Chapter 9

48 10 0
                                    

(The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟

BOYAYYIYAR ALKARYA(the hidden island )🌄🌄🌄🌄🌄

phone number:09035784150

telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

whatpad :@SAKHNA03

chp(09)
Bayan gama hirara tasune da kuma gama nasihar da iyayen sukayiwa yayannasu sai yazamana sun nufi makwancinsu domin kuma bawa shima jiki hakkinsa,saidai al'amarin daya faru a wannan daren ya sanjawa dukkan iyalan akaklar rayuwarsu daga haske izuwa duhu.
cikin dare kaman wanda aka tsikari sameer kawai tsintar kansane da tashi zaune,juyawa yayi har zai koma ya kwanta saikuma yaji abin kaman ya wuce motsin da yasaba ji kullum hakanne yasashi tashi domin ganin meyake faruwa,fitowa yayi da takobinsa a kunkuminsa domin uzairun ya hane shi da jaga gefen gida batare da makami ba,sanda yake cikin nutsuwa da san gano a ina motsin yake fitowa razana yayi da abinda yagani a bakin turakar iyayenasu........
............A bangaren su uzairu bayan shiga daki da daddadare............
bayan shigarsunne sunyi shirin kwanciya sai ya zamana salma ta ki kwanciya kaman yadda suka saba a kullum,uzairunne ya kalleta da mamaki kafin yace"menene ya faru immin mulaifah na ga baki kwantabab kina zaune uhmm?"kallonsa tayi fuskarta kaman da damuwa kafin tace "hakika nima haka nakejin kaman rayuwarmu zata sanja daga yau amma hankalina akwance yake dannasan bamu bar baya a kuraba,dama mulaifah ce damuwata amma yanzu hankalina ya kwanta tunda nasan na barta a hannun mijinta kuma inada yakinin bazai cutar min da ita ba kobaya raina,duk inajin cewa kaman zata shiga cikin kangin rayuwa,ammma nasan komai yayi farko zai zama karshe"koda takawo haka a maganarsa sai yazamaan fuskarta dauke da damuwa har takai cewa hawaye n zubowa daga idonta amma hakan bai hana fuskarta murmusawa ba,ajiyar zuciya uzairu yayi bayan ya gama saurarr matar tasa,sannan abin ya bashi domin bai taba tsintar ta acikin irin wannan yanayin ba,kafin yace"kii kwantar da hankalinki ki kwanta sannan ki barwa allah komai na rayuwarki domin komai zai faru saida izinin allah,jijjiga kai tayi alamar taji abinda yace kafin ta juya da kwanta batre da musuba.
Bayan kaman can sulusin darene uzairu yayi zuruf ya farka inda yayi arba da wasu mutane akansa wanda baisan daga inda suke ba,mutanen sun rufe dukkan jikinsu da bakin kaya sannan babu alamar sassautawa a lamarinsu,nuna shi sukayi da takobi sannan yana juya gefensa yaga wuka mai kaifi a wuyan salma wanda suka kewayeshi suna jiran suji ta bakinsa,jikinsa ne yayi sanyi sosai ya tafi tuanani na wacin gadi,kafin daga bisani kuma babban cikinsu ya kace shirun ta hanyar cewa"zaka fada mana abinda yakawomun kosai kaga kanta a kasa iyeeeeeee"hawayene yake fitowa a fuskar ma'auratan kafin daga bisani salma tace"banyada da kafamusu abinda suke nemaba koda kuwa hakan zai yi sanadin rayuwata,inaso kakula da ran mutanen da zasu salwantu idan har kace zaka ceci nawa ran inaso koda zamu rasa dukkan rayuwarmu akan hakan to karka kuskura kafada musu abida suke nema ,idan kuwa kai hakan to raina bazai taba yafemakaba,sannan daga karshe inaso kakulamin da yayayna idan har rank yakubuta daga garesu"ganin surutun da ta tsaya tanan musu yana bata musu lokaci sannan kuma maimaikon ma yasa shi fada musu abinda suke nema saima kara taurara zuciyarsa da maganarta yake,hakanne yasa babban ciknsu luma wukar hannunsa a makogaranta wanda take ta shige jikinta kana kuma ta bawa jinin jikinta samun damar fitowa waje da karfi,fitowar da jinin yayi daga wuyan ta da kuma faduwar da tayi batareda da alamar rai ba shiya karawa wutar dake cikin cikin uzairun fetur,inda take takama batare da tunanin mezai faruba,jijjige mutanen dasuke rike dashi yayi inda take yafara wani irin gunji sannnan cikin zafin nama kafin kiftawar idansu yazare takobinsa yayi kansu.............
...........dowowa cikin labari ......................
lokacin da suka saka wuka a wuyan salma shiyayi dadai da zuwan sameer bakin dakin inda shima yayi kansu cikin zafin nama batare da bata lokaciba.
Saida suka shafe wani lokaci yazamana ba abinda kke ji jejin sai karar takobi dakuma mashi,tun suna fada turakar uzairun wajen inda aka kashe salma har ya zamto sun fito harababr gidan suna zuba artabun da ba wanda yasan karshensa,saida yazamana cewa bakaken dakarun na kaiwa hari dan su samu su kaisu kasa har su samu su samu damar kayar dasu uzairu domin cimma burinsu kafin lokaci ya kure musu,a inda a bangaren su uzairu kuma saiyazamana suna kaiwa sara hade da suka cikin zuciya dakuma tsanar mutanen bisaga abinda suka musu.
Saida suka sake daukar wani lokacin suna wannan fadan batare da dakarun sun samu damar koda yankar daya daga cikin su sameer ba,lura da hakan da babbansu yayi yasanya shi kaiwa uzairun hari inda kuma cikin sa'arsa yasamu damar yankan uzairun a cikin sa ta gefen dama,kara yayi tare da fara durkusawa yana mai dafe cikinsa wajen da jini ke zuba kaman an aikoshi,ura da hakan da sameer yayi ya sashi juyewa izuwa wata halitta daban a bangaren yaki wanda ko shi kansa uzairu bai taba ganinsa cikin yanayinba,yazamana idansa yarufe kaiwa sara da suka yake duk inda ya ga alamar mutum a gefensa.
Bayan wani lokacine dakarun suka kulai dacewar awan ya ragu fiye da yanda suke tunani sannan sukuma sun kasa koda taba rigarsane,sannan yabawa uzairu kariya sosai inda shima suka kasa samunsa akaro na n jejbiyu.
Guu dakarun suka fara izuwa cikin jeji domin tsira da ransu,a bangaren sameer kuwa hakan bai masa ba saida shima rufa musu baya cikin zafin nama su ma kuma suna gudu domin tserewa mutuwarsu,ganin zaiyi nisane sannan kuma ga uzairu na bukatar taimako yasashi dawowa daga bin abokan gababr.Dukawa yayi ya tallafeshi suka shiga izuwa ckin gidannasu.
Kururuwar da ya fito daga dakin da mai afkuwa ya afku aciknsa jiya da daddarene yasani yin hanzari domin isa naga abinda ake a cikin dakin,mulaifah ne akan gawar mahaifiyarta ta rungumeta kamar za'a kwace mata ita da ga wajenta,yayinda duk ilahirin jikinta yake rawa tare da muryarta dake fitar da amooo mai matsanancin tausayi dakuma rashi acikinsa.
A bangaren sameeer kuwa yana durkushe ya zuba mata ido ko rarrashinta ma yakasa balle yahana ta ihun datakeyi,inda yakejin ihun tamkar ana huda tsakiyar kirjinsa,amma hakan bashi zaisa yasamu damar hanata ihun ba.
A haka suna zaune uzairu yashigo yasamesu shima cikin dauriya duk da irin yanakan dake gefen cikinsa amma bai hanashi tashi ya zo izuwa wajensu ba ,shima sameer a bangarensa mamakine yacikashi ganin wanda yake cikin jinya ya taso ,hakanne yasa sameer kasa boye mamakinsa har saida ya tambayeshi"abba meyasa ka taso acikin wannan yanayin?"murmushi yayi cikin dauriya kafin yace"kar ka damu sameer zan iya daurewa,sannan a wannan halin da uwar yayana take ciki ba abinda take bukata daga wajena dayawuce yi mata sutura dakuma kaita makwancinta dan haka zan kokarta naga na cika mata wannan burinnata,"bayan ya karisa maganarsa ne ya karisa izuwa ga gawar matar tasa dakuma yar tasa da ta sanja kamanni a iya daren yau kadai,dafa kanta yayi kafin ta dago kannata wanda sai sannan takula da mutane biyun dake cikin dakin,rirrike mahaifinta tayi tana cewa"abbaaaa ummata,itace a kwancefah abba itace kuma abba na tasheta taki tashi bare ta min magana abba,abba so takefah ta tafi ta barni irin na yaya sameer,abba kace mata kar ta tafi tabarni bazan iya jurewa ba abbahhhh"jijjiga mata kai yayi dadai lokacin da kwallah tafito shima a idonsa kafin yace"zaki iya mulaifah tabbas zaki iyah kar kice bazaki iyaba jurewa ba idan allah ya jarrabeki kinji"janye ta yayi kafin yacigaba dacewa"sannan bai kamata kimamta kuka ba kinji domin addu'arki take nema bawai kukanki ba ,kiyi mata addu'a sannan akai ta makwancinta domin a yanzu shine gatanta dazamu mata na karshe kinji?"gyada masa kai tayi alamar taji mai yace kafin ta share hawayenta ta tashi domin bashi wajen ya shirya mahaifiyartata,hanyar kofah tayi tana tangadi kamar zata fadi inda sameer yayi saurin riketa suka karisa fita daga dakin.
Bayan sun fitane daga dakin suka samu waje agefe suka zauna,tallafeta yayi a kirjinsa yaana jijjigata domin bakinsa yakasa furta koda kalma daya daga cikinsa.A bangaren mulaifah kuwa kanta ta kifah akan kirjinsa tana sauraran irin radadin da zuciyarta take bayyana mata akowane dakika na bugun zuciyarta,bayan wani lokacine sameer yakula da mutanen dasuka ke tsaye akansa,mamakine yakamashi sai daga baya ne yagane mlm uwaisu daga cikin mutanen anan ne yakual da mai yakawosu wajen wato jana'iza,fitowa uzairu yayi daga dakin da gawar take kafin yamusu iso zuwa ga dakin.
Bayan gama yimata sallah da kuma kaita makwancinta sai yazamana cewa saura iya su uku ne wajen domin uzairu yafada musu cewa kowa yatafi lalurinsa na yau da kullum,bayan sungama artabu da uwaisu akancewa sai ya nemo masa magani a game ciwon dake jikinsa,a inda uzairun yakafe akan cewar bazai bar wajen neman maganiba kuma ai ciwone idan yana binsa a hankali to da sannu zai warke tamkar bai taba yiba.
A hakadai rayuwar ta ke gara musu har takai ga salma tayi kwana uku a gidanta na gaskiya,hakika mulaifah tayi abin mamamki domin dukkasu basu zata zatayi dangana kamar yanda tayi a yanzun ba,a bangaren sameer kuwa tausayin dukka ahalinne yacika masa zuciya yazamana duk abinda mulaifah zata bukata kafin takai ga fadamasa zai mata batare da gazawarsaba,hakan shiyabada gudummawar kara kwantar mata da hankali dakuma kara tawakkallin rashi mahaifiyarta ta.
A bangaren uzairu kuwa tafiya tayi tafiya har takai ga cewar dafin dake cikin wukar da'aka sokeshi da ita ratsa duk lahirin jikinsa batare da su sameer sun lura da hakan ba domin yayi kokarin tare duk wani hanya dazai basu damar gane halin dayake ciki.
Bayan dan wani lokaci bayan gama cin abincinsu sanu zaune duk da bawani hira sukeyi kaman da ba ,amma duk da haka idan ka gansu zakasan bakaramar dangana sukayiba da rashin bangon gidan wato salma(ummi).Bayan sun gama zamannasune kowa ya tashi domin wucewa abinda yashafi lalurinsa,saidai mikewar mahaifinnasu keda wuya yazube akasa tamkar ba numfashi ajikinsa,cikin sauri su mulaifah sukayi kansa a razane tare da kinkimarsa zuwa dakinsa,inda suka fara kokarin bashi taimakon gaggawa dakuma gano mai yake damunsa,hankalin sameer ne yakai ga gefen rigarsa inda yasa tsumma ya daure,abinda suka gani ne yasasu razana inda mulaifah kam tasa kuka da ganin halin da babannnata yake ciki,wanda ita batasan yaji ciwo ba ma bare tasan ya ciwon yake,bakomai suka ga ba illlah raunin dake gefen cikinsa wanda ya dafe yayi bakikkirin har yakai ga ya harba duk ilahirin jikinsa,mulaifah cikin kukanta tafara cewa"meyasa abba kaima zakayi haka?kenan so kke kaima katafi kabaeni ko so kuke kubarni nikadai ko ?"rikota sameer yayi tare da fadin"ahah mulaifah kidaina fadin hakan kinji bazai tafi ya barkiba bana son naganki cikin damuwa ko kadan,sannan kikwantar da hankalinki da sannun abbah zai tashi mu zauna tare kinji"yana cikin rarrashinnatane sukaji babannasu yaza numfashi mai tsayi alamar dawowa daga suma,zuyawa dukkansu sukayi kana suka karisa izuwa wajensa.Mulaifah ne ta rike hannunsa kana tace abba dama baka da lafiya amma baka fadamana?meyasa abbahh kayi haka?"kallon yar tasa yayi cike da tausayinta kafin yasa hannu ya shafa kanta yana mai fadin"yake yata kiyi sani cewa idan abu sai samu mutum to ba makawa sai sameshi dan haka ki kwantar da hankalinki ki rungumi duk yadda rayuwa tazomiki kinji?allah yamiki albarka ya kuma arbarkaci rayuwarku keda mijinki dama zuri'arku baki daya"uk maganar dayake mata hannunsa na kan yartasa yana shafa gashin kanta yayida itakeyasa meyasa wannan bakakea ta tayi karfin halin yin murmushi tare da rike hannun mahaifinta alamar taji abinda yace.Duk abinda uba da yar suke hankalin sameer na kansu yanda suka birgeshi a wani bangaren kuma suke bashi tausayi yanda rayuwa da juya tashi daya,maganar da uzairuyamasa ne yadawo dashi daga dunyar tunanin iyalan daya tafi,mika masa hannu yayi akan ya matso kusa dashi shima,cikin sauri kuwa shima sameer din yamatsa kusa dashi kana ya hada hannunsu su biyu ya rike a hannunsa kafin yace"kaman yanda na rike hannunku haka inso ku kasance a haka cikin taimakon juna matukar kuna a tare da juna,ku sani cewa ku tamkar wani sabon reshene dazaku cigaba da yaduwa har kubada cikekkiyar bishiya irin wanda aka fitar daku daga jikinta,dan haka ku kula kumata bayi mai kyau da gaskiya domin jijiyoyinta su riketa sosai,komin iska komin ruwa bazata taba faduwaba bare har ta kasa fitar da itama reshe mai kwari ba,ina fatan maganata ta isa inda nkeso ta isa a birnin zukatanku"kallonsa suke da mamakin irin yanayin maganar sa yau kafin cigaba da cewa"duk abinda nakeso na isar a gareki yata nasan na isar dan haka yarage naki yin amfani dashi,sai kuma yanzu inso kibamu gu nida mijinki zan barmasa ragamar nauyin wajennan wanda bazaiyiyu na barmikiba saboda yanayin raunin rayuwarki a matsayinki na ya mace,dan haka kimin afuwar fahimtar zancen....................."kafin yakarisa ta kateshi tare da cewa na fahimceka abbah kuma da sannu zan kasance mai zama akan duk turbar daka dorani kuma,kuma na fahimshi mai zaka yi bayani akai,sumbatar goshin mahaifinnata tayi kafin sumbaci goshin mijinnatama daga baya kuma tafita ta basu waje domin su tattauna.
Shin kasan wani game da boyayyiyar alkarya???? shine tambayar da uzairu ya watsawa sameer inda muka yi shiru nida shi................
♥️❤️sadi-sakhna ce♥️❤️(the legendary novelist)🌄🌄............next chp loading..45%...........bye💃💃💃

Boyayyiyar AlkaryaWhere stories live. Discover now