Chapter 5

56 9 1
                                    

(The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟

BOYAYYIYAR ALKARYA(the hidden island )🌄🌄🌄🌄🌄

phone number:09035784150

telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

whatpad :@SAKHNA03

chp[05]
*** mafarin labarin yarima samhal a game da boyayyar rayuwarsa .***
YARIMA SAMHAL ne cikin shiga ta alfarma amma wanda suke kamada kayan fita irin karamar farautar nan da masu mulki ke zuwa ,hakika matashin jarumin ya hadu matuka ta fuskar bajinta dakuma zati,inda dakarun dasuka take masa baya suka fito da ainihin kwarjininsa.Dajin dayake yamma da kasar khaisira suka nufa cikin gudu a kan dawakansu domin aiwatar da abinda suka fito dominsa ,bayan tafiya mai dan tsayine suka yada zango domin hutawa kana kuma suka kutsa cikin dajin domin yin farauta .sun dauki tsawon sa'a biyu amma ba wani naman daji da yagifta ta ganinsu a dajin ,bayan wasu dakika ne sukayi arba da wata kada a gefe dasu kadan tana gewayawa ,wani badakare ne ya zabura domin kaimata mashin dake hannunsa ,amma cikin zafin nama kafin yakai ga soketa yarima samhal ya dakatar dashi tare da alamar cewar shi zaije izuwa gareta ,bayan ya fara sassarfa izuwa garetane yajuyo kana yace musu ,"kar ku biyoni ina son nakamata da gudune bawai da makamai ba kujirani domin yau inajin sha'awar yin gudu "koda rufe bakinsa sai zura da gudu ya nufe cikin zafin nama ,a inda itama ta arta a na kare ,sai da suka shafe kimanin tsawon wani lokaci amma yarima samhal yakasa cimmata yayinda itakuma takasa tserewa daga gareshi .Tafiya mai nisa sukayi wanda har yakaishi ga bacewa daga dakarunsa ,duk wannan nisa dasukayi yarima samhal baisan dashiba domin burinsa yakai ga abin harinsa ,gudu suke harsuka kai ga wani tsauni wanda har suka kare tsayinsa har suka kai ga karshen sa ,ganin ba mafitane yasa kadar yin tsalle domin gujewa daga gareshi ,a inda shikuma yariga da yabada karfinsa a karshen dutsen ,wanda hakan yasashi fadawa kasa ,tun yana bugar bishiyoyi yanaji har yakai ga hankalinsa ya gushe lokacin ya iso ga kasa .
Kyakykyawar budurawace da bazata wuce shekara sha tara a duniya ba ,tafito daga wata bukka wacce take gefe da wasu bukkoki guda biyu da suke kewaye da sansanin wajen ,dayake zagaye da dangar jima.wajene da aka gyarashi wanda duk mai kallo zai san cewa wajen yafita daban a cikin dajin.
Saanye take da kayan fata dasuka amshi jikinta matuka ,wanda suka haska akan fatarta dakuma madaidaicin jikinta da ya cika duk wani abu da'ake bukata a wajen ya' mace ,saida tagama juyi tare da mika sannan tayi salati ,yanayin da fuskarta ya nuna wanda shi ba annuri ba sannan kuma ba bakin cikiba ya bani tabbacin cewa watakil daga bacci ta tashi, MULAIFAH kenan ya' ga maharbi UZAIRU dakuma mahaifiyarta SALMA wanda suka kasance suna rayuwa a dajin SHAJIR wanda yake dauke manyan bishiyoyi da kuma kyawun yanayi .Tafiya take cikin nutsuwa dakuma sanyi sannan ta tsugunna a gaban mahaifiyarta wato salma ta gaisheta cikin nutsuwa ,wanda hakan ya kasance dabi'arta ne ,saida ta amsa mata itama cikin fara'a sannan mulaifah ta kalli ummanta kana tace "umma tun safe abba bai dawo bane ?gashi har nayi bacci na tashi amma banganshi ba ?",saida salma ta daga kai tadubi ya'r ta ta kafin tace "hakika nima nashi damuwa domin bai saba kaiwa marece ba a wajen farauta amma yau kam har yanzu bai dawo ba "suna cikin tattaunawa ne a game da rashin dawowar maharbi uzairunne ,sai gashi yadawo ,dukkansu daga kai sukayi suna kallonsa domin ganin me nene a tare dashi ,bakomai yasasu shiga mamakiba illah kallonsa dasukayi da gawa a kafadarsa.Saida yasamu waje a harabar sansanin nasu kafin ya shimfida mutumin dayake dauke dashi,kana ya daga kai ya kalli mulaifah sannan yamata alama da ta mikomasa salgar sa (butar da mafarauta ko mutanen da suke amfani da ita wajen diban ruwa domin yin tafiya dashi )bayan ta mikomasane ya zuba ruwan cikin salgar a kasko sannan yazuba wani magani a ciki ,yasha a dukkan ilahirin jinkin mutumin ,bayan wasu lokutane dashafa maganin jikinsa yafara rawa wanda hakan ya tabbatar wamaharbi uzairu cewar akwai sauran numfashi a jikinsa ,saida yagama gyara wani wurare a jinkinsa kana ya dauke shi izuwa dakinsa wanda abubuwan maganinsa yake ciki .
Sosai majinyacin yake karbar duk wani taimako da kuma kulawar daya dace daga wajen iyalan musamman ma mulaifah daya kasance koyaushe tana wajensa a zaune ita take bashi duk wata kulawa .Amma duk da haka babu wani motsi dayake nuna ci gaba a game da marar lafiya .
Saida yashafe tsawon sati biyu batare da ya farfado ba saidai ruwan maganin da kuma ruwan abincin da in an bashi yake shiga cikinsa ,wanda shine ma ya tabbatar musu da cewar akawai sauran rayuwa a tattare dashi .bayan cika cikansa sati biyune a kwance ranar mulaifah ba zaune a gefensa ta zuba masa manyan idanuwanta tana kallonsa ,wanda a hakanne ta tafi tunanin yanayin rayuwar wanda yake kwance a gabanta tamkar bashi da rai "ya kai wannan bawan allah, daga ina kke oho ,nasan a halin da kke ciki a yanzu baka taba tunanin zaka tsinci kanka a wannan halinba, (,tabbas rayuwar duniya ba abuce mai dorewa ba ,duba da yanda muke rayuwa a yanzu sai mutum ya manta da zuwa yayi sannan kuma zai koma a kowane irin lokaci ,yanada kyau a rayuwar dan adam ya ko ya yasamu dan wani lokaci a rayuwarsa yasamu yayi aikin alkhairi a wannan lokacin ,to hakika yanayima rayuwarsa asusune ,wanda kuma zai taru a fuskar da baya tsammani ,)......motsawar da hannun mutumin yayi ,shiya dawo da mulaifah daga tunanin da ta tafi ,wanda sai da tasake gani a karo na biyu ta tabbatar hakika yafara motsi, kana ta fita da gudu tana kiran abbanta yazo yagani .Saida tafitane ta tuna cewar mahaifinta ba ya gida ,sannan ta isa ga mahaifiyarta tana fada mata ,bayan tawowarsu dakinne suka ga ya bude idansa yana kokarin tashi ,zaunawa sukayi a gabansa suna kallonsa yayinda shima a bangarensa yake musu kallon rashin sani .kallon kallo akayi na natsawon wani lokaci ,yazamana suna masa kallon ya farfado bayan kaman bazai tashiba ,shikuma yana musu kallon mamaki na su waye sudin .Suna cikin hakanne maharbi uzairu yadawo ,ganin basa haravar gidannasu ne yasa shi isa ga turakarsa inda ya ke jinyar marar lafiyar ,domin yasan acanne zai tarda yar tasa ,wanda nanne yazame mata wajen zama ,koda yasa kansa a cikin dakin sai ya tsaya yana kare musu kallo ganin yanda suke kallon mutumin shima kuma yana kallonsu ,sallamar dayayi ne ya katse kallon nasu ,duk suka juyo izuwa gareshi ,mulaifah ce dake bakin kofa ta amsa masa kana ya shiga ya zauna a kusa da mutumin sannan ya tambayeshi "ya kai wannan bawan allah daga wane yanki ka fito ?sannan kuma ya sunanka ?"duk tambayar da maharbi uzairu yakewa mutumin ba guda d'aya daya samu amsar ta a ciki sai ma ido daya zuba masa ,saida uzairu yasake maimaita tambayarsa ,kaman bazai sake amsa masa ba sai kuma yace "bansan a ina nake ba sannan ni banda suna"kallonsa sukayi da mamaki sannan maharbi uzairu yasake cewa "haba yakai wannan mutum ya za'ayi ace bakada suna ,?kadai tuna yanayin rayuwarka"kallonsa mutumin yayi kana yace "ni bansan kowa ba ,sannan banida suna inma ina dashi bansanshiba " "sunan sa SAMEER " shi abinda yafito daga bakin mulaifah muryar ta cikin kuka ,bata kara koda kalma guda daya ba ta fita da ga dakin fuskarta cikin kunci da damuwa .;
Abinda ya da mulaifah shine wata biyu kenan da rashin yayanta datayi mai suna sameer ,wanda suka tashi tare ,ta shaku dashi matuka ,wanda sanadiyyar rashin lafiya da yayi yarasu ,rashin sa yasa ko cikin dajin bata shiga koyaushe tana gida ,sannan yanayin walwalarta ma yaragu sosai .Amma dawowar da mahaifinta yayi da wannan mutumin ,sannan aka fara jinyarsa a gidansu ,sai kawai ta tsinci kanta da samun nutsuwa idan tana a kusa dashi ,sai yazamana ta na kallonsa a matsayin wani dan uwan allah yasake bata a lokacin data rasa nata dan uwan .Wannan shine dalilin dayasa da yace bashida suna ta cemasa sunansa sameer ;Kodajin abinda mulaifah ta fada dakuma yanayi data fita sai hankalinsu yayi kanta dakuma tausayinta daya kamasu ,tashi sukayi suka bi bayanta,inda suka sameta a dakinta tana kukan rashin yayannata wanda yadawo mata sabo a sannan ,maharbi uzairu ne yashafa kanta kafin yafara mata magana "ya ke y'ata musulmi baya cika cikakken mumini sai yakasance yana yarda da dukkan kaddar datazo masa walau mai kyauce ko akasin haka ,yakamata kidauki rayuwa a duk yanda tazomiki ,tabbas nasan zaki shiga damuwa duba dayacewar kuntashi kunga yanayin rayuwarku ya sha banban dana sauran kowane ya'ya',sannan dan uwanki shikadai kika sani ,shima kuma allah yakarbi abinsa ,sann ............"ahah abba niba wannan bane yasani kuka ,hakika na karbi duk wata jarabawa a rayuwata ,damuwata daya shine ,ya abbana kar kori wannan sameer duk da cewa bakasan wayeba sannan koda yagane shi waye dan allah karokeshi ya zauna damu ,kar yatafi ,domin kawai natsin zuciyata da yarda dashi sosai ,sannan inaganin sa tamkar ansake bani wani abokinne wanda zan dinga fita dakuma shawara dashi "hmmmm shine abinda salma tacecewar bayan ta gama jin tuk korafin yar tata kafin taadora da cewar "shikenan kidaina saka wannan damuwar haka a ranki ,sannan idan har zai zauna a tare damu to ba makawa sai ya zauna ,idan kuma ya tuna ko shi waye yaga zai tafi ga yan uwansa to mu bazamu hanashiba ,sannan kafin haka tafaru da munyanke cewar zamu turashi ga abokin babanki yazauna acan kafin yagano yan uwansa ,amma tunda kince haka ,zamu zauna dashi na wasu kwanaki idan har yaga yana sha'awar zama damu to shikenan ,idan kuma baya bukata sai mukaishi ga cikin gari ,haka mulaifah ta hakura ta bi shawarar da iyayeta suka yanke a game da sabon sameer din da ta radawa suna .Haka rayuwar sameer din takasance a tare da sabon iyalan da ya tsinci kansa a ciki ,dasannu yake samun lafiya inda har yazamana yana iya fitowa da kansa har ya dan zagaya sansanin nasu ,saidai magana ne da bai faye yiba sai yazama dole shima ya tambayi mulaifah .watarana ne bayan satinsa daya da farfadowa ,salma ta kira mulaifah ,akan ta zaga da sameer izuwa wajen dajin ko zai ware jikinsa ,hakan yayiwa mulaifah dadi wanda har saida yanuna akan fuskarta .Shiga tayi da murnar ta dakinnnasa inda tasameshi a zaune yayi shiru kaman mai tunani saida tayi masa sallama kafin ta shiga ,inda tasamu waje gefe dashi ta zauna ,dagowa yayi ya kalleta kana yamaida dubansa inda yake2 kallo batayi tsammanin zai kulata ba kaman yanda yake mata a koyaushe ,saikuma taji akasin hakan daga bakinsa cikin sanyin murya wanda take dauke da izza dakuma miskilanci "menene yasaka ki farinciki da har ya bayyana akan fuskarki ?"saida ta kalleshi kafin tace "tun lokacin da kafarka tafara warkewa nakeson raka ka mu zagaya bayan gidan mu ,saidai ummi bata bani izini ba ,sai a yau ta amincemin dana zagaya dakai ko zaka dan ware daga zama guri daya " "shikenan duk yanda kikace "shine abinda yafito daga bakinsa bayan gama jin bayananta dayayi.
Saida suka kama hanya ,har sun danyi nisa amman ba abinda ya gibta na magana a tsakaninsu ,kowane a cikinsu akwai tunanin dayake yi a zuciyarsa ,sameer ne ya katse shirun ta hanyar cewa "uhmm meyasa kuka amincemin dazama a tare daku bayan bakusan koni waye ba ?sannan kuma meyasa kika kirani da sameer kuma naga kina kuka a dalilin kiran ?shin menene dalilin ki na amincewa dani ?"tsayawa tayi tana kallonsa har saida ya kai ga karshen tambayoyinsa ,kana ta zauna a kan wani dutsi dayake kusa da ita ,ganin hakanne yasa shima yakoma gefenta ya zauna yana kallon ta domin jin wane kalar amsa zata bashi ,dagowa tayi takalleshi kafin tace "saboda mun yarda dakai kan bazaka cutar damu ba ,munyar da koda ka cutar damu to dama yana a kaddararmu dan haka hasashen zakayi mana mugunta bazai sa ka mu ki taimaka maka ba ,sannan kuma bakomai yasa nakira ka da suna sameer ba ,saidan nayi kewar mai sunan tun lokacin daya tafi yabarni bayan yasan shikadai nake da abokin nishadi na dakuma shawarata ,nakira ka dashine saboda gani nake kaman andawo min dashine a karo nabiyu lokacin da na cire rai dasamun wani abokin !!!,tambayarka ta karshe kuma ,haka kawai zuciyata ta tsinci kanta da amincewa dakai ,koda kuwa zaka kasheni a yanzu sannan kadawo min da rai na banajin yardar danai maka goge a zuciyata ,sannan a karshe inason kar ka tafi kai ma kabarni lokacin dana saba dakai ,kuma inason kayimin alkwarin zaka yarda dani sann .........gurananin dasuka jine yasa su juya wa dasauri cikin rudani 😊😊
😊 to halin rubutu a yi hakuri 😊

kutara dani a gaba ,taku 💝(SADI ~SAKHNA )💝

Boyayyiyar AlkaryaWhere stories live. Discover now