"nagodee da kulawarki kanwata hakika zan kiyaye hakan idan yakasance abinda kike bukata kenan "juyawa tayi takalleshi da jin dadin abinda yafada ,wanda harsaida yaga hakan akan fuskarta ,kafin ta gyada masa kai alamar taji ,sannan ta juya cikin gidannasu ,har takai ga wajen dasuke zama domin cin abinci ,amma kwatakwata hankalinta naga tunanin yayannata sameer ,zaman da tayi ne na tsawon lokaci tana tunani batare da ta motsa wani gaba na jikinta bane ,har ya kai ga mahaifiyarta ta kula da yanayin da ta shiga ,wanda ita bata kula da kallon da mahaifiyar ta ta ,ta ke mata ba ,a bangaren mulaifah kuwa yanayin datake tsintar kanta a wannan kwanakin yana bata mamaki matuka ,domin halayyarta yasanza sosai wanda har take tunanin ko wani abune yasameta .
Bayan sun gama cin abincinsune kowa yanufi dakinsa ko akwai abinda zai yi na rayuwar yau da kullum kafin sukai ga kwanciya ,sameer ne a zaune akan dardumar da take shimfide a tsakar dakinsa yana tunanin da bashida mafita ,domin duk lokacin da ya fara tunanin waye shi ko yanason ya tuno abinda ya shafi rayuwarsa ta baya ,sai yaji kamar ansaka kofa anrufe cikin kansa sannan kuma kansa sai ya dauki ciwo mai matsanancin zafi ,yanzun ma hakanne yafaru dashi daya fara tunanin ,saidai kafin yakai ga yimasa illah kaman koyaushe sai kuma tunanin mulaifah yashigo cikin kansa lokacin datake cemasa yadaina tunani hakan zai'iya cutar da shi ,sannan kuma da alkwarin da yayi mata akan da sannu zai daina ,murmushi yayi tare da jijjiga kai lokacin daya tuno sanda take masa magana a cikin daji dazu ,wanda haka kawai tunowar dayayi yasashi yin murmushi .ganin tunanin bazai kaishi bane ,yasashi tashi izuwa ga gaban tagar dakin yana kallon farin wata daya yayi haske sosai har takai ga ya haskaka dukkan ilahirin sansanin nasu ,abinne yabashi sha'awa matuka inda yaga kallon bazai isheshi daga daki ba ,hakan yasashi yanke shawarar fita wajen domin shan iskar tadake kadawa a hankali saboda hasken watan da yakai ga matakin girmansa ,bayan yafitane yana karewa sama kallo ,ganin yadda taurari  suke walwali a sama dakuma yanayin hasken da wajen yayi ,yasashi shagala da kallon wajen ,har idonsa yai arba da ta wata mace a zaune tana zuya bayanta daga gareshi ,gashinta baki ya zuba a bayan ta ,inda yasamu masauki akan farin kayan dake jikinta wanda hakan yasa mai kallo yake hangowa kalar bakin gashin koda daga nesane ,mamaki ne kamashi akan shin wace ce da daddare a wannan wajen ,karisa wa yayi hankali har ya isa tabbb da bayanta ,kafin yai gyaran murya ,zuyowa tayi a tsorace dan ganin waye a bayanta wanda hakan yakara fito da girman idonta dasuke dauko hasken wata ta cikinsu ,bakaramin mamaki ne yakamashiba daganin mulaifah ce ba kowaba ,amma shin dama tana sanya irin wannan kayan ?shine tambayar dayayiwa kansa ,ganin da mulaifa tayi na yatsaya ya tafi tunani kaman bashine kuma ya mata gyaran murya ba,sai tayi murmushi domin tasan hakan kaman halinsane rashin magana ,katse shirun tayi ta hanyar yimasa magana "ya sameer bakayi bacci bane ?" "ehhh "shine kawai amsar daya bata kafin yasamu wajen dan nesa da gefenta ya zauna ,ya kara kallon ta a karo nabiyu da mamakin shigarta na farar doguwar riga wanda ta haska a cikin ta tamkar itace farin watan ,kasa boye mamakinsa yayi kawai ya tambayeta "shin dama kina saka irin wannan kayan ?idan hakane to meyasa kike saka na fata kuma ? Sannan me kikeyi anan bayan kowa yana daki ?"Juyawa tayi tana kallon sa har yagama tambayar sa kafin taja numfashi sannan tace "ehh ina sakawa amma nafi sakawa da daddare ko kuma inzamu shiga cikin gari ,amma tun lokacin bayan rasuwar yayana sai yau nasaka ,kayan fata kuma umarnin mahaifina ne tun ina yarinya su nake sakawa sannan sukadai ya amincemin sakawa da rana ko idan zan shiga cikin daji ,zamana a wajennan kuwa dama mun saba da zama da dan uwana ,domin iyayena basa zaman hira bayan angama abinda za'ayi na ranar har takai ga anshiga daki ,amma nida dan'uwana muna fitowa muyi ta hira har saimunji bacci mu shiga daki .A yauma abinda yasa nafito lura nayi da yanda farin wata yayi haske da kuma iskar da take kadawa a jejin ,amma tun bayan rashin sa nadauki hararmu a matsayin tarihi ,"haka takai ga karisa maganarta idonta na cike da hawaye ganin hakanne yasa sameer fadin "kiyi hakuri ban tambayeki dan na bata miki rai ba ,hasalima bansan hakan zai tuno da mutuwar dan uwanki ba ,amma nayi miki alkwarin hakan bazai kara faruwa ba da yardar allah ,ki daina kuka banasan sake ganin ki a wannan yanayin ,duk da nasan abin akwai wahala domin rashin dan uwa abine da yake da wuyar gogewa a rayuwa amma inason kisa tawakalli a zuciyarki kinji "daga kai tafara yi da sauri tana kallonsa alamar taji abinda yace kuma da sannu zatayi aiki dashi ,kallanta shima yake yi kafin yayi murmushi sannan yace mata "idan har kina shiga cikin damuwa ko kina kuka to bazan zama yayankiba ,ko bakison namaye miki gurbinsa ?"kallonsa take ganin yanda yasake da ita a yanzu ,murmushin itama tayi kafin tace "zanfi kowa farinciki idan hakan takasance sannan kuma zanyi kokarin daina shiga duk wata damuwa idan har hakan shine babban sanadin dazai kaina ga samun sabon yaya a tare dani ""shikenan wannan shine ka'idarki daga yanzu zan dinga gani idan har kika cigaba da shiga damuwa to zan tafi nabarki ke daya ,kin aminci ?"bayan ya tambayeta ne kana kuma yamika mata hannunsa domin su kulla idan tayarda da abinda yace ,hannunta itama takai cikin jin dadin abinda yake matasuka, bayan sun kulla ne ya kalleta kana yace "kanwata yakamata kije ki kwanta dare yafarayi ,yanada kyau kisamu ishashshen bacci domin hakan nada amfani ga rayuwar dan'adam "bataso tashi yanzuba duba da yanda hirar tasu take tafiya cikin jin dadi ,saidai kuma bazata iya masa musu ba da maganarsa ba hakan yasata mike sannan tayimasa saida safe ,saida tajuya har zata shiga sansanin su sai kuma ta juyo ta kalleshi ,murmushi tayi kafin tace "ya sameer kaima fah yakamata ka kwanta domin kana bukatar hutu sosai ,sannan a yanda na kula jikinka baya bukatar sanyi sosai ,kuma naga wajen yafara sanyi sosai "tun lokacin da ta tashi zatatafi yake kallon ta dayan ta doguwar rigar tayi mata kyau tana binta a baya ,har sanda ta tsaya tana masa magana duk idonsa na kanta ,saida tagama magarne ya juya da kallonsa inda yake zaune kafin yace "shikenan nima yanzu zan tashi dama ,kije ki kwanta yanzu nima zan tafi ,saida safe ki kwanta cikin farinciki "yana maganrne yana tashi daga inda yake zaune ,har ya nufi inda turakarsa take ,yazuya ya kalleta yana bye bye ,kana itama ta yimasa bye bye ta wuce nata dakin .
ASUBA TA GARI SAMEER DA MULAIFAH ..
    Tun lokacin da mulaifah da kulla shiri da yayannata sai yazamana bata da wani lokaci datake zama ma bare har tayi tunanin dazai sakata cikin damuwa ,a inda tawani bangaren kuma yayannata ya sauya mata gabadaya ba kaman yanda tasanshiba a kwanakin baya .Rayuwa suke cikin farin ciki inda hatta tsakanin sameer da jaruunn yazama shakuwa ta shiga sosai duk inda suke zaka gansu tare su uku ko yaushe .Zama sukayi suna wasa cikin nishadi wanda a yanzu kuma jaaruun ne yake bin mulaifah sai ya karbi gyalen hannunta ita kuma taki bashi ,suna ta gudu yayinda shikuma sameer ya shagalta da kallonsu ,har takai ga salma (umminsu )tana musu magana amma kwatakwata hankalinsu baya kan maganar datake musu ,dan sosai yanayin yake sakasu nishadi matuka ,ganin basu jinta ne yasa itama ta tsaya tana kallonsu domin taga sunajin dadin yanayin dukkansu ,bayan dan wani lokacine sameer ya kula da umminnasu a tsaye a wajen sannan ya juyo da sauri yana mata barka da aiki dakuma yamma ,amsa masa tayi kana tace "gaskiya dana kai alkhairi ne a rayuwar mulaifah ,ba abinda zance maka sai allah yasaka maka da alkhairi domin zuwanka rayuwarmu yacanza abubuwa da dama a rayuwar mu ,mun gode daka daukemu tamkar yan uwanka "  "ahah ummi nine yakamata nagodee muku da sabuwar rayuwar dakuka bani ,bayan bakusan daga inda nakeba ,hakika nine da godiya akan hakan ","shikenan dannan yanzu dai inason kudaibo min ruwane a rafin gefe damu ,kuma naga wancan basusan ma dazuwa na wajen ba "tafada tana nuna mulaifah wanda hankalinta duk yana kan jaaruun ,bayan barinta salma daga wajenne sameer ya tsaida mulaifah daga wasannasu kafin ya fada sakon dazasu je ,amsa masa kawai tayi kafin suka kama hanyar rafin .tafiya sukeyi mulaifah da jaaruun na gaba yayinda sameer kuma yake baya yana kallonsu ,tabbas koshi kansa idan ya kalli mulaifah a kwanakinnan yasan tasanja sosai bakaman yanda yasanta a kwanakin baya ba ,yana tunani bai saniba har yana kokarin wuce kwanar rafin dasu mulaifah suka shiga ,dariya mulaifah ta tsaya tanayi masa ganin ya wuce inda zasu deba ruwan ,kana tace "ya sameer me kke kallone a gabanka har ka wuce kwanar wajen diban ruwan ",saida ya kula da abinda yayine shima sannan ya juyo izuwa wajen da suke .To haka takasance a wajen diban ruwan ma ba abunda sukazo yi wajen sukeya ba ,domin mulaifah shigewa ruwan tayi tana tana tsokanar jaaruun ,ganin abinnnasu yaki karewa ne yasa sameer fadin "mulaifah bakya ganin ruwannan zai sakaki mura ne ,?kwanannan naga kin sauya sosai " " ehh ya sameer ,kashigo da kafarka kana tafiya a ciki akwai dadi sosai "  "ahah kuyi abinku ni na ......kafin yakai ga karisawa ne yaji ruwa a jikinsa ,dagowa yayi da sauri ya na kallonta ,yayinda ita kuma ta shagala dayi masa dariya ganin yanda yake kallonta kaman anyiwa yaro laifi ,"ya sameer karama idan ka kamani "tana gama fadi ta zuya da gudu cikin dajin ,inda shikuma yabita abaya ,a hanyar gudunnatane shima jaaruun ya kwace gyalen dake hannunta ,sai ya zamana ta manta da binta da sameer yakeyi ,itama tafara bin jaaruun don karbar abinta daya karba ,gudu sukeyi dukka su ukun ,inda basu ankara ba sai ganinsu sukayi a wani waje da tun a tarihi basu taba tsintar kansu a waje makamancinsa ba, wajene  daya ............tikkkkkk ,daga marubuciyar taku 😊...

ku hadu dani a gaba danjin yazata kaya a wajen da suka tsinci kansu ..

BOYAYYAR ALKARYA( the hidden island ):written by 💝SADI ~SAKHNA 💝

Boyayyiyar AlkaryaWhere stories live. Discover now