(The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟
BOYAYYIYAR ALKARYA(the hidden island )🌄🌄🌄🌄🌄
phone number:09035784150telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0
whatpad :@SAKHNA03
chp [07].Wajene daya kunshi kyawawan furanni wanda suka banbanta da kalar bishiyoyin da'ake samu a saura sassan duniya ,(bishiyoyi ne manya masu dogayen ganye da kuma tsayi ,sannan furannin wajen na dauke da fulawoyi manya da mutum zai iya shiga ya kwanta aciki sannan suna dauke kaloli kala kala ,kama daga ja ,har zuwa su shudi da kuma kalar rawaya (yellow ),dukkansu shagala sukayi da kallan wajen ,har takai wajen yadauke hankalinsu matuka wanda har ya kaisu ga shiga shaukin tunani mai dadi,a yanayin da suka shigane na shagala da kallon wajenne ,har ta kai ga mulaifah tazame saboda wajen dayake dauke da damshin ruwa da kuma tabo daya mamaye wajen ,yanayin zamewar da mulaifah tayi yasa ta saddakar da jinta a kasa da zatayi ,saidai sabanin hakan sai jinta tayi a jikin mutum ,bude idanuwanta tafarayi a hankali har ta budesu dukka akan fuskar sameer da shima idanunsa yake kanta .
Sunshafe tsawon wani lokaci suna kallon juna a haka ,yayinda kowa da abinda yake sakawa a ransa ,abangaren mulaifah kuwa tunani ne mai dadi yake fisgarta wanda yahadu da sinadarin iskar wajen yabada wani yanayi marar misaltuwa ,inda shikuma uban gayyar yake kallon kanwartasa tayi masa kyan dabai daba ganin irinsa ba sai a yau ,ganin suna kokarin faduwa ne a haka yasa dawowa daga duniyar tunanin dasuka tafi ,tare da mamakin yanayin dasuka shiga tashi daya .kadewa gefen kayanta tafarayi kafin kuma ta tafara tafiya acikin wajen dan karewa wajen kallo ,binta yakeyi abaya kafin yafara magana ta hanyar katse shirun da ya gibta a wajen ,"kanwata kaman a yanda mukayi tafiya a izuwa wajennan babu nisa da inda mukaje diban ruwa ,sannan mun zo fiye da wajennan a jejinnan amma ban cikaro da wannan wajen ba sai yanzu ,sannan yanda kike kallon wajen da mamaki akan fuskarki yabani tabbacin cewar bakisan wajennan ba,kokuma koda kinsani to da alamar bakiyi tsammanin zuwa wajennan ba a wannan lokacin ?" ehh hakane domin duk rayuwar danayi a jejinnan bansan da wajennan ba,wanda hakan nima yaban mamaki matuka,sannan wajen yamin sosai ,duk da dama akwai wajen da bansan da suba a wannan dajin me yiwuwa wannan wajen na daya daga cikinsu ","tabbas wajennan na dauke da abubuwan ban mamaki sosai har ma da ban sha'awa sosai,"daga ganin yanda fuskar sa ke fitar da murmushi yanuna cewa wajen na masa dadi matuka.Tafiya suke suna labarin daya shafi duniyar tasu har takai ga sun wajen rafin da suka zo deban ruwa ,nan dimma ba abinda yakawosu sukayi ba wato deban ruwan ,zama sukayi a bakin ruwan kafarsu na kuma na cikin ruwan ,wanda da alama dukkansu basu gaji dayima junansu lbri ba ,lbrin suka fara inda sameer ya bukaci mulaifah ta bashi labarin abubuwa na yau da kullum ,ganin yana maganane amma yaji shiru alamar wanda yake magana da ita hankalinta baya wajensa ,juywa yayi ya kalleta ta zuba tagumi tana kallon ruwan dake gabanta kaman ba itabane yanzu take cikin nishadi ,muryar sane cikin sanyi dakuma alamar kulawa yadaki kunnen mulaifah har yadawo da ita daga tunanin datakeyi ,ta hanyar tambayar ta "menene yake damunki ,naga kin shiga cikin dqmuwa haka ,iyeee ?fadamin mai ke damunki "kallansa tayi kana tace ,bakomai ba abinda yake damuna "hmmmm kina nufin kice min babu ne zai sa fuskarki shiga damuwa uhmm ,ko kina nufin kice min har yanzu bansan ki ba uhm ?ko kuma har yanzu bankai matsayin jin damuwaki bane ?" "ahah yaaya sameer ,ahah bahakabane kawai dai wani abune yafadomin na rayuwar na baya ,kuma banaso nace maka tunani nake saboda na amince maka akan bazan sake tunani ba kuma gashi nayi ,dan allah kayia hakuri kaji yaya sameer bazan sake daga yanzu "duk maganar datake idon sa nakanta da yanayin da idonta yake alamar kaman yaro yayi laifi ,dakuma karamin bakinta da yake juyawa ta kowane bangare ,yanayin kalar2 tunanin dayazo cikin zuciyarsa new yabashi mamaki inda baisan sanda ya yafara murmushi ba,ganin tana magana baice komai ba yasa tacigaba da cewa ,cikin muryar shagwaba "uhm....uhm... Yaaaa sameer ina ta baka hakuri amma ko magana bakayi ba " "ehhh najiki saidai bazan sake miki magana ba idan nasake ganin ki cikin wannan yanayin kuma ba'a binda sameki ,kinji ,banason ganinki a hakan ko kadan,tashi muta fi kar ummi ta fara neman mu,tashi tayi batare da musu ba tabi bayansa ,suka fara tafiya su biyu zuwa giddansu ,inda shi dama jaaruun ya tsufa a gida .Koda suka shigo gidan kowa saukar da kai yayi sanadiyyar laifinsu da sukayi na dadewa a inda ta aikesu ,kallonsu tayi kana tayi murmushi domin tanada masaniyar inda suka tsaya kafin deban ruwan "kun gaji da yawon kun dawone ?karku damu kuje ku zauna ai babanku ya fansheku ,domin shine yaje ya debo ruwan ganin baku dawo da wuriba ,dan haka ku kwantar da hankalinku saidai kiyayewa gaba kawai,haka zancen ya wuce inda da haka.
Bayan gama cin abincinsu kowa yana zaune ana hira wanda a yanzu suma iyayen suna dan zama ayi hira dasu ,wanda hakan na da dadi sosai (irin wannan hali yawancinmu hausawa muka rasa ,saboda yanayin al'adarmu,sai kaga uba yashigo gida yana daure fuska kokuma ita kanta matarsa bashida lokacinta ,inaga kuma yayansu ,wanda wanima sai ya shafe wani lokaci batare da yaga ubansa ba ,saboda sanda yadawo yayi bacci kafin ya tashi kuma ya tafi aiki ,kokuma suma iyaye matan sai kaga wata ta harkar kasuwancinta itama take ba ta yayantaba ,wannan ba dabi'a bace mai ma'ana sam )to bayan tashinsu ne daga firar iyayen suka fara tattaunawa a game da halin yayansu ,uzairune yafara fadin"tabbas yakamata muyi wani abu akan yarannan ummin mulaifah domin inaji ajikina kaman akwai abinda zai faru wanda al'amarin ba abune daza mu iya wani abu akai ba ,game da su mulaifah kuma ,na manta bangaya miki ba jiya jaaruun ya kai su mulaifah boyayyan jeji wanda bansan menene manufar hakanba ,amma inaga dan ya yarda da sameer ne shiyasa "kallon sa salma tayi kafin tace "ya akayi fadi cewa jaaruun yakai su mulaifah boyayyan jeji "kallon ta yayi kafin yace"jiya da nake dawowa daga daji nagansu a wajen amma sunny basu ganni ba kuma da alama basu san ya akayi sukaje wajenba,kuma nagansu acikin yanayi na kaunar junansu a wajen"hmmm salma tayi ajiyar zuciya kafin tace "to yanzu ykke ganin za'ayi "murmushi kawai yayi kafin yace "allah yakaimu gobe"itama kawai shiru tayi kana tace "allah ya kaimu "tashi sukayi suma suka shiga daki.to asuba tagari saida safe ahalin uzairu.😊
To nima sai goben kohhhhh ? in allah yakaimu ,da alherinsa ina muku fatan alheri ga duk wanda yake karanta wannan littafin nagode sosai da sosai .
SADI-SAKHNAce (the legendary novelist )
YOU ARE READING
Boyayyiyar Alkarya
AdventureThe legendary story about the mysterious hidden🌄🌄 island the numerous of people and evils fails to find out about it. But find by the unremembered prince 🤴 without his knowing 🤔🤔🤔