(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)
🌄🌄BOYAYYIYAR ALKARYA🌄🌄(the hidden island)
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
(The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟
BOYAYYIYAR ALKARYA(the hidden island )🌄🌄🌄🌄🌄
phone number:09035784150telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0
whatpad :@SAKHNA03
chp[12]
Saida yarima samhal yadauki wani lokaci amma ba mai tsawoba saboda azababben gudun dayake kafin yakai ga masarautar tasu ,yanazuwa bai zame ko inaba sai wajen mahaifiyarsa, wanda take zaune gefenta bayine a zaune suna mata hidima ,wucewa yayi zuwa gabanta yazauna ,wanda ganin hakan yasa bayin dake gabanta suka fita domin basu damar tattaunawa ,kallonsa tayi da alamar mamarki kafin tace ,abiii daga ina kke haka kaman baka cikin hankalinka ?sannan tsawon kwanaki kana ina ?saboda nasan baka dadewa a wajen mu'allim ,ka tambayeni nabaka izinin tafiya amma baka dawoba har abbanka yadawo daga tafiyarsa ,nima nashiga damuwa sosai akan hakan , inaso kafadamin mai ke damunka saboda abinda kkeyi a kwanakinnan yafara bani tsoro sosai "haka ta karisa maganar ta itama muryar ta dauke da tashin hankali ,rike gwiwanta yayi kana yace "nasan zaku shiga damuwa akan hakan amma ina rokon afuwarki akan hakan ,sannan inaso na tambayeki akan wani abu?",uhmmm inajinka wace tambaya ce ke tqfe dakai kafadamin na ji "saida yayi jimmm kafin yace "kin taba jin bayanin ya boyayyiyar alkarya take a wajen mai martaba ,sannan meyasa mutane suke neman ta ?","meyasa kke tambaya akan boyayyiyar alkarya kai kuma ,bayan wannan ba huruminka bane sai kasan mai take kunshe dashi "kara rike kafarta yayi fuskarsa alamar roko kafin yasake cewa ,dan allah ummi ki fadamin akwai dalilin inso nasani ne "mamakinsa tayi yanda yadamu akan abun kafin kuma can tace "bawanda yasan inda take a halin yanzu ,sannan babban tashin hankalin damuke ciki shine yanda boka gazaza yadukufa wajen nemanta ba dare ba rana ,saboda yayi amfani da ruwan cikinta wajen tashin shugabarsu wato urai hilwa daga kwancaccen ruhinta dayake kwance ,dukkanin sarakuna harma da abbanka suna cikin rudani a game da wannan al'amari saboda dukkannin iyalansu da talakawansu suna cikin hadari sosai ,"koda ta kawo nan da zancenta sai ta tsaya ,yayinda yarima samhal kuma a bangarensa ,ya tsinci kansa cikin yanayin da bai taba tsammani ba ,domin ji yayi tamkar andora masa wani dutse akan kirjinsa wanda baisan iya adadin nauyinsa ba ,tashi daya gimbiya jazila ta ga hankalin dannata yana sauyawa inda tashi daya jikinsa yafara rawa zufa na keto masa ta ko'ina ,rike hannunsa tayi dayake kan cinyarta "menene ke damunka haka kke zufa ko baka da lafiyane uhmm ?" "ahah bakomai"shine kawai abinda yace kafin yatashi ya fita daga dakin .
Koda yafita zuwa yayi yasamu abokinsa wanda suke amini wanda a ganinsa zai iya samun nutsuwa a wajensa,zama yayi yai shiru batare daya ce komaiba wanda har abokinnasa ya gaji ya fara masa magana "samhal meke damuka ne ,yaushe ka dawo daga wajen mu'allim ,kasamu labarin abinda yasameka a wajensa ne ?"juyawa samhal yayi ya kalleshi kafin yace "nasamu nasarar samun abinda nake nema ,saidai al'amarin dake cikin labarin tashin hankalinsa ya isa ,wanda a yanzu bansan ta yanda zan faraba ,domin yanzuma ina bukatar yin wata sabuwar tafiyar saidai nasan su mai martaba bazasu barniba ,sannan idan kuma na tafi bada sanin su ba ,a karo nabiyu ,na shiga hakkinsu kuma ,inason ka fadamin yazanyi yanzu to " "tohh menene yafarune dahar kashiga wannan yanayin haka ?" "al'amarine mai wuyar yarda ,koda nafada ba lallai ne kayarda dani ba ,sannan akwai hadari mai girma game da bayyana labarin a halin yanzu ina neman afuwarka da karka takurani akan sai kaji a halin yanzu " "shikenan allah ya yaye mana matsalolinmu (ameen ),saidai kuma kar ka sare inga kaje ka tambayi su mai martaba gobe kaji ko zasu iya barka kayi tafiyar da kke son yi " "shikenan na gode da shawarar ka ".
Washagari da safe bayan rana tafara fitowa da wuri yarima samhal yadoshi turakar iyayennasa domin jarraba shawarar da abokinnasa yabashi ,saidai har sannan bashi da karfin gwiwa akan hakan ,kirjinsa na dukan uku uku ,tafiya yake har ya isa ga sashen mahaifiyarsa ,sai kuma yaga bakowa ,inda ya samu sakon cewar suna sashen mai martaba sannan kuma mai martaba ya bada sallahun nemansa dayaji labarin dawowarsa jiya ,kai tsaye hanyar turakar mahaifinnasa yanufa ,inda ya tarar dasu suna karin kumallo ,neman waje yayi gefe ya zauna idonsa na kallon kasa alamar girmamawa ,mai martaba ne yafara masa magana tareda cewa "samhal naji labarin dawowarka daga wajen mahaifiyarka sannan kuma nagane cewar kana fita duk sanda kaga dama ka dawo sanda ka ga dama dan ka samu cikin tashin hankalin nemanka ,musamman ma mahaifiyarka ko?to dan haka ban yadda kasake fita daga fadar kasar nan ba ,idan kana bukatar wani abu ka samu mahaifiyarka amma zancen fita nariga nasaka matakan tsaro a hanyar fita idan ma kayi niyyar ketasu ka wuce to zan ji labari ,dan haka zabi yarage naka "haka mai martaba yagama kafa masa dokoki batare daya ji kodaya daga bakin samhal dinba ,wanda hakan yasashi tashi yajuya batare da ya fadi abinda ke tafe dashi ba .
BAYAN WATA GUDA,haka yarima samhal yayita zama acikin fada batareda yafitaba saboda doka dakuma umarnin mahaifinsa ,duk wanda yanganshi a wannan kwanakin sai ya tausaya masa sanadiyyar rama da yayi saboda rashin cin abinci dakuma fargaba .
Yau dinma hakane yafaru domin kuwa zaune yake dare yaraba akan gadonsa ,wanda tashinsa kenan daga razanannan mafarkin daya zame masa jiki na mulaifah ,wanda a yau abin yakara bashi mamaka ,saboda ganinta dayayi a cikin mummunan yanayi fiye da ko yaushe ,kasa komawa bacci yayi a haka har yaga wayewar gari .Bayan gari ya wayene samhal ya nufi wajen abokinsa wanda shikadaine yake da ikon zuwa saboda yana cikin fadar,samunsa yayi yana kwance a dakinsa ya tasheshi kafin yace "uhmmm ya kamata katashi daga wannan baccin haka kai ba mace ko ?" ehh kaine mai cewa wani yana bacci saboda wani abu yasameka ko ?toh wai tukunna ma menene ke tafe dakai da safiya haka uhmm ?wani abune yafaru ?" "komai ma yafaru wanda a yanzu bazan iya cigaba da zama ban fitaba ,anzo lokacin da nakasa daurewa a halin yanzu ,inason kota yaya ne kataimaka min nafita daga cikin fada a tsakanin jiya da yau " "amma yazakayi da su mai martaba ,idan suka gane baka nan yazamuyi to ?" "bakomai zanji da al'amarin idan na dawo amma akwai matsala idan ban tafiba inason karaka ni muje idan ma har bakason tsayawa ka iya amsa tambayoyin su mai martaba ","to shikenan yanzu yaushe kke ganin zamu fita daga fadar nan tareda kai kasan akwai tsaro ?" "inason mu fita da daddare zansan yanda zanyi da dakarun bakin kofa ta hanyar yin basaja ,ko kuma saka musu maganin bacci a abincinsu na dare ,wanda kuma kai nakeson kaji mana da wannan ,tunda ni bana zuwa bangaren abinci ,idan kuma naje a yanzu za'a iya samun matsala a cikin shirinmu ,", "shikenan allah yakaimu daren ",ameen yarima samhal ya amsa.
Haka kuwa akayi kafin dare su yarima samhal sun gama dukkannin shirin abinda zasu aikata acikin daren ,bayan dare yaraba su yarima samhal suka samu nasarar saka dakarun cikin mayen bacci wanda cikin sanda suka samu nasarar fita daga fadar khaisira,wanda saida suka dan fara nisa daga fadar kafin suka hau dawakansu wanda tun rana fahsir (abokinsa) yafita musu dashi ,kamawa sukayi suka hau da azababben gudu ,suka doshi daji shajir.
Saida suka shafe kwana daya da wuni daya kafin suka kai ga jejin da zai sada su da dajin shajir cikin shigar badda kama ,samun waje sukayi suka yada zango ,fahsir sai karfi yake akan nisan tafiyar da sukayi da kuma yanayin dajin daya fara tsorata shi ,duk mitar dayake samhal bai kulashi ba ,wanda inda sabo yasaba da surutunsa.Bayan sun dan hutane da isowarsu kana kuma suka dauki abinda zai musu amfani suka shiga izuwa dajin na shajir ,tafiya sukeyi cikin nutsuwa yayinda yarima samhal na gaba fahsir kuma na bayansa ,sun danyi tafiya mai tsawo kafin suka kawo wani waje,dubawa suka dinga yi amma basu samu wata hanya dazata sada su da inda suke nemaba ,ganin tsayene cikin rashin samun makamar abinda zasuyi yasa fahsir yiwa yarima samhal alama da hannunsa akan zai zagaya domin yin lalurarsa ,can bayan wani dan lokaci samhal natsaye yana jiransa sai kuma yaji ihuu daga gefensa da alama kuma muryar fahsir ceo ,zare takobinsa yayi ya nufi inda amon muryar ke tashi cikin azababben gudu ,ganin wulgawar fahsir yayi ta gabansa yayinda shikuma yashiga tsakiyar su da abinda ke binsa dan ganin menene ,bai ankara ba ya ji andaki kirjinsa ya fadi wani abu ya haye kansa ,hada ido sukayi da jaaruun wanda koda suka ga juna sai kuma jaaruun yafara lashe fuskarsa da harshensa ,acan bangaren fahsir kuwa tsaye yake yana yiwa samhal magana daga nesa ,"kai baka da hankaline kana ganin abu akanka ,sai ya cijeka ko baza ka yanke shi takobinka ba ko?😱"jin maganar da fahsir yake yaki karewa yasa samhal ture jaaruun daga kansa yatashi ya zauna ,koda ya kalli yanayin da fahsir yake sai kuwa ya sheke da dariya 😁😂,ganin fitsarin dayake bin cinyarsa ,gashi dagashi sai dan bante ,duk jinkinsa sai rawa yake ,ganin dariyar da samhal yake masane yasashi duba jikinsa ,zare ido yayi da ganin halin dayake da jikinsa yake ciki ,kafin yajuya da sauri yana kunkuni shikadai ,ganin suna bata lokacine yasa jaaruun yimusu jagora zuwa ga ainihin gidansu mulaifah ,tafiya suke yana gaba suna binsa a baya har suka iso ga wajen ,samhal ne yatsaya yakarewa wajen kallo,inda wajen yafitomasa iri daya da wanda yagani a cikin matihul sahir kafin yayi hanyar dakinsu kafin yatafi ,saikuma yaga jaaruun yayi hanyar dakin daya zauna farkon zuwansa wajen maimakon wanda suke ,binsa kawai yayi har suka kai ga dakin ,saka kansa yayi acikin dakin sai dai kuma abinda idonsa ya hango a dakin shikadai yasashi wani razana tare rawar jikin .................................tohh meya gani ne 😊😊😊😊,nice dai 💖SADI-SAKHNA 💖(The legendary novelist ).
kutara dani a gaba ,always available my fans😍😍😘.
YOU ARE READING
Boyayyiyar Alkarya
PertualanganThe legendary story about the mysterious hidden🌄🌄 island the numerous of people and evils fails to find out about it. But find by the unremembered prince 🤴 without his knowing 🤔🤔🤔